← Book details Zabin Iyaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 145

Sashe 70

Zabin Iyaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

"Haulat tun dazun ke nike zaman Jira Ina cikin tashin hankali tunda kika gaya man wacece Raihana sai naga kamar har sun gama tsafinsu zasu fiddani a wannan rayuwa mai dadi ya kukayi da yankar wuk'ar har ya aikata duniyar ko?."Murmushi Haulat ta sakar tana cewa."Nazo kin san nasha doguwar tafiya ba kika kawo man ruwa ba kin hauni da tanbayoyi Daulah."dafe kai Daulah tayi tana nufar freeze ta dauko bottle din ruwa tana bude mata tana cewa."Ba zaki gane bane Haulat ni nasan a tashin hankalin da nike dakyal nayi bacci jiya fa daman na hada ma shegiya kulli a jiyan ya sake cin ubanta nasan zan rage tashin hankalin da nike ciki amma Ina baki ga tun asuba na kiraki ba?ai room dina na gudo da ya yafi sallah fa."Ansar ruwan Haulat tayi tana sha sai da tasha mai yawa tana maida numfashi dan zuwa wajen yankar wuk'a sai mai dakiya dan ko da warin da da'kinshi yake aka barka ka bani Allah yasota har ta fito bai nemi kwanciya da ita ba shine saukin da samu dan batayi tunanin ba zai bukaceta ba dan da wuya kaje wajen yankar wuk'a ya barka ka taho bai sakar maka gajiya ba dafata Daulah tayi tana cewa."Haulat kodai ba'a dace ba?na shiga ukku ba lalace ni Daulah shikenan tawa tazo karshe.'ajiye jarkar ruwan Haulat tayi tana dafo Daulah tana cewa."Har kin manta waye yankar wuk'a Daulah?kin manta da ba bukatar da ta gagari yankar wuk'a sai dai ba'a gaya mashi ita ba Daulah?shifa Yankar wuk'a shike raba dodon tsafin karshe ma."sauke naunauyen numfashi Daulah tayi tana jin sanyi da natsuwa na ratsa mata zuciya,tashi tayi da sauri tana cewa."Bari naje naga irin fitar da shegiyar zatayi dan yau bata kwanar man gida."Rikota Haulat tayi tana cewa."Tsaya kiji Yankar wuk'a yace ba take zata tafi ba duba da ashe itama kanta tana tsafi babbar yar'tsafi ce duba da jininta ma su gadon tsafi sukayi dan da ace bamu je da wuri ba da yanzun wata magana ake ba wannan ba duba da tsafi ta dauko ba na wasa ba gab take da shiga cikin zuciyar Raihan Allah dai ya rufa asiri munje wajen Yankar wuk'a Kuma idan har ta shiga bata fita kuma ba wanda zata sake shiga a cikin zuciyarshi mudun ta shiga kowa ke ciki sai ta fiddoshi dan bata zama da kishiya."Zaro idanu waje Daulah tana yin baya zata fadi da sauri Haulat ta riko ta tana mai cigaba da cewa."Haba Daulah karki sama kanki damu Kuma ai Yankar wuk'a ya lalata aikin da ta fara yi dan ya kara dasama Raihan tsanarta dan haka yace a hankali zata bar gidan kuma yace ba zasu ta'ba yin nasara akan ki ba."hawayen da suka fara zubo mata tasa hannu ta share tana sauke ajiyar zuciya mai karfi lokaci guda tana kallon Haulat tana cewa."Wallahi ba tsafi ba ko bishiyar tsafi ce a kanta sai ta bar gidan nan dan haka nima zan cigaba da angizashi yana cin ubanta kafin tabar gidan nan dan na tsani shegiya ba zan taba sonta ba har abada dangin tsafi."
ara
aurata akan yanda zata gallazama Raihana Haulat tayi sannan ta tashi tayi tafiyarta akan komai kenan zasuyi waya.
*Bayan kwana biyu*
Tunda Raihan ya saka Raihana up and down Raihana bata sake ganin Raihan ba shima haka bai sake ganinta ba dan ta kulle duk wata hanya
da zasu ha
u ganinshi ma bata san gani ko maganarshi bata son ji,shiyasa da ta tashi tayi sallah take yin breakfast ta gyara ko ina ta koma ciki bata sake fitowa sai kuma idan zatayi lunch shima har ta gama ba zata yarda ta ha
u dashi ko Daulah din ba haka suka koma yin rayuwa a gidan...yau da ciwon kai ta tashi dan da
yal ma take ganin gabanta sai ta dafe kanta take iya bu
e idonta kuma ko motsi mai karfi bata son ji haske ma bata son gani sosai lokaci ta duba taga har 1:00pm tayi da dafa bango ta samu ta shiga toilet tayo alwallah ta samu ta gama sallah da
yal bajewa tayi
asa tana maida numfashi tana lumshe idonta ta dafe kanta da take jin kamar ya tsage ko a cire mata kan ta huta da zugin da yake mata,ganin har 1:30 ta kusa yasa ta samu ta tashi dan zuwa yi masu lunch dan bata son abinda zai ha
ata da Raihan shiyasa take kiyaye duk wani abu da zai ha
ata dashi shiyasa ta daure dan zuwa yin lunch din dan tasan yanzu haka yana hanyar zuwa gida yin lunch ya koma dan shi baya wasa da abinci kuma baya cin abincin waje a rayuwarsa shiyasa duk inda yake da lokacin cin abincinshi yayi yake zuwa yaci ya koma haka yake ji bata san ma damuwa a yau daman tana fama da ciwon kai tasan ba
aga mata
afa zaiyi ba,a hankali ta tashi da
yal tana nufar hanyar fita luuuu ta tafi zata fa
a tangal tangal da
yal ta dafe Sofa tana zama sama tana mai lumshe ido kawai tana kwantawa dan bata iya ko yin tafiya jiri ke daukarta sosai hawaye ne suke zubar mata kwance kawai take...cikin sauri ya kalli Kk yana cewa."A'a Kk sai naje nayi lunch sannan zan zauna dasu gaskiya."girgiza kai Kk yayi yana cewa."Haba Raihan tun yaushe mutune nan suke son zama dakai kaga ba dadi sai suga kamar wula
anci ko?"ta
e baki yayi yana shafa cikinshi yana cewa."Kasan idan har lokacin cin abincina yayi ba gane komai kenan ba idan har banci ba,to suma dan Allah daukar man excuse wajensu akan zanyi sallah zan kuma yi lunch zan zauna dasu 3pm zuwa 4 mun tashi kaga sai nafi saurararsu dakyau."Tashi Kk yayi yana cewa."Raihan ci kai dai kaci kuma ba wani cin kake da yawa ba sai zafin dai za'a cin kuma ba'a ci sosai gaskiya su Raihana na ko
ari Allah ya basu ladar."Harararshi yayi yana cewa."Kai dai ka sani."tare suka fito daga Office din Raihan,Kk ne yace."Kasan kuwa Rilwan yana kasar nan ashe shine baiyi attending din bikinka ba daga na Raihana har na Daulah jiya naje Katsina wajen Dad na taddashi a Office din Dad."Kallon Kk Raihan yayi dakatawa yayi sai kuma ya furzar da iskan bakinshi yana cewa."Rulwan Umar Y Umar ne zaiki attending bikina to why?."Idnt now but surely next week zai bar kasar ma again."Gya
a kai yayi kawai yana shigewarshi mota dan nufar gida dan shi yau wata irin yunwa yake ji kamar wanda ya wuni bai ci komai ba dan har biyubiyu yake gani Allah yaso bashi yake driving din ba da ya buga ma wani mota lumshe ido kawai yayi yana jin kamar yayi flying ya ganshi a gida yana cin abinci kawai yanda yake jin yunwar nan kamar wanda aka yi ma sata a ciki, sauke naunauyen numfashi yayi dan bai jira driver ya bu
e mashi mota ba ya bu
e da kanshi ya nufi cikin gida cikin sauri har yana ha
a hanya haka ya shigo cikin parlon dinning ya nufa cikin saurinshi ya zauna yana kallon flask din da suke jere a saman dinning din plate ya janyo yana bu
e flask din take ya
ata fuska yana sake bu
ayan shima dai ba komai cikinshi da alamu tun flask din da aka zuba break ne ciki ba'a kwashe ba,take ranshi ya
aci yana mai nufar kitchen yaga maiyasa ba'a gama lunch ba har biyu ta kusa yana shiga kitchen din yaga wayam babu kowa a ciki kuma babu alamun ma an
aura girki ranshi ne ya
aci yana hango girman rainin hankalin da Raihana tayi mashi a yau a sauri ya nufi room dinta ranshi
ace fuskarsa a murtuke.
Chapter 70 · 0% Book details