Sashe 49
Zabin Iyaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Share pls IN IYAYE* _Parental choice_ *NA* *JAMEEY* *BOOK ONE* _Bissimillahir Rahamanir rahim_ https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ?mode=ac_c Riko shi Daulah tayi tana cewa."Myluv barta haka ni yunwa nike ji kuma moimoi da stew nike son ci."kallon Daulah yayi yana cewa."Wifety da kin barni na koya mata hankali har ta isa ta mareki?"Ita dai Raihana tana du e kasa tana kuka matsawa yayi yana kamo kunnenta ya mi e tsaye da ita yana cewa."Daga yau idan har Babe tayi maki magana kika ce zaka yi mata wani abu sai nayi maki abunda yafi wannan sakara jakka ke wacece a gidan nan inba yar aikin gida ba da har zata zo tayi maki magana zaki aga hannu ki mareta ke din banza dan ubanki!dan ubanki daga yau idan har muka tashi bacci baki gyara gida da ha a mana breakfast ba sai na taka ki zaki tashi kiyi mata moimoi ko sai nayi ball dake na karya afafun."Tashi Raihana tayi tana goge hawayen fuskarta kitchen kawai ta dosa dan fara hada breakfast din koda ta shiga dafe kanta tayi dan ciwon da yake mata sosai bata ta a yin ciwon kai irin na yau ba amma a haka Raihana ta samu ta fara kokarin ha a alale tana yin bleeding din wake tana kuka haka ta gama ta ha a sannan kuma ta koma ta fara shara suna zaune parlo rungume da juna suna labari suna dariya haka ta fara gyarawa daman wajen ya dan aci ka an duba da yan kawo amarya da suka zo harda yara a hankali tana gyarawa tana dubo girkinta har ta samu ta gama ta goge ko ina ta kunna turaren kamshi sannan ta jera masu komai a saman dinning sannan ta shige room dinta wannan karan key ta saka ta barshi jikin kofar wanka ta shiga ta gasa jikinta dan ta gaji sosai ta samu ta saka doguwar riga marar nauyi sannan ya ha a tea ta sha ta sha magani ta koma ta kwanta tun tana tunanin rayuwar da take a gidan Raihan da wata hanya zata bi dan samarma kanta mafita ba tare da Dad ya ga laifinta ba dan ita damuwarta Dad ne ta tabbata idan yanzun ta kira Abbie tace mashi bata son auren tabbas zai sa Raihan ya saketa to ya zatayi da Oba?tunawa tayi da irin warning din da Oba yayi mata akan tayi hakuri ta zauna da Raihan karda yaji kuma karda ya gani ko da ara bai yarda ta gaya ma Abbie ba shi ta kirashi idan kuma ta sake ta ha a da ubansa to shi ba zai yafe mata ba,kuka ta fashe dashi mai ciwo tana cewa."Innalillahi wa inna alaihirajiun ya Allah ka kawo man auki ya Allah kana gani duk wannan masifar da nike shiga na shigeta ne dan na faranta ma iyayena ya Allah ka kawo man agaji." Kuka take sosai a haka bacci yayi awon gaba da ita ta kudundune a cikin deveot sai sauke ajiyar zuciyar kuka take...inda suka ci abincin ana suka bar komai sun watsa wajen sun ata parlon kamar wasu kananan yara wai wasa sukayi duk sun tarwatse pillow din a carpet sannan suka koma ciki suka kwanta bacci ma ale da juna cikin so da kauna...A hankali ta bu e idonta tana duba time addu'a tayi tana saukowa a hankali saman gadon ta gyara sannan ya shiga toilet wanka tayo da alwallah sannan ta saka wata teabubu sosai atamfar ta haska ta,ta ara yi mata kyau turaruka ta shafa sannan tayi sallah ta fito kallon parlon ta tsaya yi tana kallon yanda suka maida parlon sai kace anyi dambe a cikin gya a kai kawai tayi tana fara gyarawa cikin natsuwa tana yi tana hutawa dan ba yi take ba ita bama tayi tunanin ta iya gyaran parlo ba a rayuwarta abinda tun da take a duniya bata ta a yi ba ita bata ganin daddati a gidansu komai a gyare yake, bayan ta gama ta maida parlorn tas ta shiga kitchen firar shinkafa ta dafa ta saka vegetable sai daukar ido take stew tayi mai dadi sosai duk ta zuba a flask ta kai a dinning ta ha a drinks ta kai da komai itama ta zuba nata ta shige ita dai mamaki take yanda har ta gama wannan abun aikin da ya dauketa kusa 2hr bata ga Raihan ya fito dan zuwa sallah ba dan tun fara aikinta tana jin ana ta sallah a masallaci girgiza kai kawai tayi tana shigewa dakinta bayan ta gama cin abincin ta maida komai kitchen ta wanke zata koma taga sun fito makale da juna sai zuba mashi shagwaba take yana biye mata murmushi tayi dan ita dariya ma abun yaso bata ashe Yaya Raihan ya iya soyayya haka? auke kanta tayi ta shige dakinta tana fatan dai sunyi sallah daga haka ta dauko wayarta ta hau waya da Rayyan tana tambayarshi yaushe zai dawo kasar,bayan sun gama ta kira Rahina suna cikin yin waya Raihan ya turo kofar yana cewa."Ke fito ki dafa ma Babe indomie bata son abinda kika girka ko dadi babu kin wani tashi kin cika mutune gishiri."Kallonshi tayi tana maimaita kin cika ma mutune gishiri stew din da ko gishiri ma bata saka mata ba,to taya har yayi yawa kuma?ihun da yayi mata yasa ta saki wayar saman gado tana saukowa ta fita zaune taga Daulah saman dinning sai yatsina fuska take ita a dole abinci ba dadi kallon banza Raihana tayi mata tana wucewa kitchen..kallon Raihan Daulah tayi tana dan shagwabe fuska tana cewa."Nidai Babe tuwo miyar kubewa nike son ci har indomie din ta fice man a rai."Murmushi Raihan yayi yana cewa."Wifety mai zakayi da tuwo kuma?"langwabar da kai gefe tayi tana cewa."kawai shi nike marmari sai kuma smooth din Banana da zuma."Gya a mata kai yayi yana cewa."Okay bari ta kowa indomie din ni sai naci sai tayi maki tuwon."gya a kai tayi tana shafa gemumshi tana bashi labari shi kuwa sai murmushi yake zubawa a hankali Raihana ta ajiye indomie din zata juya ta tafi ya dakatar da ita yana cewa."Ke."tsayawa tayi amma bata waigo ba ta tsani ke din nan da yake ce mata sai kace bai san sunanta ba,ai ko yana manta sunan kowa banda nata idan har kuwa zai iya manta sunanta tabbas zai manta nashi sunan maganar da taji yayi yasa ta waigo da sauri tana cewa."Yaya Raihan kaima kasan ban iya wani tuwo ba banma san ya ake yin shi ba."idan baki iya ba sai ki koya."Turo baki tayi tana cewa."Nidai gsky Yaya Raihan na gaji da wannan abun da kake man sai kace wata baiwa tun safe nice aya a gidan nan nidai wallahi ban wani girka tuwo idan tana son ci ai tana da hannu da kafafu kuma ta ga hanyar kitchen nan taje tayi da kanta amma ni ban iya ba bansan yanda akayi ba."tasowa yayi kanta da gudu ta ruga ta shige room dinta ta saka key tabar shi jiki koda ma ya danna remote dakin ba zai bu e ba,ta gwanmace ya duketa da tayi ma matarshi tuwo kuma ta tabbata ba wani gishiri da ta zuba ma stew kawai munafunci ne yasa tace bata iya ci gishiri kuma sai a maida ta machine ai koda machine in ne ita ai yaci ace ta huta balle kuma ita ba machine ba balle kuma engine...jin ta sakama dakin key yasa ya jiyo baice komai ba sai hakuri da ya ba Daulah ya kuma ce mata karda ta damu zai kama Raihana shi yasan mai zai mata lailashinta yayi ya samu taci indomie din sannan suka kunna kallo kiran sallar da akayi yasa Raihan tunawa baima yi azahar ba,da sauri ya tashi dan zuwa yayi salloli ita kuwa Daulah ko a jikinta gyara zamanta tayi tana cigaba da Kallonta dan ita rabon da tayi salla ma randa ta fara ganin Raihan taji ta kamu da sonshi bokan da yayi mata aiki kan Raihan ya hanata sallah kuma ba zatayi ba dan idan har tayi gigin yin salla to abunda ke jikinshi zai are ne kuma ita ku i take son tayi daga jiya zuwa yau kawai har ta samu kyautar 30M a wajenshi sannu a hankali dai duk da yanzu hankalinta ya koma yanda zata fitar da Raihana a gidan dan kuwa ba zata yarda ta kulla koda wata bane a gidan Raihan tare da Raihana ba zata yarda ba dan kyaun yarinyar yana bata tsoro gashi ta mallaki duk abinda Raihan yake bu ata a jikin mace dolenta ta tashi tsaye bazata zuba ido ba wai ace haka zasuyi rayuwar da Raihana ai watarana ake gudu kuma dan gobe ake wanke tukunyar dare. *BAYAN WATA BIYU* Yau watan Malika biyu da fara zuwa islamiyyar su Usman kuma sannu a hankali duk ta saba da malaman islamiyyar dan kuwa tarbiyyarta daban take da sauran ga hankali ga natsuwa ga kuma ilimi,shiyasa a cikin wata biyu Malika ta shiga zuciyar malamai da dama gashi har wata gasa aka je ta kuri'ani tayo masu na aya yanda take nuna kulawarka kan ci gaban makarantar sosai yake faranta masu rai..a hankali ya shigo class din yana samun waje ya zauna suka fara karatunsu kamar yanda suka saba bayan sun gama komai ya tashi ya tafi office dan yana da wani aiki shiyasa yau ko wa'azin da ya saba yi masu kullum baiyi masu ba, yana fita Malika taga ya manta wayarshi salati tayi tana cewa."Laaa Malan Usman ya manta wayarsa."Zainab dake gefenta tana karatu tace."Ikuwa to ki auka ki kai mashi nasan bai wuce office din shi."Girgiza kai tayi tana cewa."A'a."Cike da mamaki Zainab take cewa."A'a kuma?To maiye a ciki dan kin kai mashi wayarshi da ya manta?."Numfasawa Malika tayi tana cewa."Sai dai mu tafi tare hakan kamar zaifi kin san ba dacewa ace naje mashi office kin san ba'a son ka aicewa tsakanin mace da namiji ko a musulunci.'kama baki Zainab tayi tana cewa."Ikon Allah kedai Malika ustaziyace ta karshe wallahi komai dai abi yanda musulunci yace mijinki yaji dadi zaiyi dacen mace ta gari gaki da kyau ga kuma ilimi riba biyu."murmushi mai sauti Malika tayi tana cewa."Zainab kenan ai kyau bashi bane a zaman aure inda kina da kyau baki da ilimi ai kyaun naki