← Book details Zabin Iyaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 143 OF 145

Sashe 143

Zabin Iyaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Tunda yaje Office ya kasa yin komai shi dai gashi nan dan tun randa Usman yace mashi ya saki Umaima ya kasa cire Umaima a ranshi ko zama yayi sai ta fado mashi a rai yanzu abu yayi nisa har mafarkin Umaima yake zaune yake Umaima ce take mashi yawo a zuciya wani irin tausayin yarinyar yake gashi kuma yanda zuciyarsa take addabarsa da son ganin Umaima har abun ya fara bashi tsoro maike faruwa da shi ne? tambayar da yake ma kanshi kenan dan ya rasa gane kanshi yana lissafi sati
aya kenan zuwa na biyu rabuwar auren Umaima da Usman tun daga lokacin a kullum cikin tunanin Umaima yake gashi ko Usman da yayi sakin bai damu ba rayuwarsa kawai yake cikin jindadi kamar ma bai aikata komai ba haka zaizo susha firarsu ko maganar Umaima baya yi mashi kuma fuskarsa babu alamun damuwa amma shi ba da aikata abu ba amma abu yazo ya haye mashi watarana ma kasa bacci yake saboda Umaima sai dai ya tashi yai ta sallah Firzar da naunauyen numfashi Hamad yayi yana kallon Usman da shigowarshi office din kenan yana cewa."Lafiyar ka dai ko?ina ta sallama shiru."Lumshe ido yayi yana girgiza mashi kai yana cewa."Lafiya lau bacci ne nike ji dan duk daren jiya idan har nace maka nayi bacci to karya nayi maka."Shiru Usman yayi yana kallon Hamad sai kuma ya ajiye mashi file din da yazo kawo mashi yana cewa."Kana da abinda ke damunka Hamad kuma babu boyeboye a tsakaninmu kasan bani boye maka duk wata matsalata daman ina ankare da kai kwana biyun nan kamar wani marar lafiya ayi maka magana kayi shiru sai an taboka kace kai bama kaji ba bayan kuma ba haka kake yi ba Hamad maike damunka gaya man kodai na tashi daga matsayin da nasan ni a wajenka ban sani ba?."Bu
e file din da ya kawo mashi yayi yana rufewa ya kalle shi yace."Har abada matsayinka na nan Usman dan ka tashi daga aboki amini kallon dan'uwa nike maka kamar yanda nike kallon Raihan da muke jini
aya."gyara zamanshi Usman yayi yana cewa."To idan har haka ne Hamad maiyasa kake zaune cikin damuwa amma baka gaya man ba?bayan ni da naji abu yana damuna gunka nike zuwa dan nemo mafita ko Sadiq da muke yan'uwa ban gaya mawa."Kallonshi Hamad yayi sai kuma ya murmusa yana cewa."Nima ban san dalili ba Usman amma tun randa ka saki Umaima ban sake natsuwa ba,kullum da tunanin Umaima nike kwana nike tashi yanzu abun yayi nisan da ban iya bacci saboda ita sai naji zuciyata tana man zafin tana harbawa tana son ganin Umaima kai Usman Allah yaso ina da picture dinta da su Raihana tun suna secondary shi nike daukowa na kalla da na kalla sai kuma naji sanyi na shigata yanzu har lamination na picture din nasa anyi ma na ajiye a beside drowa sai na kashe dare ina kallon picture din daman ina samu na tashi nayi sallah dan rage tsawon daren wallahi ina cikin tashin hankali ban san make faruwa ba Usman amma bai wuce tausayinta da nike ne."
Shiru Usman yayi yana kallon Hamad sai kuma ya kalli Hamad yana cewa."Hamad."Kallonshi Hamad yayi yana ansawa kawai, murmushi Usman yayi yana cewa."Hamad son Umaima kake."Wata zabura Hamad yayi yana kallon Usman yana nuna kanshi yana girgiza kai yana cewa."So Usman?a'a gaskiya ba dai so ba tausayinta kawai nike yi amma ya za'ayi naso matar da ka ta
a aure Usman?bayan nida kai mun tashi daga abota mun zama yan'uwa jini
aya."Jinjina kai Usman yayi yana cewa."Camdown Hamad babu laifi dan kaso Umaima ai ba harumin bane babu igiyar aurena a kanta kuma ni ba zan ta
a maida Umaima ba balle dan haka ka natsu ka gane maiye so wallahi sonta kake duba da yanda kayi man statement dinta kai kuma baka ta
a soyayya ba balle har ka gane sai dai abinda zan gaya maka
aya ne Umaima tana bin mata idan har kaji kana sonta a haka zaka iya zuwa kayi mata tayin soyayarka idan har an dace zanyi farinciki zan yi maku fatan zaman lafiya ita kuma Allah ya shiryeta."Firzar da naunauyen numfashi Hamad yayi yana."Ni kuma ban yarda da Umaima tana neman mata ba Usman kamar yanda na gaya maka tun farko, sannan batun so ba zan yi gardama ba dan koda ban son Umaima zan iya aurenta a ko wace irin rayuwa take na zauna da ita na rayu da ita har abada Usman."
age kafadarshi Usman yayi yana cewa.'Fine hakan yayi Hamad tunda kaji zaka iya balle ma sonta kake da kaunarta zan maku fatan alheri ku cigaba da neman za
in Allah idan har akwai alkhari a tsakaninku Allah ya tabbatar."Murmushi Hamad ya saki dan sai da Usman yace mashi son Umaima yake ya ida yarda da abinda yake ji kan umaima zallar soyayya ce ba tausayi ba kuma yana jin zai iya rayuwa da Umaima koda dagaske tana yin lesbian din balle shi har ga Allah zuciyarshi taki amincewa da haka sake sakin wani murmushin yayi yana cewa."To kai ka hakura da soyayyar da kake ma Umaima ne Usman?kasan nasan komai nasan kana son Umaima."Gya
a kai Usman yayi yana cewa."Tun randa na tadda Umaima na nemab Malika na cire ta a zuciyata Hamad na cire ta har abada dan ba zan ta
a iya zama da ita ba kai kasan yanda na tsani masu hali irin na Umaima a rayuwata."Jinjna kai Hamad yayi yana cewa."Haka ne fa to ni ina son Umaima kayi man jagora wajen fallasa mata sirin dake raina."Tashi Usman yayi yana cewa."Wannan kuma bada ni ba dan ba zan rakaka neman soyayyar Umaima ba Hamad ba dan komai ba sai dan ban san ko jin muryata amma zan maku addu'ar Allah ya tabbatar da alheri ita kuma ya shiryeta."Tashi Hamad yayi zai yi magana Usman ya dakatar dashi yana cewa."Dan Allah Hamad karkace zaka matsa man dole."shiru Hamad yayi sai kuma yace."Shikenan Usman na fahimceka Allah ya tabbatar mana da alkharin kamar yanda kace."Amin Usman yace yana fita daga office din bai san maiyasa ba sai yaji zuciyarsa tayi masa ba dadi har ya danji haushin Hamad dama ya nemi saka shi a maganar furzar da naunauyen numfashi yayi yana ganin cewa to shi ina ruwansa haushin mai zaiji dan Hamad yana son Umaima shi tausayi ma Hamad ya bashi da duk matan duniya ya rasa wa zai so ya aura ta zama uwar
ansa sai Yar'iska yar-kwalta yarshayeshaye fasi
a kamar Umaima ai abun aji tausayinsa ne kuma ajiye masa jaje ace Allah ya kyauta gaba amma idan har alkhari ne Allah ya tabbatar ya kuma shiryeta..ji yayi zaman office din ma ya fice mashi a rai dan
ara
aimi zuciyarsa tayi akan Umaima dan yana jin ba zai bari dare yayi ba har a kwana ba tare da yaje ya fallasa sirrin dake ranshi akan Umaima da haka ya adana komai yana fita dan komawa gida ya sake wanka so yake ya dauki gayu na musamman da zai karanta ran Umaima.
Chapter 143 · 0% Book details