← Book details Zabin Iyaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 145

Sashe 88

Zabin Iyaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Share pls
IN IYAYE*
_Parental choice_
*NA*
*JAMEEY*
*BOOK ONE*
_Bissimillahir Rahamanir rahim_
https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ?mode=ac_c
Bayan sun dawo sama kwantar da kanta tayi saman cinyarshi tana kallon wa'azin da ya kunna masu ita dai kallo take amma sam ba saurara take ba dan hankalinta baya a jikinta kwance kawai take tana neman mafita a rayuwarta tabbas gaskiya su Mubina suka gaya mata wannan ce damar da zata samu shakuwa ta shiga a tsakaninta da Umaima wannan ce babbar damarta da zasuyi soyayya mai
arfi da Umaima da har zata kaisu ga aure wannan ce damarta da zata saka Umaima taji bata iya rayuwa sai da ita to amma taya?taya duk zata yi hakan bayan ta fara lura da Umaimar bata son ma takura ko ka
an,taya zata saka shakuwa da yadda mai karfi a tsakaninta da Umaima? dole ta sake taku dole ta dawo a cikin natsuwarta da hankalinta tasan mai ya dace ace tayi tun dare baiyi mata ba,dole ta danne duk abinda take ji na soyyayar Umaima tayi abinda yace tayi idan har ba haka ba kuwa zatayi asarar da ba zata ta
a yafe ma kanta ba,sai kace ba ita bace Malika Omar Yaushe ta sauya take neman maida kanta lusara irin haka?ita a yanzu Usman ba matsalarta bane kuma ba damuwarta bane dan ta gama da shafin shi tunda ta shigo gidan yanzu babbar matsalar da take gabanta da kuma damuwarta samun Umaima shine babban gurinta ta samu ta mallake zuciyar Umaima ta mamaye ko ina Umaima taji bata son ba kowa kanta sai ita shine damuwarta kuma dole ne Umaima ta zamo tata ita
aya ba zata ta
a sharing din Umaima ba,ba zata iya zuba ido tana kallon wani na kwanciyar aure da Umaima ba, ba tare da kuma ta
auki mataki ba tana jin bata iya jurar ranar da kwana nan Umaima zaizo ba tana ganin kamar ha
iye zuciya ma zatayi ta mutu dan ba
in ciki..zama tayi tana kallon Usman tana amsa kiran da yayi mata numfasawa Usman yayi yana cewa."Dan Allah Malika ki
ara kokari wajen gaya ma Umaima sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ki
ara nuna mata Maiye ma sunnar baki
aya dan Umaima tana bukatar sanin haka kuma sai kin
ara hakuri da ita da janta a jiki dan ita bata da yawan magana bata kuma son jama'a haka halinta yake."Murmushi tayi mai sauti tana cewa."Wanann ba damuwa bane in shaa Allah zan fara yi mata kissar annabawan Allah da yanda sukayi rayuwa da matayensu da kuma abokan zamansu in shaa Allah nasan zata karu sosai kuma zata cire duk wani kishi da ke zuciyarta muyi zama tamkar jini
aya dan ni Umaima tayi man naga tana da hankali bata da hayaniya ba ruwanta zanyi ko
ari sosai naga mun zauna lafiya da ita kuma ko ba komai Umaima ai Kanwata ce kuma jininka ce Jarumina."Ha
e kawai bakinsu yayi waje
aya yana tsotsa dan baida abinda zai iya yi ma Malika sai addu'a dan ta kai a kirata da mace ta gari yana fatan kafin barin Umaima a gidan ta kwashi ilimi a wajen Malika wanda zai taimake ta watan watarana kuma yana son su shaku su zama tamkar yan'uwa yanda ko bayan rabuwarshi da Umaima alaqarsu ba zata wargaje ba,dan yasan sakin Umaima zai iya shafar Malika a familynsu amma ita Umaimar da kanta zata wanke Malika a wajen Dada har su sake da ita su maidata yar'uwa...Usman bai fita gida ba sai la'asar ya kuma
gaya ma Malika da tayi ma Umaima
ari dan zai kai dare bai dawo ba zai biya gida kuma zasu je godiya a gidan su Malika din, Cikin farar shadda gizina ta taimaka mashi ya shirya da babbar riga sannan ta
aura mashi dark-blue hula da tayi dai-dai da takalmin shi suka hau da watch din shi Rolex,rakoshi tayi kasa kallo
aya Umaima tayi masu ta dauke kai tana cigaba da shan pawpaw juice din tayi, tsayawa yayi a gabanta yana cewa."Zan fita Malika zata yi maki
ari anjima."Gya
a kai kawai tayi tana cigaba da shan juice dinta, kallon Malika yayi sai kuma ya janyota jikinshi yana kissing dinta yana cewa."Sai na dawo Gimbiyata."Allah ya tsare mana kai ya dawo mana da kai cikin koshin lafiya."Da Amin ya ansa yana fita yana auna irin girman rainin da Umaima take mashi,taya yana mata magana amma bai da arzikin da ko okay zata ce mashi sai ma ta shareshi,idan har bai taka mata birki ba to zata koyama Malika ne ta janyo mashi raini yana zaune da matarshi cikin so da kauna da mutunta juna idan yayi sake rashin kunya Umaima zata koya mata.

Zama Malika tayi tana cewa."Umaima."Kallonta Umaima tayi tana ansawa tana cewa."Amarya."Dan jim Malika tayi sai kuma ta numfasa tana cewa."Usman yace man zanyi maki
ari."Jinjina kai Umaima tayi tana cewa."Ai najishi." Daga haka bata sake cewa komai ba, Furzar da numfashi Malika tayi tana cewa."Okay."dan shiru ne sukayi na mintoci sai kuma Malika tace."akwai littafan addini wane kike son ina maki
ari kullum koda yana gida dan yana da kyau sosai bayan Alqur'ani mai girma a ha
a da su sira Hadith tauhiq da dai sauransu."Kallonta Umaima tayi na minti biyu tana dauke kanta tana cewa."Malika ko?"Daga kai Malika tayi tana sakin murmushi dan tunda take bata ta
a jin sunanta yayi mata da
i ba sai da Umaima ta fadi sai taji ma Umaima tafi kowa iya fadin sunan bata
i taita fadi ba, kure Umaima tayi da ido tana sakin murmushi, gya
a kai Umaima tayi tana cewa."Nagode da gudunmawarki a gareni amma na iya littafai sannan kuma ko
arin da yake cewa kiyi man shima nagode ba sai kin wahalar da kanki ba."Girgiza kai Malika tayi taa cewa."Haba Umaima maiyasa kike haka?hakan ba daidai bane kuma ai ilimi deji ne ba komai ake sani ba nidai inason na samun ladar kiyi hakuri muna karatun nima zaki koya man inda ban sani ba kinga zamu Karu da juna kuma zamu samu ladar juna."Dan shiru Malika tayi tana mai matsawa ka
an kusa da ita tana cigaba da cewa."Kamar yanda na gaya maki dazun zan kuma maimaita maki ban maki kallon kishiya kallon yar'uwa nike maki kema ki bani ha
in kai mu cure waje
aya dan korar she
an a cikin gidan nan muna
aruwa da juna shine zaman tare Umaima."Kallonta Umaima tayi sai ta
aga mata kai tana sakar mata da murmushi, sauke numfashi Umaima tayi tana sakar mata da murmushi itama tana cewa."Nagode ke mutumniyar kirki ce Malika."Murmushi ta saki tana cewa."Kema ai mutumniyar kirki ce Umaima ai amfanin zaman tare a musulunci shine a Karu da juna ta ko ina kuma a zauna da juna lafiya tsakani ga Allah tabbas akwai kishi amma sai asan yanda za'a yi ya
i da kishin."Gya
a kai kawai tayi tana tashi tana cewa."Haka ne balle kuma ni ban kishi dake,bama ke ba kowa Yaya Usman zai kawo gidanan ba zanyi kishi ba tunda Allah yace suyi hu
u kinga daman ban sa ran zan zauna ni
aya ba."da kallo kawai Malika ta bita tana sauke numfashi dan ta fara gano hanyar da zata bi ta shiga jikin Umaima har ta yarda da ita yarda ta har abada.
Chapter 88 · 0% Book details