← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 175

Sashe 65

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Shut up Maleeka..!” Chief Jaja ya daka mata tsawa kafin ya matso kusanta sosai yana huci yake furta “D’aniskan yaron nan is driving me crazy.. Ina d’aga masa k’afa ne sabida ke.. Sabida kince akanshi zaki iya rabuwa dani kuma zaki iya rasa rayuwarki duk akan wanann D’aniskan yaron da ma baisan kinayi ba.. Bayajin bari ba’a hanasa ya dena.. Duk hanyar da za’abi a nuna masa cewa an isa k’arshen case d’in anbi yak’i ya amince yak’i ya dakata ya hak’ura da binciken da yake, anyi duk mai yuwa yak’i ya daina.. Ya rantse sai ya isa k’arshen case d’in nan.. Toh kuwa Ina mai tabbatar miki Maleeka Mu’azzam Gamji yana tono mutuwarsa ne da kansa.. Dan akwai BAT a sama dani duk randa ya isaga BAT Toh kuwa babu shakka mutuwarsa kenan..!”

Maleeka ta shiga girgiza kai tana fad’in “No please.. Dan Allah kar ku kashe shi.. Kar ka bari a kashe shi.. Wllhi idan na rasashi mutuwa zanyi.. Wllhi mutuwa zanyi. Dan Allah kar ka bari a halak’ashi..”

Chief ya murmusa da gefen baki yana shafan b’angaren fuskar Maleeka da hannunsa guda “Baby bani zan kasheshi ba BAT ne zai kashesa..”

Cikin rud’ani Maleeka tace “Bayan BAD akwai BAT.. Toh Waye BAT..?!” Tai tambayar cikin rud’ani..

Murmusawa ya kumayi kafin yace “Jemage kikeji, baya farauta sai cikin dare.. BAT is worse than BAD.. Abinda zan iya fad’a miki kenan.. Idan ya ci gaba da Digging zai isa wajen BAT, idan ya isa nan kuma believe me ya hak’o kabarinsa da kansa.. Zaifi masa kyau idan ya yarda ya tsaya a nan domin BAT baida d’and’anin imani...!”

Suna cikin maganar wayar Chief ta soma ruri, sunan BAT ya bayyana saman screen d’in.

Zuciyar Maleeka yai wane irin tsinkewa ganin BAT ya bayyana.

“Get out now..!” Chief ya fad’i yana dubanta.

Yanda ya bud’e murya gaba d’aya yai maganar saida ya d’an firgita ta.. Tai saurin sa kai ta fice daga ofishin dukda taso taji abinda BAT da Chief zasu tattauna akai.

Tana fitowa taga wayan Ameer na shigo mata. Tai k’ok’arin saita kanta kafin Ta keb’e domin amsa kiran Ameer.

Tana d’agawa Ameer ya soma fad’in “Well done Officer.. Kinyi k’ok’ari da kika tura wa Mu’azzam sak’on BAD.. Tabbas sak’o ya isa ga Mu’azzam har ya nuna mun.. Well done..”

Fuzar da huci tai kad’an kafin tace “Look Ameer, I don’t know what you are talking about..”

“No no no.. Don’t you play dump with me Maleeka.. Ke kad’aice kikeda motive na turawa Mu’azzam wanann sak’on.. But koma yaya ne I must thank you domin kuwa sak’on zai taka babban rawa a auratayyan Mu’azzam da kuma Safeenah musamman yanzu da aka wanke Safeenah Banida chance d’in kareta a Kotu kinga sak’on BAD zai amfani domin kuwa na tabbata a halin yanzu Mu’azzam bazai tab’a yarda babu wata alak’a tsakanina da ita ba..” Ya k’arashe yana mai fashewa da dariya. Lokaci guda yaci gaba da furta “Good job Officer.. Keep it up.. Dole na baki kyautar kiss ta cikin waya..” Ya k’arashe yana mai kissing wayar yana kuma tintsirewa da shewa.

Zama Maleeka tai gijif saman kujera abubuwa cunk’ushe cikin zuciyarta, ita yanzu bata Ameer da ahirirtarsa take ba. Damuwarta shine wanene BAT wanda Jaja yake tarayya dashi wajen ruguza Mu’azzam.. A baya tayi tarayya da Jaja ne dan tasan Tabbas Jaja nada masaniya kan case d’in mutuwar Ikram, dan ta tab’a tsintar text message wata rana cikin wayarsa bayan Sun gama aikata mai zasu aikata a hotel room, sak’on ya shigo wayar Chief.. A lokacin wayar na aje gefenta kan gado yayinda Jaja ke bathroom.. Nan taga an turo sak’on kuma zallan sunan Safeenah Gamji kawai taga an rubuta a sak’on shiyasa tai zargin Safeenah nada alak’a da case d’in mutuwar k’anwar Mu’azzam.. Hakan ne yasa ta nemi Barr Ameer suka had’a team ta sanar dashi abinda take zargi gameda Safeenar shi kuma Barr Ameer yai amfani da abinda Maleeka ta fad’a masa yana Barazana ma Safeenah da cewa yasan wani abu gameda ita. Amma a halin yanzu batajin zata iya, Dikda cewa tin farko bataci dunduniyar Mu’azzam ba, ita kawai abinda take so shine ta fidda Safeenah daga rayuwarsa ita ta samu gurbi, bayan wannan batada wani motive na ruguza Mu’azzam.. Yanzu da rayuwarsa ke cikin had’ari ta damu matuk’a.. Batasan mai zata aiwatar ba.. Idan ta sanar dashi ga abinda Jaja yakeyi tasan Tabbas ba Mu’azzam kawai ba harta itama zata rasa rayuwarta ne.. Zata rasa Mu’azzam domin kuwa Tabbas su Chief sai Sun karsa matuk’a bai dakata da binciken da yake ba.. A b’angare guda tasan Mu’azzam da kafiya akan duk abinda yasa gabansa.. Batajin zai dakata da binciken nan.. Gaba d’aya Maleeka ta rasa wanne zatai, zuciyarta ya gama karaya da hidiman Jaja.. Tana matuk’ar tsoron ta rasa Mu’azzam.. Lumshe idanunta tai hawaye suka gangaro mata.. Ji take tsaf zata iya bada rayuwarta ga Mu’azzam sabida tsananin k’aunar da take masa.. Wayarta ne ya kuma ruri nan taga Chief ne mai kiranta. Tana d’agawa yace da ita su had’u da dare. Ya sanar da ita sunan hotel d’in da zasu had’u daga haka ya katse kiran bai tsaya sauraronta ba. Ta goge hawayen da suka zubo mata.. Tabbas dole ta had’u da Chief a daren domin ta k’ara samun clue gameda BAT.. Ya kamata Mu’azzam yasan akwai BAT a sama da Chief wanda suke k’ok’arin kaisa k’asa. Da wannan tunanin ta mik’e ta nufi restroom ta gyara fuskarta kafin ta fito ta nufi ofishinsu.

**
A can gidan Daddy kuwa murna ake kanyi ana Barka da juna, Safeenah kaw Mommy da Aunty Shemau sai nan suke da ita musamman data basu labarin daren jiya a cikin cell saida shugaban ‘yantaddan cikin cell d’in ta sanyata tai mata tausa tana a matsayin Safeenah Gamji babu halin tak’i yi taci bugu a banza.

Meema kaw duk maganar da takewa Safeenah, Safeenar tak’i kulata, idan taga Meema a waje ma b’ata fuska take ko ta bar wajen gaba d’aya.

Wannan karon zaune ta tadda Safeenar a d’akinta tana shan grapes. Tana duba wayarta da tai missing na kwana guda.

Meema ta dubeta tace “Addah Feenah wai bazaki min magana bane inata binki ina miki barka..”

Safeenah ta dakata da abinda take tana aikawa Meema wane irin wulak’antaccen kallo “Maiyasa zan amsa munafuka irinki wacce batada burin da ya wuce taga na dawwama a Kurkuku.. Ai nasan na ciki na ciki ba haka kika so ba, kinso na zauna a can don ki samu abinda kike so.. Algunguma traitor.. How could you Meema..? Inaji ana cewa a cikin wanda kuka fito ciki guda ma ana samun wanda zaike bak’in ciki dakai ban yarda ba Sai akanki Meema..”

Cikin rashin gane ina kalaman Safeenah suka nufa Meema ta shiga girgiza kai tana fad’in “Adda Feenah where’s all this coming from..? Addah Feenah mai kike nufi..?”

Safeenah ta kuma watsa mata wani kallon kafin tace “Munafuka, don’t act innocent. Kinsan sarai abinda nake nufi kuma Allah ya toni asirin munafuka irinki.. Dama kaf gidan nan an miki shaidan munafunci da gulma ni kad’aice ke yarda dake na baki dukkan yarda na da sirrina kikaci amanata.. Ko zaki ce bakisan Ameer na kirata a waya ba..?”

Gaban Meema ya fad’i dan ta tina lokacin suna Fufore ta amsa wayar Safeenah sanda Barr Ameer ya kirata har ta goge kiran daga call log amma tayi hakan ne dan kar Safeenah ta jefa kanta cikin matsala wajen Mu’azzam ya zaci tana cin amanansa da wani ne. Tayi hakan ne domin ta taimaki ‘yaruwarta amma ba da wani nufi ba. Allah shine shaidanta.

Safeenah taci gaba da jinjina kai ganin Meema nata amsata ba “Dama nasan kin sani, kuma kina son sanar da Mu’azzam.. I was such a fool da na Kasa gane ina kika nufa tuntuni.. Komai kece kike karanta mun yanda zanyi Meema ashe so kike ki rabani da mijina ban sani ba.. You are jealous of me..!” Ta d’an dakata kafin Ta kuma tsareta da ido tace “Tell me Meema.. Do you love Mu’azzam..?”

Baki sake Meema ke dubanta cikeda tsananin mamaki.. Ta soma girgiza kai cikin rashin yarda da abinda ‘yaruwar tata ke fad’i mata “Addah Feenah.. Kin kuwa ji mai kike fad’i.. Why would you think like that..? I mean.. Kinsan mai kike fad’i kuwa..? Addah Feenah how on earth zan so mijinki..?”

“Ai ba kanki farau ba.. Ana samun irin haka Meema.. Son Mu’azzam kike shiyasa kiketa k’ok’arin exposing d’ina wajensa dan ya sakeni ke kuma ki samu ya aureki koh..? Munafuka kawai algunguma.. Yau duk illahirin gidan nan sai sunji mai kika aikata..!” Ta k’arashe tana mai mik’ewa kafin ta bangaje Meema ta wuce.

Mommy da Aunty Shemau suna d’aki suna kuma jinjina lamarin Aunty Shemau tana sanar da ita sunyi waya da Uncle Salman Daddy ya sanar dashi duk abinda ke faruwa amma yace kar a sanar da Inne.

Mommy tace “Ai gwara da ba’a sanar da wannan jarababbiyar tsohuwar ba da yanzu ta d’agawa mutane hankali gaba d’aya.. Gashi Allah ya tak’aita, gaskiya tayi halinta Allah ya wanke Safeenah daga zargin da ake mata. Yanzu kuma lokacin mu ne da zamu d’au fansa kan Mu’azzam.. Wllhi Sai ya sakar mun d’iya kuma sai mun tafi Kotu akan abinda yaima Safeenah sannan muci taransa.”

Daidai lokacin Safeenah ta turo k’ofa tana fad’in “Mommy babu wanda zai rabani da mijina.. I still love him dukda abinda ya aikata..”

Baki sake Mommy da Aunty Shemau ke dubanta.

Safeenah ta dubi Aunty Shemau tace “Aunty ku shirya yau d’in nan zuwa dare zaku kaini gidana.. Na kira Aunty Faty da Aunty Hadiza k’awayen Mommy zaku kaini gidana yau da dare.. Wllhi bazan bar ma wata shegiya can gidana da mijina ba.. Dan naga alama har a cikin gida ma akwai masu son su rabani da mijina su shige gidana..” Tana ida fad’in haka ta juya ta fice.

Mommy ta mik’e ta biyo bayanta tana fad’in “Ke ke Safeenah.. Zo nan..” A parlor suka tsaya gaba d’ayansu harda Aunty Shemau. Mommy na tambayarta mai take nufi.

Duban Meema dake rakub’e gefe tai tace “Mommy ‘yarki Meema son mijina take har sak’o take tura masa na cewa nida Ameer muna cin amanarsa.”
Chapter 65 · 0% Book details