← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 175

Sashe 129

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya Faty ta tsare Musaddiq da idanu kafin Ta girgiza kai tace “Musaddiq akan mahaifiyarka ta aikata kuskure guda shine zaka bud’e baki ka kirata mai laifi..”

Cikin k’unan zuciya yake furta “I know what I’m talking about Aunt.. Nasan kura kuran da Mommy Ta aikata da dama wanda baki bazai iya fad’i ba, kunnuwa bazasu iya sauraro ba haka nan zuciya bazata iya d’auka ba.. Aunt please, if you’re hiding Mommy ki fitar da Ita yanzu.. Mu’azzam na waje yana jira kuma na tabbata bazai bar gidan nan ba tareda Mommy ba..”

Hajiya Faty ta daidaita tsayuwarta tana dubansa kafin Ta girgiza kai, tasa hannu ta ture Musaddiq d’in gefe tana fad’in “How dare he zai shigo mun gida ba tareda izini na ba..” Tasa kai ta Shige fuuu Musaddiq na biye da ita na kiranta.

K’arasowa tai yanda Mu’azzam ke tsaye a haraban gidan yana jiran fitowar Musaddiq d’in.

“Wace doka ce ta baka dama ka shigo mun gida ba tareda amincewata ba.. Who do you think you are..? Just because you are a Cop doesn’t mean zaka shigo mun gida kai tsaye..” Ta d’ago kai tana duban securities “Kai security kuzo ku fitar mun dashi..” Ta k’arashe tana kiran securities d’in nata.

Mu’azzam da tin fitowarta ya kafeta da idanunsa da suka gama kad’awa, hannayensa dafe saman kunkuminsa yake takowa gabanta. Yayinda Musaddiq ya dakatar da securities d’in ya hanasu k’arasowa.

Mu’azzam ya tako gaban Hajiya Faty yana kuma tsareta da idanunsa masu furgitarwa “Where is Mommy.. Where are you hiding her..?” Tambayar da ya mata kenan cikin rarrabewar kalamai.

Hajiya Faty na huci take fad’in “Don’t you dare.. Kar ka kuskura.. I know my right Detective.. Idan baka fice mun a gida ba I’ll charge you of trespassing..”

“Hajiya zaki fuskanci hukunci idan har kika kare mai laifi..” Ya fad’i idanunsa tar kan Hajiya Faty.

“Kar ka kuskura kace zaka mun barazana, nasan ‘yanci na.. Haka kawai bazaka shigo gidana kace kana neman mai laifi ba.. Ina mai baka shawar da ka fice tun wuri before I make my own move.. Na tabbata bazaka so abinda zan aiwatar ba.. Fita yanzu..” Ta k’arashe tana nuna masa hanya.

A hankali yake jinjina kai yana dubanta “We are not done yet, idan har Kina b’oye Mommy sai kin fitar da ita.. Na miki alk’awari..” Yana ida fad’in haka yasa kai ya juya.

Musaddiq yai saurin bin bayansa yayinda Hajiya Faty taja wani dogon tsaki tana instructing masu gadinta da kar su kuma k’yale wann mutumin ya shigo mata gida..

Musaddiq yai saurin take masa baya yana girgiza kai, a ya k’araso jikin motar sanda Mu’azzam ke k’ok’arin bud’e marfin motar, duk jikin Musaddiq d’in a mace.

“Kai hak’uri Mu’azzam, zanci gaba da neman Mommy kuma bazan gajiya ba har sai an sameta in sha Allah.. Kuma ina mai tabbatar maka Mommy bata cutar da Aunty Nuratu ba.”

Mu’azzam ya tsaresa da idanu yana dubansa kafin ya kauda fuskarsa kad’an yana rage girman idanunsa, ya d’an b’ata lokaci kafin yace “Why would she be running away.. Idan har ba wani babban abu take b’oyewa ba Maiyasa take guduwa..?”

Musaddiq ya had’iyi abinda ya tsaya masa a mak’oshi da k’yar kafin yace “Mommy tasan kai D’ansanda ne so dole taji tsoro ta gudu bayan kashe maka d’ah da tai right in front of you.”

Mu’azzam ya girgiza kai da sauri “But you told me Mommy ta d’auko wa Mahaifiyata mai magani na bogi.. Right..?”

Musaddiq ya jinjina kansa a hankali kafin yace “But ba’a bata wann maganin ba, Aunty Nuratu bata tab’a shan maganin matar ba.. Ka yarda dani ban bari hakan ya kasance ba.”

Murmushi mai ciwo Mu’azzam yai kafin yace “Idan har zata iya aikata abu makamancin wann, zata iya aiwatar da abinda yafi wann muni.. Kar ka mance Mommy ta cire gudan jinina akan idona.. Ina kallo yana bin k’asa.. Sai kuma kazo kana sanar dani ga abinda taso yi wa mahaifiyata bayan cewa shekaru da dama Mommy ta kwashe da sunan tana jinyar mahaifiyata.. Musaddiq shin baka tunanin Mommy zata iya k’ulla abinda yafi wann muni..” Ya d’anyi fasali yana daidaita tsayuwarsa kafin yaci gaba da fad’in “Idan har zata taste cikin Safeenah da kanta, bayan cewa Safeena d’iyarta ce, bata damu da halin da zata iya jefa Safeenah ciki ba, tana kallo Safeenah na juyi a k’asa cikin severe pain, jini na bin k’afafunta.. Tana kallo D’anta na bin k’asa wane irin abu ne bazata iya yi ba..?” Ya kuma girgiza kai kafin yace “Com’n Musaddiq use common sense here, idan har zata iya cutar da Safeenah irin haka Toh kuwa Tabbas babu wanda bazata iya cutarwa ba.”

Furzar da huci kad’an Musaddiq yai kafin yace “I don’t know Mu’azzam.. Iyakacin abinda na sani na sanar dakai.. And a nawa tunanin tinda Aunty Nuratu bata sha wann maganin ba Mommy can be considered innocent right..?”

D’agowa yai da mamaki yana duban Musaddiq saidai kafin yakai ga furta wani kalma ya hangi wayarsa dake saman kujeran motar tana vibrating.

Bud’e marfin motar yai da zummar d’auka wayar saidai tuni kiran ya katse. Nan ya d’auki wayar cikin hannunsa yana dubawa. Assad ne ya kirasa bai samesa ba.. Bayan kiran Assad da ya gani da dama harda na Aunty Larai.

Kiran Assad ne ya kuma shigo masa, ya d’aga wayar yana mai k’arawa a kunnensa yana d’an duban Musaddiq d’in dake tsaye gabansa.

“What.! Wane asibiti kenan..? Alright alright, gani nan zuwa.” Daga haka katse kiran yai ya shige mota yana k’ok’arin kunnata. Ya dubi Musaddiq dake tsaye wajen har lokacin “Ka koma gida ka duba jikin Safeenah.. Idan ka samu wani abu gameda Mommy ka kirani ka sanar dani..”

Jinjina kai Musaddiq yai ba tareda ya iya cewa komai ba, damuwa saman fuskarsa.

Har Mu’azzam d’in ya soma juya motar ya dakata yana duban Musaddiq d’in dake nan tsaye wajen “Muje mai dropping naka..” Kasancewar da motar Mu’azzam d’in suke tafe.

Musaddiq ya girgiza kai yace “No you go ahead, I’ll take a cab.. Naji wayan naka sounds serious.”

Mu’azzam ya d’an dubesa kafin ya jinjina kai yace “Ka kula..”

Jinjina masa kai kurum Musaddiq yai kafin Mu’azzam d’in ya shige.

Musaddiq ya shafi fuskarsa da tafukan hannayensa yana mai furzar da fuci a hankali.
**

Dr ya k’araso ya tadda Aunty Larai da Assad suna jiran ba’asi daga garesa.

Suna ganinsa suka mik’e tsaye Aunty Larai na tambayan jikin Sadiyar.

Dr ya d’anyi gyaran murya yana fad’in “Kar ki d’aga hankalinki is nothing serious.. Hasalima ba abin d’aga hankali bane abun farin ciki ne..” Ya d’anyi fasali yana dubansu yanda suke duban nasa da mamaki sun kawo mutum asibiti ruwa ruwa kuma yace ba abin tashin hankali bane.

Aunty Larai ta katsesa “A’a ban gane ba Likita.. Mu kawo yarinya ruwa ruwa irin haka kace ba abin d’aga hankali ba Yo abin meye..?”

Dr ya murmusa yana dubanta sai kuma yace “Haba Hajiya ke ai na zaci kin d’ago mai nake nufi idan shi mijin nata bai d’ago ba..” Ya k’arashe yana duban Assad dan a nasa zaton Assad ne mijinta.

Assad yai saurin girgiza kai yana fad’in “A’a bani bane mijinta..”

Dr yace “Oh, ina mijin nata..? I need to have a word with him..”

Dr bai kai aya ba suka sinkayo muryar Mu’azzam da k’arasowarsa kenan daga bayansu yana fad’in “Gani nan.. Ni ne mijinta.. What’s wrong with my wife..?”

Yana k’arasowa Assad Sai ya d’an dubesa yana sakin murmushi k’asa k’asa yasa kai ya fice dan ya kula al’amari ne da ya shafi mata da miji.

Aunty Larai kaw tuni ta soma Washe baki dan itama zata iya ce ta d’ago jirgin likitan.

Dr ya dubi Mu’azzam yace “Da fari zanso na fara da congratulating d’inka, amma kafin Nayi wann zanso na tambayeka Maiyasa ake barinta haka babu abinci a system d’inta a yanayin da take ciki wanda ba lafiyarta kawai ba harta jaririn dake cikinta zai iya affecting.”

Saida Mu’azzam yaga wani haske ya gifta ta saman idonsa, ya kuma duban Likitan da tsananin mamaki yace “Dr mai kace.. Did you say my wife is pregnant..?”

Dr ya murmusa yace “Da alama dai yanzun ne kuka sani, koda yake ba lallai ku fahimta ba sabida she’s just in her 4th week.”

Dr yaci gaba da fad’in “Cikinta lafiya lou yake. Ta sume ne sabida babu abinci a system d’inta, amma mun saka mata drip, idan ya k’are zuwa anjima zaku iya tafiya.”

Mu’azzam kam ya kasa komai sai duban likitan yake full of surprise. Yayinda Aunty Larai wacce ta gaza b’oye Farin cikinta ta shiga tambayan likitan ta ina d’akin da aka kwantar da Sadiyar yake.

Dr yai mata nuni da hannu yana mata bayani. Aunty Larai ta shige murna fal zuciyarta.

Ya dawo da dubansa ga Mu’azzam da har lokacin ke tsaye wajen kaman an dasa.. Labari mai dad’i a tsakankanin tashin hankali.. Wai Sadiya nada ciki.. Ikon Allah, Mommy Ta cire cikin Safeenah gaban idanunsa Sai ga wann labari da ya riskesa tun kafin wayewar gari.. Allah kenan mai gudanar da al’amarinsa yanda yaso.

“Thank you for this wonderful news Dr..” Mu’azzam ya fad’i yana mik’awa likitan hannu sukai masabaha.

Dr ya jinjina kai murmushi saman fuskarsa “Congratulations once again.. And please a dinga kula da cin abincinta da abinda take so.” Ya k’arashe da d’an zolaya.

Murmusawa Mu’azzam yai yana jinjina kai “Za’a kiyaye in sha Allah Dr.. Can I see my wife..?”

Dr ya jinjina kai yana mai nuna masa hanya “This way please.”

Mu’azzam ya kuma masa godiya kafin ya nufi d’akin.

Kwance ya hangota saman gado drip d’aure hannunta na hagu.

Aunty Larai Ta dubesa da murmushi yanda yake takowa cikin d’akin “A’a Inspector an shigo.?”

Ya murmusa kad’an yana gaidata.

Ta amsa cikeda fari’a tana k’arawa da “Aaah lallai mission yayi kyau, Masha Allahu..”

Ya sadda kansa kad’an yana d’an shafa kai. Murmushin bai bar saman fuskarsa ba.

Aunty Larai taci gaba da fad’in “Masha Allah.. Ubangiji ya sanya masu albarka.. Allah ya rabasu lafiya yasa a haifo masu albarka.”

Ya d’an duk’ar da kai kad’an yana amsawa da “Ameen Aunty..” idanunsa naga Sadiya wacce ke kwance tana shan drip idanunta a rufe irin na mai bacci, fuskar nata har ya d’anyi fayau dashi.
Chapter 129 · 0% Book details