← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 175

Sashe 79

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ajidde ta saki baki da hanci tana duban Mama Hindu.. Sai kuma ta girgiza kai tace “Mama Hindu kina nufin ‘Yaniskan turawa shi ya bada wannan dokar..?”

Mama Hindi Ta girgiza kai tace “Sunansa Mu’azzam.. Ki daina kiransa ‘Yaniskan turawa jami’in tsaro ne idan yaji kina kiransa haka zai kulleki a police station..”

Takaici ya cika Ajidde ta gama kula mutumin Babban D’an rainin hankali ne.. Wato kar Ta tab’a masa mahaifiya da datti jikinta sai tayi wanka.. Ta tab’e baki tace “Shi wannan sam halinsu baizo d’aya da abokinsa ba.. Ni banma San ya akai sukai abota ba..”

Mama Hindu ta girgiza kai tace “Waye abokin nasa..?”

Ajidde tace “Kuran tashe mana..”

Mama Hindu ta girgiza kai tace “Wannan wane irin suna ne kuma Ajidde..?”

Ajidde ta dubeta tace “Toh oho nima bansan sunansa ba.. Amma ai a gidan gonar nan yake aiki... Gashi tinda ya tafi garinsu fah har yau bai dawo ba.. Mama Hindu kinaga zai dawo..?”

Mana Hindu ta murmusa tace “Toh kodai shine ke sakaki tunani kwana biyun nan.. Da alama shine sirkin nawa..”

Baki sake Ajidde ke dubanta sai kuma ta rufe fuska tana dariya “Kai Mama Hindu.. Ni wllhi har kin sa naji kunya.. Kuran tashe Abokina ne kuma Yayana mai tare mun fad’a ehe..”

Mama Hindu Ta dara kad’an tace “Munsan irin wad’ann yayyen.. Da alama dama shine sirkin nawa.. Ke kaw ya akai bakisan sunansa ba.. Allah dawo dashi lafiya na had’u dashi..”

Ajidde Ta kuma darawa kafin tace “Kai Mama Hindu ni wllhi dariya da kunya kike bani.. Kuran tashe fah d’an gayu ne.. Saima randa zai tafi garinsu da na gansa.. Wllhi yasha gayu cikin kayan da ‘yan gayu ke sakawa kuma ma fah ya fini kyau.. Kinga dukda shi ba fari bane amma ya fini haske.. Kuma ya fini tsawo..” Ta k’arashe tana mai mik’ewa tsaye tana gwada tsawonta da tsayin k’ofa lokaci guda tana bayanin tsawonsa ma Mama Hindu.

Mana Hindu ta murmusa tana mai shigewa shiriritar Ajidde da yawa yake.

Ajidde ta Sauk’e ajiyan zuciya tana duban kanta jikin madubi tana mamakin Mama Hindu tace ta k’ara kyau.. Ta murmusa kafin tace “Yo dama ai ni mai kyau ce Mama Hindu..” Idanunta suka sauk’a Kan Aunty Nuratu sai taga kaman ita take kallo.. A koda yaushe idanun nata saidai kaga Sun kafe waje guda amma yau Sai Ajidde taga kaman dubanta take.. Ta k’araso a hankali tana mai k’ura mata idanu, Ta duk’a tana duban idanun Aunty Nuratu ta d’an soma Yawo da tafin hannunta saman idanun Aunty Nuratu sai taga kaman idanun nata na motsawa ba kaman ko Yaushe da zaka ga idanun tamkar a kafe suke waje guda ba.. Ajidde tai shiru tana tuna bayanan Malama Hafsah cewa ko taga wani canji a tattare da matar da take Jinya ta adana hakan ma kanta, kar tai saurin sanar da mutane dan daga yanda Ajidden ke mata bayanin ciwon ya mata kama da asiri ko tsafi.. Amma da taimakon ayoyin Ubangiji idanma asiri ne ko sihiri zai lalace. A hankali Ajidde Ta furta “Tabbas akwai waraka cikin ayoyin Ubangiji..”

**

ABUJA

Assad ya murmusa kad’an yana dubansa kafin yace “I’m feeling much better now.. Damuwata kawai shine we couldn’t catch Danger.. We were so closed k’iris ya rage mu kamasa ya tsere mana..” Ya k’arashe yana d’an fuzar da huci kad’an.

Mu’azzam ya girgiza kai yace “What’s important a halin yanzu shine lafiyarka.. Let’s all take a break.. Na tabbata a kwana a tashi zamu had’u da Danger watarana..”

Assad ya jinjina kai kad’an kafin yace “Su Hajiya sun taso daga Nasarawa d’azu Shaheed ke sanar dani a waya, anjima kad’an nasan zasu iso.. Yarinyar nan ne mai shegen magana Humaida ita ta sanar da Hajiya. Kuma saida nai warning nata kar ta sanar dasu Hajiya amma ta sanar dasu..”

Mu’azzam ya d’an murmusa kafin yace “Hajiya ai bazata iya bacci ba tareda ta ganka ba..” Mu’azzam bai rufe baki ba ‘yan gidansu Assad sukai sallama, Hajiyarsa wacce itace mahaifiyar Sai K’aninsa mai bi masa Shaheed wanda shi ya tuk’o Su Hajiyan sai ko k’anwarsa Humaida... Suka shigo duk a rikice..

Assad na wurga ma k’anwarsa harara ganin yanda mahaifiyarsa duk Ta rikice. Ta dubi Mu’azzam bayan sun gaisa tace “Ni wannan aiki naku harga Allah tsoro yake bani.. Shin bazaku aje aikin nan ba ku nemi wani. Aiki kullum cikin fargaba da tashin hankali..”

Mu’azzam sai murmushi yake ba tareda yace komai ba, shi ko Assad girgiza kai kurum yake yana fad’in “Hajiya babu wani abu fah mun saba da wannan cikin aikinmu..”

“Kai tafi can ka rufe mun baki.. Rai guda d’aya ce. Ba wannan ake jiye maku ba.. Aikin tsaro a k’asa irin wannan ai abin tashin hankali ne k’ananan suke shan wahalan ba manyan ba.. Allah dai ya kawo mana d’auki ya bamu shuwagabanni adilai..”

Gaba d’aya suka amsa da Ameen kafin daga bisani Mu’azzam yai masu sallama Shaheed k’anin Assad yai masa rakiya zuwa waje.

**

Bayan sallar isha ya dawo gidan, tin daga k’ofa yake jiyo hayaniyar Mommy tana fad’in sai Safeenah ta tattaro kayanta Sun tafi.. Yanda Ta bar gidan Daddy dole Safeenah ma Ta bar gidan Mu’azzam tinda dik abinda ke faruwa akan Mu’azzam d’in ne..

Yai sallama ya turo k’ofar parlorn.

Safeenah tana ganinsa Ta nufosa a guje tana b’oyewa bayansa fuska shar shar da hawaye “My Halal pls don’t let Mommy do this.. Dan Allah kar ka bari Ta rabamu..”

Mommy na sakin huci take duban Mu’azzam d’in “Kinaji Safeenah idan ni na haifeki kin gama zaman aure da wannan maras mutuncin.. Ki shige mu tafi bana son wani dogon bayani..”

Safeenah Ta kuma fashewa da kuka tana fad’in “Mommy no please.. Wllhi I love my husband.. Please don’t make me choose between you..”

Mommy Ta jinjina kai tana huci “Yayi Safeenah.. Duk Kun juya mun baya akan wannan maras mutuncin.. Yayi.. Baga mahaifinku ba bagaku ba.. Yayi kyau.. Kije Safeenah indai namiji ne gaki gashi nan.. Ina nan zaki Zo min kina kuka..”

Ta juyo tana duban Mu’azzam.. Murmusawa tai kafin tace “Bokanka ya iya aiki matuk’a Mu’azzam.. Da alama ka lashe zukatan ahalina.. Bazan tab’a yafe maka ba tarwatsa mun kan ahali dakai..”

“Ke kuma Safeenah na barki da namiji..” Tana ida fad’in haka Ta fice tana sakin huci..

Safeenah Ta fashe da wani irin kuka tana mai duk’awa wajen..

Hannun Mu’azzam taji saman kafad’unta.. Ta d’ago tana dubansa wani kukan na zuwa mata.. Mik’ewa tai Ta fad’a jikinsa tana kukan mai isarta.

A hankali ya d’ago hannayensa ya rungumeta cikin jikinsa.

For the first time da yaji tausayin Safeenah ya d’arsu cikin zuciyarsa tun bayan da binciken mutuwar Ikram ya biyo kanta.

SameenaAleeyou📚

*GIDAN ARO*

*42*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Meema da Kiki suna zaune parlorn sunyi jigum jigum, harda guntun hawaye a fuskokinsu.. A haka Musaddiq ya shigo ya taddasu. Bai ce masu komai ba suma basu ce masa komai ba, ya haura sama ya nufi d’akin Mommy yana dubata, bai sameta ba sai wata mai aikin gidan guda d’aya tana tattara d’akin Mommyn yanda Mommy tai fashe fashen abubuwa masu fashewa a d’akin dangin su frames dasu flower vase.

Musaddiq yanata bin d’akin da kallo cikeda mamaki. Lokaci guda ya girgiza kai yace “What happened here.. Ina Mommy..?”

Mai aikin Ta girgiza masa kai alamun bata san yanda Mommy take ba.

Bai kuma cewa komai ba ya fito ya sauk’o k’asa ya taddasu Meema dake zaune jigum jigum ko wacce da kalar tagumin da tai..

“Kai ina Mommy..?” Ya tambaya yana dubansu.

Meema Ta girgiza kai tace “Bamu San ina ta tafi ba.. But she says bazata sake dawowa gidan nan ba..”

Da tsananin mamaki Musaddiq yace “Mommyn.?”

Suka jinjina masa kai.

“Toh mai ya faru..? Maiyasa Mommy zatace haka..?”

“Muma bamu sani ba kawai daga side d’in Daddy mukaga Ta fito tana kuka..”

Kallo ya bisu dashi kafin ya zaro wayarsa ya soma dialing layin Mommy.. Bugu d’aya a na biyu ta d’aga.

Musaddiq hankali tashe yake fad’in “Mommy ina kika tafi..? Nazo gida na tadda baki nan.. Yaran nan sunce min Wai kince bazaki sake dawowa ba..? Mommy what is happening..?”

Maimakon ta basa amsa sai kukan da tai tana fad’in “Musaddiq Daddynku yaci zarafina.. Yamin abinda bai tab’a min ba tinda k’uruciya.. Ko kasan yau har marina yai akan Mu’azzam.. Ka kula da ‘yanuwanka amma nikam na gama zama gidan Mahaifinku.”

Da tsananin mamaki ya saki baki yana sauraron Mommy abinda bai tab’a faruwa gidansu ba, Wai Mommy ta tafi ta bar gidan kuma bazata kuma dawowa ba “Mommy where are you now..?” Ya tambaya yana ficewa.

“Ina Apo gidan Hajiya Faty K’awata..” Ta basa amsa kai tsaye.

“Alright gani nan zuwa Mommy..” Daga haka katse kiran yai ya kuma ficewa daga gidan ya nufi gidan Hajiya Faty kawar mahaifiyarsa.

Musaddiq yai jigum yana duban Mommy yanda take nuna masa farar fuskarta da zanen yatsun mijinta ya fito.

“Daddy ne ya miki haka.?” Musaddiq ya tambaya yana dubanta idanunsa sunyi jazir sabida tsananin b’acin rai.

Ta jinjina masa kai tana kuma matsan k’walla “Dashi da Safeenah duk sun juya mun baya kan Mu’azzam, nasan kaima bayansa zakabi sabida shi d’angata ne bai laifi a idanunku..”

Mik’ewa Musaddiq yai kurum yana sakin huci yana duban fuskar mahaifiyarsa, jinjina kai yai kafin yace “Zaizo har nan ya baki hak’uri ya kuma d’aukeki ya maidake gidanki..!” Daga haka ficewa yai kaman zai kifa k’asa.

Mommy Ta bisa da kallo kafin Ta murmusa tace “Ai jini ba K’arya bane.. Uwa kuwa Ta wuce gaban wasa..” Hajiya Faty ta fito tana dubanta tana murmushi “Ina Musaddiq d’in.. Ko har ya fice ne ba sha ko ruwa ba.?”

Mommy Ta murmusa tace “Ya tafi yayi yak’i ma uwarsa..”

Hajiya Faty Ta dara kad’an tace “Kaji D’an halak haka ake so d’ah ya kasance. Kinga ko baki samu goyon bayan Safeenah ba kin samu na Musaddiq..”

Mommy ta jinjina kai tace “Ita dama wannan ai shashasha ce, kuma Ina nan dake zata Zo min tana kuka lokacin da zai gurza mata ya tabbatar mata cewa ya amsa sunan namiji..”
Chapter 79 · 0% Book details