← Book details Zabin Iyaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 145

Sashe 31

Zabin Iyaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

She will never truly carry the title of my wife she
s just someone who lacked lovers and was forced on me." Da karfin Hamad ya taka burki yana cewa."What are you doing that Raihan?wannan ai wula
anci ne da cin zarafi ya kake waya da budurwa a gaban matarka ta aure har kake fadi darting talk irin haka a kanta."Kallon Hamad yayi bai dai ce komai ba ya cigaba da wayarshi anshe wayar Hamad yayi yana danneta yana cewa."komin zafi ka ringa tunawa da Raihana yar'uwarka ce duk lalacewarta Raihan tafi
arfin cin zarafi da wula
anci a wajenka."Bani wayata Hamad."abinda Raihan kawai yace kenan ba tare da yace ma Hamad komai ba, numfashi Hamad yayi zai yi magana Raihana ta dakatar dashi tana sakin murmushi tace."Dan Allah Yaya Hamad ka bashi wayarshi karka damu indai nice karkaji komai ai watarana sai labari banji komai ba kuma ban damu ba dan yana waya da buudrwarshi yanda yake jin bai sona haka nima bani sonshi amma ni zan zauna dashi a ko wane hali saboda na faranta ma iyayena amma so dai kam bani sonshi ba zan taba sonshi ba dan ni shi ba kalar type din da nike so bane a ko a cikin maz... rintse idonta tayi tana jiran saukar marin da taga ya daga hannu zai yi mata,Hamad ne ya ri
e mashi hannu yana cewa."Akan mai zaka mareta tana da ra'ayin da zata fadi abinda ke ranta kamar yanda kaima ka gaya ma budurwarka naka ra'ayin ko?."fisge hannushi yayi yana fita daga cikin motar cikin
acin rai ya nufi wata mota da yake sun iso bakin hall din taku biyu yayi KK ya ri
e mashi hannu yana cewa."Be smile please."dafe kanshi yayi yana cewa."KK."
aya mashi kai yayi yana cewa.'Ku kawai ake jira let go please ga amarya nan ta fito fa." Shiru kawai yayi har yana yin gaba kamo hannunshi Hamad yayi yana ha
awa da na Raihana zasu janye ya
ara ha
awa yana cewa."Yau ka
ai ko dan farincikin Ammie." Daga haka suka cigaba da tafiya dan shiga hall din.

Share pls
IN IYAYE*
_Parental choice_
*NA*
*JAMEEY*
*BOOK ONE*
_Bissimillahir Rahamanir rahim_
https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ?mode=ac_c
They walk together calmly and proudly,haka suke tafiyar dan ba mai cewa wa'annan ba masoya bane ba zaka ta
a fahimtar auren ha
i bane kuma auren ma dukansu ba so suke ba,dan kuwa ko wane fuskarshi a sake take sai dai ko wanannsu da abinda ke cikin zuciyarsa,shi Raihan ya saki fuska ne saboda Ammie dan irin kallon da yaga tayi mashi yasa ya dawo cikin hankalinsa yasan halin Ammie ba komai bane a wajenta tace zata yi mashi fa
a a wanann taron mutane nan da suka ha
a,ita kuwa Raihana fuskar dai a sake take tana kokarin ganin ta danne damuwarta dan tasan mudun ta nuna damuwa akan fuskatarta to farincikin da take gani akan fuskar iyayenta zai koma damuwa ne bayan kuma ko auren ta yarda dashi ne dan farincikin iyayenta, duk da daga Raihana har Raihan kusan halinsu
aya basu san taron mutane ko ka
an dan ita Raihana duk inda mutum ya wuce 30 to zata fara jin tsoro ne dan gani take ita kamar ta fasa ihu haka taji tsorone yake kamata fal ranta gani take kamar za'a duketa,ko a yanzun ba abinda jikinta yake sai rawa ga tsoron mutune ga kuma tashin hankalin wani irin zama zatayi da Raihan ya zasu fuskanci rayuwar tasan waye Raihan kuma tasan irin tsanar da yake mata, da
yal ta samu ta zauna tana maida numfashi tana dafe kanta da yake mata ciwo kamar zata cire haka take ji,ga Mc da take surutu tana wasasu tana fa
in dacewarsu tun da suka shigo ba ma a wani tsaya
ata lokaci ba aka fara gabatar da program sosai abun yayi kyau ya kuma attracted duba da yanda ake biography din couple aka zo aka yanka cake duk da a wajen yanka cake din Raihana tasha kallon banza da tsaki a wajen Raihan dan koda tazo bashi kin ansa yayi sai bata damu ba daman tasan ba amsa zai yi ba dan karda taki badawa ne Ammie taji babu dadi cewa yayi daman shi baya cin cake a haka aka barshi suka koma suka zauna anci ansha duk da ita kasa cin komai tayi dan cikinta ma a tunkushe yake rabonta da cin abinci har ta manta sai dai tea kawai take sha abinda yake iya wuce mata kenan, saboda koda ta fara cin abinci da auren ya fado mata a rai take ajiye spoon ta buga tagumi, ko yanzun duk abinda akaci bata saka shi a baki ba koda ruwa bata sha ba tana dai kallo ana ci ita bata da natsuwar ma zata har zata iya cin wani abu,taro yayi taro anci ansha angode Allah dan ba'a tashi dinner ba sai after 11 zuwa 12 sannan aka tashi Momy Ramlah da kanta ta ha
a hannun Raihan da Raihana suna tafiya tana masu nasiha cikin natsuwa da dubara da kuma wasa a haka har ta saka su a cikin motar da za'a tafi dasu tayi masu sai da safe ta wuce tata motar dan kuwa ance ba wanda zai kuma rakata ta tafi da mijinta.

Koda suka shiga motar makurewa gefe kawai Raihana tayi dan agajiye take iyakar gajiya ga headache ga kuma zulullumi duk sun mata yawa lumshe ido kawai tayi tana tunanin mafita a rayuwarta ta tabbata dai aurenta da Yaya Raihan har sun zama mata da miji duk ita har a zuciyarta bata
aukarshi miji dan bai cancanci ta yi mashi wannan kallon ba,zata zauna dashi a matsayin Yayanta wanda zatayi ma biyayyar da kanwa take ma Yayanta amma bata jin zata iya yi mashi kallon mutumin da zai ja ragamar rayuwarta bata son Yaya Raihan kuma bata son ko zama kusa da shi amma ya zatayi da qaddararta? dole tabita a yanda tazo mata sauke numfashi take a ajere-ajere..wani eatry Hamad ya tsaya ya ansar masu fruit da kaza sannan suka wuce estate din su koda suka isa a hankali Hamad ya daina remote din da Momy Ramlah ta bashi na gidan get din bu
ewa yayi ya shiga babban wani compound ne ba abinda ke yawa a compound din
awisu da jimina sai shawagi suke ga wani abu da yake a tsakiya yana aman ruwa da fitilu masu walwal kara gaba yayi ya nufi wani get din yana shiga ya samu waje yayi parking yana cewa."To." Abinda yace kenan dan bai yarda yayi wata magana mai tsawo ba dan kowanensu dagashi har Raihan din babu annuri ko kadan a saman a fuskarsu kowa ya kama kan shi ne da yake daman ita Raihana ta kosa a iso ko ta goge kwaliyar da ke a saman fuskarta ta samu ta kwanta dan a gajiye take sosai har ta nufi hanyar shiga Hamad ya dakatar da ita ya bata fruit din da ya sawo da kaza dan daman shi ita ya sayar mawa ba Raihan ba ansa tayi tana mashi godiya ta wuce ta barsu tsaye kallon Raihan yayi yana cewa."Haba Raihan wannan rana ce fa ta farinciki a gareka amma duba yanda kake ta cin magani wannan ba dacewa bane mahaifa sun wuce wasa ka tuna iyayenka ne suka yi maka za
i da kuma suka tashi yi maka za
in sai suka za
a maka mace har mace kamar Raihana ga kyau ga natsuwa ga kuma ilimi kai ka godema Allah da ka samu kamilar mace kamar Raihana shi Usman yayi ihu mana da aka
aura mashi Umaima."Kallonshi Raihan yayi cike da mamaki Umaima Yusuf Usman ya aura KK ya gaya mashi yasa wasane kawai yake mashi
aga kai Hamad yayi yana cewa."Kwarai kuwa Umaima jiya akayi auren kuma tana gidanshi iyaye suka ha
a dan haka kayi hakuri nidai abinda zan gaya maka kenan ka anshi auren nan kuyi rayuwarku cikin farinciki da soyayya da kauna."Girgiza kai yayi yana cewa."Ba zan ta
a rayuwar soyayya da kauna ba da Raihana ba zan ta
a yiwa ba dan tun fil-azam bani son yarinyar batayi man ba kuma ba zata ta
a yi man ba,Hamad ina son ka sani cewa ni Raihan Umar Fatah nahiyata nafi karfin
Raihana ni ba mate din aurenta bane kuma ba zan ta
a yi mata kallon mata ba,zan zauna da ita amma ka sani su Abbie mai aiki da girki suka kawo ma Daulah a gidan nan amma ba dai matar Raihan ba banda mata da wuce Daulah ita nike so kuma dole a ba zuciya abinda take so."Murmushi Hamad yayi yana girgiza kai yana cewa."Raihan kenan ba baki zan maka ba amma nan gaba zaka yi kukan nadama,mundun ka biye ma bakar zuciyarka ka wula
anta yar'uwarka akan wata can bare watan ma Daulah mai akayi akayi wata Daulah da har kake i
irarin cewa ba zaka ta
a yi ma Raihana kallon mace ba,bayan ta ko ina Raihana tafi wanda kake kumfar baki a kanta."Ta
e baki yayi yana yin gaba ba tare da ya sake cema Hamad komai ba shi dai Hamad da kallon ya bashi yana mamakin abokan nashi daga Usman din har Raihan din shi dai yana jin idan har iyayenshi suka ce mashi ga mata zai hakura ya ansa kuma ya kula da za
in iyayenshi to su maiyasa ba za suyi haka ba?koda yake ai kowa da irin tashi zuciyar abinda yace kenan ya shiga mota dan tafiya gida ya kwanta.
Chapter 31 · 0% Book details