← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 164 OF 175

Sashe 164

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aunty Nuratu ta dubesa kafin ta jinjina kai kad’an tace “Nasan yanda kake ji and believe me nima inajin irin wann rad’ad’in.. Zanfi kowa son Hajara ta biya Abinda ta aikatawa Ikram da mahaifinku harmada Sirkinka.. Amma Dikda da haka da zan sami zarafin yafe mata zan yafe mata sabida har kullum laifin da aka maka ka yafe yafi wanda ka d’auki hukunci.. Toh amma abun shine Hukuma sun riga sun shiga Hajara dole Ta amsa masu kuma rayuka ba d’aya ba ba biyu ba Hajara ta d’auka a wuyanta, Ita d’in barinta cikin al’umma barazana ne dan bamusan mai zata aikata ba idan har ‘ya’yan cikinta ma basu tsira da sharrinta ba.” Ta d’anyi fasali kafin taci gaba da fad’in “Bazan hanaka gudanar da aikinka ba, amma inaso kai hak’uri abubuwa su lafa kafin ku tafi da Hajara, ka dubi yanayin da Karima ta shiga ganin mahaifiyarta da tai a haka, sann ga halinda Safeenah Ke ciki.. Ga Musaddiq can a cell, he hasn’t been released yet.. Don’t you think this is too much for the family.. Babankun ma kansa k’ok’ari yake.. Kai hak’uri abubuwa Su d’an sassauta kafin ku tafi da Hajara.. Na tabbata bazata iya guduwa ba bayan tilin jami’an tsaron dake cikin gidan nan,sann an kama D’anuwan nata.. Ni a ganina a bari Al’amara Su d’an daidaita matuk’a bazai shafi aikinka ba.”

Shiru yai kansa kife a k’asa yana sauraron mahaifiyar tasa. Sai yanajin wani abu mai nauyi.. A hankali ya d’ago yana duban mahaifiyar tasa, ya sadda muryarsa yana fad’in “Mamy kiyi hak’uri.. The decision isn’t in my hand.. Mommy tanada several cases akanta.. But still na miki alk’awari zanga abinda za’a iya yi.. But at the end, Mommy must face the law..”

Mahaifiyarsa ta jinjina masa kai a hankali, lokaci guda ya kamo hannayenta cikin nasa “Not a day went by without me missing you Mamy.. Nayi kewarki sosai Mamy na.”

Ta sakar masa murmushi tana shafan b’angaren fuskarsa guda “Nayi kewarka nima sosai.. Ina jin duk abinda kuke fad’a mun saidai banida ikon amsa maku.. Allah shine abin godiya da ya dake had’e fuskokinmu da alkhairi..” Ta d’anyi fasali hawaye na gangaro mata, lokaci guda ta saka hannu ta goge hawayen “Ban tab’a shiga tashin hankali mai tsanani ba a lokacin da nake kwance kaman lokacin da Hajara ta sanar dani abinda ta aikatawa Ikram.. Allah ne kawai ya k’addari bak’in cikin bazai ajalina ba.. Alhamdulillah, zuciyar dake bugawa cikin k’irjina mai yawan zikiri ne da ambaton mahaliccinsa..”

Hawayen da yake k’ok’arin dannewa suka gangaro masa, ya d’an kifa kansa kad’an zafin abinda ya samu Ikram cikin k’irajensu.
Suka d’auki lokaci a haka kafin Mu’azzam ya mik’e yana shafe fuskarsa da tafukan hannayensa.

“Zanje naga Musaddiq Mamy.” Ya fad’I yana mai sadda kansa.

Jinjina masa kai tai tana k’ok’arin maida nata hawayen “Kajeka.. Kaje kaga D’anuwanka.. Allah shi maka albarka.”

A hankali ya amsa da Ameen Mamy. Har cikin ransa yaji dad’in addu’an nata wanda ya jima baiji daga gareta ba.

Mu’azzam yasa kai ya fice mahaifiyarsa tabisa da kallo tana mai kuma lumshe idanunta, abubuwan da suke kan faruwa na mata gizo.

A haka Daddy ya shigo madaidaicin parlorn. Yai tsaye yana dubanta, ya d’an d’auki lokaci a haka kafin ya soma takowa.

Ya jima sosai tsaye kanta yana tinanin abinyi musamman da yaga hawaye na fitowa daga cikin lumsassun idanunta.

Sai ya kai hannayensa kaman zai dafata Sai ya janye hannayen nasa, yayi haka har kusan sau uku kafin daga bisani ya sami courage na tallafo kafad’unta, Ta bud’e lumsassun idanunta masu zuban ruwa.

Ganin Daddy da tai tsaye gabanta tallafe da kafad’unta ba komai ya tuna mata ba sai tarihin had’uwarsu da yanda ya tsinceta da ya labarta mata sanda take kwance a Fufore ba tareda Daddyn yasan tana iya sauraronsa ba.

“Noor..!” Ya furta a hankali cikin wane irin siga, hawaye ne Ke fito masa shima yayinda Kukan Aunty Nuratu ya k’aru. Daddy bai wata wata ba ya rungumota cikin jikinsa su duka biyun suna hawaye.

Daga yanda Mommy ke lab’e tana dubansu ji tai kaman an dab’a mata mashi a k’ahon zuciyarta.

Wai Nuratu ce cikin jikin Marwan d’inta.. Toh wllhi bazata barsu su samu peace ba, kuma babu uban da ya isa ya kamata muddin bazaa kama tsohuwar banzan can Inne ba.. Kuma zama gidan daram dan batada sauran ahali bayan yaranta. Yo ita ai tama girmi saki a shekarunta wllhi.. Idan za’a mutu babu mai rabata da Marwan.

Can Mommy Ta hango Kiki ta nufo parlorn. Da gudu Mommy ta nufo waiting d’in yanda su Daddy ke tsaye tana fad’in “Wayyo na shiga uku zasu lalata min yara.. Kiki koma ki koma kar kiyi mugun gani mahaifinki na abinda bayi ba da k’uruciya.”

Daga Daddy har Aunty Nuratu da tsananin mamaki suka juyo suna duban Mommy.

Ta k’araso gabansu tana shewa “Kuce kawai na cika maku burinku na kashe Abubakar.. Tir wllhi kinji kunya.. Marwan kaji kunya, Sauran Danuwanka..! Ke kuma ko kunya babu kin Shige jikinsa kinbi wa kinzo zakibi k’ani dangin karuwai dama Karuwanci ya shigo daku k’asar.”

Bata kai aya ba taji sauk’an mari har guda biyu masu kyau.. Ta soma kururuwa tana dafe k’uncinta yanda Daddy ya mareta, cikin tsananin b’acin rai ya shiga janyo hannunta yana fad’in “Idan hukuma basu rufeki ba ni zan rufeki Hajara.!” Ya k’arashe yana mai turata cikin k’aramar store dake wajen.

Kiki kuka tana kiran Mommy saidai tuni Aunty Nuratu ta janyota ta rungume suka fice daga wajen gaba d’aya.

**

Mu’azzam yai tsaye daga can nesa yana hango Musaddiq dake tak’ure cikin cell ya kifa kansa, yaci gaba da takowa a hankali yana duban Musaddiq d’in.

Alamun tab’a k’ofar cell d’in da Musaddiq yaji ya sanyasa saurin d’agowa yana duban mutumin da ya shigo wanda ba kowa bane face D’anuwansa Mu’azzam.

SameenaAleeyou📚
*GIDAN ARO*

*81*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Ya jima tsaye hannayesa hard’e ta baya yana duban Musaddiq d’in wanda kansa Ke kife.

Kaman babu mai cewa komai cikinsu, a hankali Mu’azzam d’in ya duk’a suna fuskantar juna, hawaye ne ya hango kwance cikin idanun Musaddiq. Suka d’an kuma d’iban lokaci a haka.

“Ka tuna a lokacin muna yara, munje hutu Fufore.. Mukai wasa na cops and bad guys.. Kaine Cop ni ne Bad guy.. You were chasing me, trying to catch me.. Kana ce min I should surrender..” Ka tuna Musaddiq ya k’arashe hawaye gauraye da wani irin murmushi mai ciwo saman fuskarsa.

Lokaci guda yaci gaba da jinjina kai yana fad’in “Wann wasan ya zama gaskiya right..? You are the Cop.. And I’m the bad guy.. Gashi kuma ka kamani..” Muryarsa yaci gaba da rawa yana furta “Ni ne mafi munin D’anadam a duniya.. Da ace ban aikata mata abinda na aikata mata ba maybe da har yanzu tana raye.. Ban cancanci rayuwa ba..” Bai kai aya ba Mu’azzam da hawaye keta k’ok’arin b’allowa daga cikin idanunsa yai saurin rungumesa. Kuka Musaddiq yake sosai yayinda hawaye ke fita daga idanun Mu’azzam. Bai iya furtawa Musaddiq komai ba Sai mik’e da yai ya fice yana share fuskarsa da tafukan hannayensa.

Musaddiq ya bisa da kallo yana kuma lumshe idanunsa wasu hawayen na gangaro masa.

A waje ya tadda Hajiya Faty wata sergeant tayo mata rakiya. Jikinta a matuk’ar sanyaye ta k’araso yanda Mu’azzam ke tsaye jikin motarsa. Ta sadda kanta k’asa tana masa godiya.

Shiru bai ce komai ba, sai ya zira hannayensa ciki aljihun jeans d’insa, lokaci guda ya d’an kauda fuskarsa gefe yana furzar da huci a hankali, wayarsa ya ciro cikin aljihu ya mik’a mata “Call your driver.” Ya fad’i fuskarsa babu wani walwala.

Hajiya Faty hannu biyu tasa Ta amshi wayar ta soma dialing layin drebanta hannayenta har rawa suke. Ta ida wayar kafin ta mik’awa Mu’azzam wayarsa cikeda risinawa tana kuma masa godiya.

“Mijinki won’t find out about this.. Ina fata wann ya zama darasi a wajenki, da masu d’abi’ar bin bokaye da malaman tsubbu.. Sa’arki d’aya kince malamin da ya maku aikin ya jima da mutuwa da harda shi zan kamo na had’a na kulle ku sai muga idan zai iya kub’utar da kansa.. Amma saidai bansan ko kinyi sabon malamin ba.”

Hajiya Faty na hawaye take girgiza kai “Ni wllhi na tuba.. Ni hanyar gidan boka ma bani k’ara bi.. Allah ya saka maka da alkhairi.. Dan Allah ka rok’ar min mahaifiyarka gafara.” Ta k’arashe cikin rawar murya.

“Dama bata k’ullaceku ba.. Kin San maiyasa sabida bata yarda Bokanku da malaminku zasu iya cutar da ita ba face abinda Allah ya k’addara zai sameta.. Kije ki rok’i Ubangijinki gafara domin shi kuka sab’a.. Allah ya datar damu baki d’aya.”

Hajiya Faty Ta kuma jinjina kai tana hawaye. Daidai lokacin driver d’inta ya k’araso dan Dama kusa yake. Ta kuma yima Mu’azzam godiya ta wuce.

Shafe fuskarsa ya kumayi kafin ya shige motarsa ya d’auki hanyar gidansa.

Wanka yai ya shirya cikin k’anan kaya kafin ya kuma fitowa ya d’auki hanyar Annoor Masjid dan yaji dad’in karatun da ya saurara wancan ranan, ya k’udiri niyyan da izinin Allah karatun bazai dinga shigesa ba, da yawan maza idan suka d’an girma suka zama samari sai kaga shikenan sun daina neman ilimin addini wanda wasu sam basu ma samu wadataccen ilimin addinin da k’uruciya ba. Ba’a girma ma neman ilimi musamman na addini.. Kar mutum ya shagala da neman duniya, ya kamata ya sami lokaci na musamman ya ware domin tanadi ma gidansa na Gaskiya.

Tare dashi akai karatun bai bar masallacin ba sai bayan isha.. Daga nan kai tsaye gidan Daddy ya nufa.
**

Umma tai K’uri tana duban Yayarta yanda ta gyara ma Kiki dake kwance saman gadonta kwanciyar nata, ta rufa mata bedcover tana shafa kan yarinyar a hankali cikeda tausayawa.
Chapter 164 · 0% Book details