Sashe 126
Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Safeenah taci gaba da jada baya tana kame cikinta tana fad’in “Daga shi sai D’anmu.. Su kad’ai nake so su soni a Duniyar nan.. Ban damu wani ya soni ko ya k’ini ba idan har zasu soni, idan har zan kasance tare dasu.. Kuma d’ah na yana nan I’m sure Mommy batai nasaran ciresa ba kaman yanda tai niyya.. Zo ki tab’a kiji Kiki.. Ina iya jin motsinsa..” Tana maganar hawaye saman fuskarta amma murmushi take tana kuma shafa cikinta.. “Ga D’ah na nan.. D’ah na yana nan.” Tai Saurin K’arasowa wajen Mu’azzam tana fad’in “Kaji D’anmu na motsi.. Gashi nan yana motsi.. He’s a fighter.. Bai yarda Mommy ta datse masa rayuwarsa ba..”
Ana haka d’aya daga cikin ma’aikatan gidan ta shigo da package ta mik’awa Kiki tana fad’in delivery man ne ya kawo Wai a shigo ma Safeenah dashi.
Kiki ta amsa ta nufo d’akin, Safeenah tana hangota da package d’in ta mik’e tana fad’in “Look my Halal.. Ga kayan Babynmu da nai order jiya online ya iso.. First gift d’insa daga wajen Mamansa.” Tana maganar tana warware package d’in ta shiga fito da kayyayakin wanda duka kayan yara ne.. Kama daga kayan sakawa na early born baby zuwa takalmi harda toys.. Sai fito da kayan take tana sunbatu Tamkar dai mai tab’in hankali.
Kiki tai lamo tana duban ‘yaruwarta cikin tsananin tausayawa yayinda Mu’azzam ya shafi fuskarsa kad’an ya janyo Musaddiq suka fice.
“Ina Mommy..? Na tabbata bata gidan nan..” Mu’azzam yace yana duban Musaddiq.
Girgiza kai Musaddiq yai “I have no idea.. Bansan yanda taje ba..”
Mu’azzam ya kafesa da idanunsa da suka gama kad’awa zuwa ja “Musaddiq zan sake tambayarka a karo na biyu, Ina Mommy take..?”
Girgiza kai Musaddiq yai yace “Wllhi ban Sani ba.. Tare da kai muka shigo..”
“I know, nasan tare muka shigo.. But maybe zaka iya sanin yanda taje.. Gidan ‘yar uwa, Abokiya ko wata Confidante haka..?” Ya k’arashe yana tsare Musaddiq d’in da idanu kaman dai yana interrogating nasa.
Musaddiq ya kuma girgiza kai “Ban sani ba Mu’azzam.. Kuma idan na sani zan fad’a maka..”
Jinjina kai Mu’azzam yake yana duban Musaddiq d’in “Zan nemo Mommy.. Zan nemota duk yanda ta shiga.” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice cikin sassarfa.
Musaddiq yana komawa cikin gidan ya tadda Safeenah sai tsalle take tsakiyar d’akin tana juyi tana rungume kayan baby cikin jikinta.. Sai sunbatu take Kiki na gefenta tana kuka.
Kuka ne yaji yazo masa, cikin sauri ya fice daga d’akin yana kame kansa dake tsananin sara masa..
Kiki ma cikin kuka ta kulle Safeenah a d’aki kafin ta shiga dialing Daddy.
Daddy dake zaune gefen Aunty Nuratu sai ganin kiran Kiki yai na shigo masa, koda Daddy ya d’aga wayar Kiki kuka ta fashe masa dashi tana fad’in “Daddy... Daddy dan Allah kazo.. Daddy komai ba lafiya a nan.. Daddy Mommy Ta gudu.. And Safeenah is gone crazy..” Ta k’arashe cikin tsananin kuka tana mai duk’awa k’asa.
Alhaji Marwan ya soma karanto Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un a hankali kafin yace “Karimatu lafiya.. Ki nastu ki sanar dani meke faruwa..”
Cikin kuka Kiki ke fad’in “Daddy kawai ka dawo kafin Adda Feenah ta rasa ranta.. Daddy bazamu iya ba dan Allah ka dawo..” Ta k’arashe cikin kuka sosai.
Daddy ya lumshe idanunsa a hankali kafin yace “Ina Hajara..? Wai me yake faruwa a gidan ne..?”
Cikin kuka take fad’in “Daddy kawai ka dawo dan Allah Daddy..!” Kuka ya hanata ci gaba da magana.
K’ok’arin natsa kansa Daddy yai kafin yace “Shikenan, ki natsu kinji.. Ina nan tafe.. Ki kwantar da hankalinki kinji.. Ina Yayanki Musaddiq..?”
Kiki ta d’an waigo saidai bataga Musaddiq ba “I don’t know Daddy.. Maybe sun fice da Ya Mu’azzam..”
Daddy ya jinjina kai yace “Take care of your sister kinji koh.. Don’t leave her alone.. Zan kira yayun naki..” Daga haka katse kiran Daddy yai yana neman layin Musaddiq, saidai wayar Musaddiq bata shiga.. Ya kira na Mu’azzam ma bai samu ba.. Tanata rantse ringing ba’a d’agawa.
Juyowa Daddy yai yana duban Aunty Nuratu. A hankali ya d’aura hannunsa guda saman nata dake aje gefensa. Ya k’ura mata idanu kafin ya d’ago hannun nata ya sumbata. Lokaci guda yake furta “Kin tuna.. Kin tuna lokacin da ni d’in na tsinceki.. Kina cikin yanayi ne irin wann.. Ko ince yanayi mai kama da wanda kike ciki yanzu.. Baki san kanki ba a lokacin.. Kinyi losing memory... Bakisan komai ba, baki kuma san daga wata duniyar kika Zo ba.. A lokacin ina makaranta ne a can jihar Lagos birnin Ikko, dani da Yayana Abubakar.. Ranar sa ce ta k’arshe a makaranta..” Daddy yai shiru a daidai lokacin da ya soma tuno wani b’angare na rayuwarsu a baya.
_WAIWAYE_
Samaruka ne guda biyu suke zaune a k’ofar University of Lagos. K’aramin wanda duka duka babban bazai tsere masa da shekaru biyu zuwa uku ba ya dubi D’anuwan nasa wanda kallo guda zaka masu ka fahimci akwai shak’uwa da k’aunar juna irinta ‘yanuwantaka mai k’arfi tsakaninsu “Hamma zanyi kewarka sosai a makarantar nan.”
Wana aka kira da Hamma ya dubi D’anuwan nasa murmushi saman fuskarsa, Ya d’an shafi sumarsa kaman yanda yake masa a ak’asarin lokuta. Sai yace “Nima zanyi kewarka Marwan.. Amma kar ka damu zan dinga kawo maka ziyara.. Lagos ai ya zama mana gida.. Sann ga Salman kwanan nan shima zai taho ya soma nasa karatun.. Bazakai kad’aici ba..”
Marwan ya d’an b’ata fuska yace “Jami’a ba kaman sakandare ba balle kace zaka ke kawo mun ziyara.. Nasan Salman zai taho kwanan nan amma da kai nafi sabawa D’anuwana.. Zanso nima na koma kusa da Baffah da Inne na k’arasa karatu na a can.. Gaskiya na gaji da zaman kudu.. Balle yanzu da baka nan banjin zan iya..”
Abubakar wanda shine Hamman Marwan ya kuma murmusawa yace “Zaka iya Marwan... Wayasani ko matarka a nan Kudu take. Kaga sai ka samo mana sirka a nan.” Yai maganar Cikeda barkwanci.
Marwan ya zaro ido waje kad’an ya girgiza kai yace “Aure a kudu.. Kaima kasan Baffa da Inne bazasu tab’a amincewa da hakan ba.. Musamman Inne..”
Abubakar ya murmusa kad’an yace “Kasan menene..? Tashi muje..” Ya k’arashe yana mik’ar dashi tsaye.
“Ina zamuje..?”
“Gari zamu zaga kafin na tafi..”
Marwan ya murmusa kafin yace “Toh ina zamuje..?”
“To the Port.. Muje muga jiragen ruwa muyi nishad’i bakin Teku..” Abubakar ya basa amsa kai tsaye.
Marwan ya murmusa yace “Zanji dad’in hakan kuwa.” Suka murmusa a tare yayinda Abubakar ya janyo D’anuwansa suka soma tafiya.
Sanda sukazo tashan jirgin Ruwa sun tadda tashan wayam babu kowa kaman anyi yak’i an cinye.. Sukaita Yawo tsakankanun jiragen ruwa suna kallon wasu jirage da suka k’one.
Marwan ya tsaya jikin wata babbar jirgi da ta lalace yana kallon cikin jigin, nan ya hango kaman k’afar mutum daga kwance.
Baiyi wata wata ba ya haye ya shige cikin jirgin yayinda Abubakar ya soma kiransa yana fad’in yazo su tafi kafin wani abun ya samesu.
Marwan ya girgiza kai yace “Ka jirani a nan Brother ina zuwa..” Bai tsaya sauraron D’anuwan nasa ba ya shige cikin jirgin yana kuma mamakin abinda ya hango.
Saida ya k’araso sosai ya kuma tabbatarwa k’afar mutum ne ke reto.. Cikin sauri ya soma k’ok’arin janye katakon da ya rufe fuskarta zuwa gangar jikinta. Gabansa ya yanke ya Fad’i sakamakon bayyanar kyakkyawan fuskarta.
A hankali Marwan ya furta”Nooor..” Yai fasali yana kuma dubanta kafin ya duk’a a hankali “Mai kikeyi a nan baiwar Allah.. Wacece ke...?”
Yanayin suturan dake jikinta da wani irin kitso dake kanta wanda akai kaman gammo da sumarta ya tabbatar masa watak’ila daga wata nahiyar ta taho nan.. Ya duk’a a hankali yana kuma k’are mata kallo.. Kyakkyawar budurwa ce wacce bazata gaza shekaru 15 ba a wancan lokacin. Marwan yai zaune ya tasata gaba yana kallonta yama mance tareda D’anuwansa yake. Har saida Abubakar d’in yaji shiru ya shigo cikin jirgin yana neman D’anuwansa, can ya hangosa zaune gaban mutum. Ya k’araso a hankali yana dubansa.
“Marwan wacece wann..?” Abubakar ya tambaya.
Marwan ya girgiza kai alamun bai sani ba, Abubakar yai saurin k’arasowa ya kamo hannunsa “Tashi mu tafi.. Tashi mu bar wajen nan..”
Marwan ya girgiza kai “No.. Bazamu tafi mu barta a nan ba.. She needs our help..”
“But we don’t know her Marwan.. Ina zamuje da ita... Kaga Zo mu tafi kafin wani ya ganmu.. Ban yarda da wajen nan ba..” Abubakar ya k’arashe yana k’ok’arin janyo D’a uwansa Marwan.
Tarjewa Marwan yai yana fad’in “No bazan tafi na barta ba.. I’m staying right here with her.. Dan Allah ka taimaka min mu d’auketa mu kaita asibiti..”
Abubakar yai shiru yana duban D’anuwan nasa yana kuma duban budurwar dake kwance idanunta a lumshe “Marwan bamu santa ba, bamu San daga wace duniya take ba.. Bamu San wacece ita ba.. Maybe ‘yanuwanta suzo nemanta.. Kaga kazo mu tafi bana so ka saka kanka a matsala..”
“Hamma bazan tafiba ba tareda ita ba.. Idan kuma kai zaka tafi fine kaje..”
Ya k’arashe yana mai k’ok’arin d’agota.
Abubakar yai tsaye yana dubansa sai kuma ya girgiza kai yace “You are so stubborn Marwan.. Yanzu ya zamuyi da yarinyar nan.. Ko asibiti muka kaita mai zamuce.. Babu police report.? Yarinyar da ko sunanta bamu sani ba.. Balle musan daga wace Nahiyar ta fito..” Yana maganar yana k’ok’arin taimakawa Marwan suka rik’eta su biyun.
“I don’t know Yaya.. Amma Iyakacin abinda na sani shine bazamu tafi ba tareda ita ba..”
Abubakar ya jinjina kai yace “Shikenan muje.. Allah Sa kar ‘yansanda su ganmu da mutum haka su tuhumemu..”
Marwan ya amsa da “Babu ma abinda zai faru in sha Allah.. Allah yaga niyya mu na taimako.. Muje..”Ya k’arashe suna masu ficewa tallafe da Budurwar.
Kasancewar yamma ne lis yasa kowa nasa sauri sauri yake ya yada zango.. Babu wanda ya kula dasu da tsintuwarsu abinka da birni mai yawan Al’umma.. Wani asibtin kud’i suka kaita kasancewarsu yaran attajiri tuni Likita ya amsheta.. Sai kuma likitan ya tambayesu mai ya sameta sann wacece ita..
Suka dubi juna a tare cikin rashin sanin mai zasuce..
Marwan yai saurin cewa “‘Yaruwarmu ce had’arin mota ta samu..”
Likitan ya dubesu da mamaki yana kuma dubanta dan ga alamun bruises kad’an jikinta alamun dai had’arin tai.