← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 175

Sashe 101

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Alright Yusuf.. Eh gobe in sha Allah ina nan tafe.. Thanks for the update, Sai munyi magana..” Daga haka katse kiran yai ya k’araso saman gadon ya zauna yana kuma shafa wayar tasa.

Sadiya tana jin haka ta rintse idanunta a hankali hawaye na gangaro mata, kar dai tafiya zaiyi.? Kardai fushin da yai da ita har ya kai wann matakin kan kawai Ta masa maganar Safeenah.. Kukan da take ta k’ok’arin dannewa ya soma fin k’arfinta.

Ya daina abinda yake ya karkato kad’an yana dubanta. A hankali ya migrino kusanta nan saman gadon. Tana jin alamun k’arasowarsa kukanta ya k’aru.

Bai furta komai ba Sai janyota dai cikin jikinsa, kaman wanda yace ta k’ara. Tana nan cikin jikinsa bai hanata kukan ba har dai kukan nata ya soma lafawa a hankali.

Ya d’an d’ago fuskarta yana duba had’ida saka tafin hannunsa guda yana share mata hawayen “Tell me.. What happened why are you crying..?” Ya tambaya yana share mata hawayen.

Ta d’an dubesa sai kuma ta girgiza masa kai.

Ya gyara zamansa cikin gadon yana mai mata matashi da b’angaren jikinsa. Ya kamo yatsun hannunta guda yana murzasu cikin tafin hannunsa a hankali.

“Tafiya zakayi ka barni..?” Ta tambaya cikeda rauni.

Ya d’aura hannunsa guda saman sumarta yana shafasu a hankali “Kan wann kike kuka kike mu nasaran hawayenki masu tsada..? Kiyi hak’uri tafiyar ne ta taso min babu shiri. Naso na zauna mu k’arashi hutun mu tare but babu yanda na iya akwai ayyuka da suka taso mun.. And akwai wasu adjustments da nakeson yi kafin ki koma.. As soon as everything is done zan turo a d’aukeki..”

Ta d’an dubesa kafin ta jinjina kai a hankali “Bakayi fushi dani ba..?”

Murmusawa yai yana dubanta kafin ya d’an ja hancinta kad’an Sai ya kuma janyota jikinsa yana fad’in “Come here.” Ya mak’aleta cikin jikinsa ya matseta sosai yana shak’an k’amshinta. Idanunsa a lumshe yake fad’in “I’ll miss you Beautiful..”

Tai kwance cikin jikinsa yana narkar da ita da kalolin k’aunarsa. Jin zancen ya soma canzawa ne ya sanyata saki masa kuka. Cikeda tsoron yanda tasha wahala first time.
Kansa na nan saman k’irjinta, idanunsa a lumshe yake furta “It’s almost a week fah.. Nayi k’ok’ari ai.. Please ki barni muyi sallama..”

Kuka ta kuma fashe masa dashi tana fad’in ita dai tsoro take.

“Babu abinda zai faru I promise..” Ya fad’i yana kuma rikitata.

Ta d’an turasa kad’an cikin dabara tace “Nifa bana sallah ma ashe.” Tai maganar duk a tsorace.

Ya d’ago yana dubanta da mamaki kafin ya murmusa yace “Haba yarinya ma wa zakiyi wann wayon.. Ance miki bansan date d’inki bane..”

Ta d’an waro idanu tace “Yaushe ka sani..?”

Ya murmusa yana mai kuma janyota jikinsa “The very first time dana soma had’uwa dake.. A ranan kika sanar dani date d’inki..” Ya k’arashe yana mai kashe mata ido guda.

Ta murmusa tana rufe fuskarta da tafukan hannunta, sai kuma ta d’an Ware idanun ta narkar da murya kad’an tace “Kai Inspector ni dai gaskiya bansan yaushe akai hakan ba..”

Ya d’an janyota yana fad’in “Kin mance da mai kika jifeni first had’uwarmu..”

Sai lokacin take recalling abubuwan da suka faru. Ta zaro idanu cikeda kunya sai kuma ta kifa kanta saman cinyarsa cikeda kunya tana fad’in “Na shiga uku Wai dama a kai nai jifan nan.. Innalillahi..!” Ta kuma danne kanta cikeda kunya tana maganar tamkar zata sakar masa kuka. Shiko sai k’ok’arin d’agota yake yana murmusawa.
Sai wann lokacin take tuna abinda Safeenah tai mata data tura mata sanitary napkin a baki tace sai ta cinye.. Wato ashe Inspector ta jifa dashi ya tafi gida da abin har Safeenah watak’ila Ta gani..Kunya ya kuma dabaibayeta.

“Dama nasan bakisan Kinyi haka ba. But ni tun a lokacin na rik’e date d’in nasan bazaki shige wann range d’in ba.. So you don’t have any excuse idan kuma ba rowa zaki min ba..”

Ta marairaice fuska kaman zata saki kuka “Nidai tsoro nakeji..”

Shima marairaice mata fuskar yai yace “Matar Inspector bata tsoron mission.. I promise you bazai kai wancan ba.. Trust me..” Ya k’arashe cikin nuna mata salon k’aunarsa.

Iya juriya da dauriya kam tayi shi, saidai kaman yanda yace d’in bai Kai karon farko ba saima k’ok’arin maida masa Martanin k’aunar nasa gareta da take. Albarka ya dinga saka mata ya matseta tsam cikin jikinsa yana fad’in irin kewarta da zaiyi. Komai tare sukai itada Inspector d’in nata.. Kama daga wanka zuwa shiryawa dukda cewa da k’yar ta bari hakan ta kasance sabida kunya. Zallan k’auna mai tsafta had’ida tsayawa a rai yake nuna mata. Tabbas sunyi sallama mai tsayawa a rai da zai sakasu kewar juna matuk’a.

Kafin Mu’azzam ya tafi saida ya bar mata amanan kanta da kuma Mamynsa. Sann ya sake dank’awa Inne amanar Sadiyar tasa. Kuka da shagwab’a kaw haka ta dinga narka masa da k’yar ya samu sukai sallama da k’udirin zata biyosa nan bada jimawa ba cikin yardar Ubangiji. Dan ba don aikin dake gabansa ba da k’afarsa k’afarta bazai tafi ya barta ba Amma babu yanda ya iya abubuwa suna neman fita out of hand tinda ya taho.

Mu’azzam ya tafi ya barta da tarin kewa.

**
Tinda Shemau ta sanar da Safeenah dawowar Mu’azzam d’in ta k’udiri niyyan komawa gidanta, sann wancan ‘yariskar Wato Sadiya kenan ta fita da fitar ta kaman yanda Aunty Nuratu ta fice daga gidan mahaifinta. Koda wasa bazata bari ‘yariskar can ta dawo mata cikin gida ba dan dama ta k’udiri alwashin gidanta tamkar dai GIDAN ARO yake a wajenta sai ta fice ta bar mata gida.

Da wann tinanin Safeenah ta shirya tsaf ta nufi gidan. Saidai tana isa ta tadda kayan tashin hankali domin kaw kaf kayan gidan Mu’azzam yasa anata fito dasu, daga gani ma’aikatan company ne masu aikin interior design. Sai zuba sabbin furniture ake ana sealing nata cikin manyan cartons ana shiryasu a cikin wata k’atuwar mota. K’irjin Safeenah yai wani irin tsinkewa.

A fujajan Ta nufi cikin gidan tana tambayan mutanen wanda ko kallo bata ishesu ba.

“Ina zaku kai mun kaya..? This is my house.. Who ordered you to do this..? Kai magana nake maku..!”

Bata kai aya ba taji sauk’an k’aton abu kusan k’afarta.

Tai tsaye tana duban hoton aurensu da ya fad’o kusan k’afarta wanda ko shakka babu jefosa akai.

Da mamaki ta d’ago tana duban Mu’azzam dake tsaye yana dubanta. Ta duk’a a hankali tana Shafa hoton auren nasu hawaye na gangaro mata.

Lokaci guda ta mik’e tana girgiza kai tana hawaye. Ta isa wajen Mu’azzam a guje tana kamosa “My Halal.. Zaka canza mana tsarin gidan ne.. Please kar ka cire hotonmu ko sabon hoto kake so muyi a manna.” Tana maganar tana murmushi hawaye na zubo mata.

“Safeenah, I’m not changing anything for you.. it’s over between us.. Kin fahimta..”

Kuka ta fashe dashi gadan gadan tana girgiza kai tana hawaye “No it’s not over.. You are mine Mu’azzam..! You are my Halal bazan tab’a k’yaleka ba.. Kai nawa ne ni kad’ai.. My Halal please don’t leave me kaji. Wllhi ina maka son da banayi ma kaina..” Ta k’arashe tana kamo arms d’insa had’ida jijjigasa.

“Enough Safeenah..!” Ya fad’i yana cire hannayenta daga jikinsa, yaci gaba da furta “This is not love Safeenah.. You don’t love me, you are just obsessed with me.. And.. And this is just a crazy feeling not love.. If you can point a gun at me mai kike tunani Safeenah.. zaki kira wann abun love.. Ba love bane it’s just an obsession.. Please Safeenah you need to accept this.. Kafin Azo ana danasani gwara ya tsaya a nan.. You are like a sister to me and I don’t want to hurt your feelings.. I don’t love you as a woman please..” Ya k’arashe cikin sigan kwantar da hankali.

Zabura tai tana mai kuma fashewa da kuka ta ciccib’i hoton nasu tana k’ok’arin maidasa Majinginansa “You are just lying.. I know you love me kawai wancan ‘yar iska karuwarce Ta karkatar maka da tunani.. Tambad’add’iya wacce ta gama watsewa a layi.. Ba dole ka mance kanka ba taje tana maka abubuwan da karuwai matan layi keyi Wanda ni bana maka irinsu koh..!”

Fincikar hoton yai ya kuma jifa dashi. Yana nunata da ‘yar yatsa cikin sakin huci “Don’t make me lose my mind Safeenah..! Kar ki sake kiran matata Karuwa.. Sabida matata sabuwa ce, first grade ce, fresh ce.. Sann ni ne mutum na farko da ya mallaki darajarta.. Idan akwai wacce za’a kira tambad’add’iya a nan wacce ta gama watsewarta a club da parties ba kowa bace face ke, kin zaci na yarda da labarin da kika bani ne cewa an miki fyad’e wajen party..?” Ya girgiza kai kafin yaci gaba da fad’in “I didn’t believe you one bit Safeenah.. Kar ki mance I’m a Detective na sani if someone is not telling the truth.. Na miki uziri ne na kauda kai sabida girman zumunci.. Amma kinata pushing d’ina, kinata yin wasu abubuwa baya albarka kike ci.. Zaman bazai yuwu ba Safeenah ya riga ya k’are.. Sann da Mommy take cewa kar na shafa miki cuta.. Ni ya kamata na guje ki dan kar ki Shafa min cutan da kike d’ebo wajen yawon parties da samaruka..!” Ya k’arashe idanunsa tar a kanta yayinda Safeenar tai tsaye tamkar wacce ruwa ya shanye tana zuban hawaye.

“Zo ki fice mun a gida..!” Ya k’arashe yana nuna mata k’ofa.

Cikin tsananin sanyin jiki ta nufo k’ofar tamkar wacce ruwa ya shanye.

Saida ta kai k’ofa ya dakatar da ita. Hoton ya jifa mata bayan ya yage b’angaren nasa fuskar yace “You forgot this..”

Safeenah na hawaye Ta dubi hoton sai kuma ta d’aga ido ta hangi ma’aikatan daga can sun ciro wani sabon hoto cikin frame suna k’ok’arin mannawa a wajen. Kuka bai kuma zuwa mata ba saida ta hangi hoton Mu’azzam d’inta da wancan tsinanniyar ce da suka d’auka a park irin Wanda Ta k’eta kwanakin baya shine aka lik’a a wajen anyi enlargement an saka cikin k’atoton frame kaman ka kirasu su Zo.
Chapter 101 · 0% Book details