← Book details Zabin Iyaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 145

Sashe 69

Zabin Iyaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su Baba sun kai ku
in auren Usman da Malika Naira miliyan daya tarba suka samu a wajen iyayen Malika ta girma da arziki anyi masu karanci sai da suka ci abinci suka sha ruwa sannan Alhaji Mudi ya fara magana yana cewa."Alhmdulillahi Allahunma barik godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai da ya bamu rai da lafiya ya kuma nuna mana wannan rana mai albarka rana ce da muka da
e nuna bige da addu'ar Allah ya nuna mana ita da rai da lafiya na auren yarinyar mu Malika."dan shiru yayi yana sauke numfashi yana cigaba da cewa."Allahu Akbar Allah ya jikan Umaru ya gafarta mashi mu kuma muna
ara godema Allah da ya nuna mana ranar da zamu anshi ku
in marainiyar Allah dan Allah muyi ma Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama salati."Salati sukayi, karanta fala
i da nasi sukayi addu'a suka shafa da neman Allah ya sama auren da suke kokarin daurawa zama lafiya da kwanciyar hankali duk wata fitina Allah ya kaudata koda su Baba suka bada million
aya amma sai Alhaji Mudi ya girgiza kai yana cewa."A'a haba wannan kudin sunyi yawa dubu
ari biyu zamu amsa sai kuma sadakin ta dubu
ari biyu shima dan kun san mafi
arancin sadaki yafi albarka mu kuma albarkar auren muke fata ba wai kashin ku
in ba,amma Millon
aya a gaisuwa ka
ai ai tayi yawa Alhaji kuyi hakuri."Murmushi Abba yayi yana girgiza kai yana cewa."Haka ne albarkar ake nema sama da komai amma duk da haka ayi hankuri a anshi ku
in nan kuma in shaa Allah addu'ar da muke kenan Allah ya tabbatar da albarka ta har abada auren ya basu zaman lafiya ya ha
a kawunansu da abokiyar zamanta kuma batun sadaki muna neman alfarmar mu bada dubu
ari biyar amma biyu tayi ka
an a sadakin mace mai natsuwa da ilimin addini kamar Malika tayi ka
an kuma dai albarkar muke nema dai."Shiru sukayi zasu yi magana Baba yayi saurin dakatar dasu yana cewa."Ayi hakuri dai a kuma anshi hakan Alhaji Mudi."Gya
a kai Alhaji Mudi yayi yana cewa."Allah yayi albarka ya kauda duk wata fitina sannan kuma nan da sati
aya wato rana irin ta yau sai a
aura auren a isilamiyarsu in shaa Allah sannan kuma mun yafe lefe mu bamu ansar lefe amma bamu hana ango yi mata kala
aya zuwa biyu da zata saka tayi fitar biki ba sai kuma magana ta gaba bamu yin kayan
aki yanda Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya gaya mana ita
aya zamu
auka mu kai mashi kunsan a addinance miji zaiyi kayan
aki da komai to mu muna kwatanta sunar Manzo Allah Sallallahu alaihi Wasallama muna kuma guje ma al'ada,dan kuwa yin kayan
aki da iyayen amarya suka dauka suka
aura ma kansu al'ada ce kuma yin lefe ma al'ada ce ba haka muka gani a littattafai ba."sosai suka yi na'am da duk bukatunsu suka sake musabaha sannan suka taho zukatansu cike fal da farinciki tabbas Usman yaje gidan mutunci gidan arziki neman aure dan suna da ya
inin yanda iyayen Malika suke da dattako tabbas Malika ma haka take daman damuwarsu karda ya kwaso masu marar hankali da natsuwa to Alhmdulh ya samo mai ilmi da zata kama mashi wajen
ara
aura masu Umaima turbar da ya dace zukatansu tas suka dawo gida kuma suka tara su Dada suka gaya masu irin abinda akayi masu na arziki a gidan Yayan mahaifin Malika tabbas Usman yaje gidan mutunci sosai suka ji dadi dan su duka hankalinsu ya
ara kwantawa natsuwa ta samaisu sai suka ji son yarinyar ya shiga zuciyarsu.

Murmushi Haulat tayi tana daukar wayar tana cewa."Kawata ta kaina." Daga can
angaren Daulah take cewa."Kawata nace kin tafi ko?."Murmushi mai sauti Haulat tayi tana cewa."Kawata kwantar da hankalinki da ke na kwana a raina duka yanzu karfe bakwai breakfast kawai zanyi na tafi dan wallahi yau din nan zaki ga aiki ai yanda kika saki bakin aljihu haka ai dole boka shima yayi aiki yanda ya dace Kawata kwantar."Sauke nunfashi Daulah tayi tana cewa."Taya zan kwantar da hankali na Haulat?ai idan har kika ga hankalina ya kwanta to shegiyar yarinyar nan ta bar gidan nan tabi duniya shine kawai fatana dan wallahi na gaji da ganinta gidana."Tea Haulat tasha tana cewa."Karki damu yanzu zan tafi ai nima ban san ganinta a cikin gidanki dan idan har mukayi sanya ita zata fitar dake dan na tabbata shirunta ba na banza bane ana can ana maki surkule."Sosai Daulah ta
ara maimaita ma Haulat aikin da take so ayi mata akan Raihana da Raihan idan ku
in sunyi ka
an a shirye take da ta
ara turo wasu ita dai bukatarta ta biya daga haka suka kashe wayar ida yin breakfast Haulat tayi tana fita daman zaman kanta take bata da wanda zata tambaya fita duk sanda ta isa fita take ta dawo sanda ta gadama..tafiya tayi mai dan nisa sannan ta iso wani dan
aramin kauye samun waje tayi tana parking din motarta sannan ta fito ta nufi wani gida babban gidane mai dauke da dakuna zasu kai goma koma fiye da haka kuma ko wani da'ki akwai mata a ciki ga dukan alamu matan bokan ne,Wani da'ki Haulat ta shiga ba abinda ke tashi a cikin da'kin sai wani irin mu gun wari kamar mutun yayi amai dan warin shi ba na kashi ba Kuma ba na tusa ba kamar dai wani abu ya mutu har ya rube yayi tsutsa haka warin dai yake fita kuma baka da ikon dod'e hanci haka zaka shek'i wannan bala'in ya kune fuska Haulat tayi tana cewa."Yanka wuka mai share hawayenmu maganin kukanmu mai biya mana bukatar."Wata uwar dariya Yankan wuka yayi har yana wutsilewa k'asa yana cewa."Shegiyata kenan abokiyar shiga wuta ai Ina sane da zuwanki daman nasan zata turoki dan zama da jinin tsafi sai matsafi ke ko matsafin ma sai ya shirya ya tashi tsayin daka dan Daulah bata iya karawa da jinin Okeke."
Tagumi Haulat ta buga sai kuma ta furzar da numfashi mai zafi Haulat tayi tana cewa."Wayyo mun shiga ukku daman ni nayi bincike kan yarinyar nagano gabanta da bayanta tsafane su nasan ba zasu bar Daulah ta zauna taci arziki ba wayyo wayyo zamu na cikin masifa, Yanka wuk'a kaine uwarmu kaine ubanmu kaine Mai share mana hawayenmu kana biyama duk bukatunmu kuma kasan Daulah ta gidanka ce tana maka duk abinda kake so a wajenta to a sake share mata hawayenta a karo na ba adadi Yankan wuka."Hura wani faskeken hanci yake yana zari kananunshi idonshi kamar ballin gyad'a yana cewa."Ba dai kuna tare dani ba za'a share maku hawayenku ba jinin tsafi bane jikinta ko dodon tsafin ne a jikinta ni yankar wuk'a basu fi karfina ba dan haka kasheta kike son ayi kafin ki isa ki tadda ana zaman makoki ko kuwa a haukatata ta haukace haukan da babu inda za'a samu maganin shi sai a wajena kawai ko kuwa na harbata ta bi duniya ba zata k'ara waiwayar gida ba har ta mutu wane kuke so ayi maku a ciki?."Gyara zamanta Haulat tayi tana cewa."Ai ba wanda bamu so a ciki yankan wuk'a amma so nike ta fara shakar bakincikin da zai haddasa mata ciwon zuciya daga karshe sai a haukatata ta Kuma bi duniya haka nike so ayi mata."Jinjina Kai Yankan wuka yayi yana wasu surutai tana buga wani abu a gefenshi sai Kuma ya kalleta yana cewa."To har yanzun dai zuciyar Raihan babu Raihana a ciki sai dai ta dan fara neman hanyar shiga a cikin zuciyar tashi idan Kuma har ta shiga bata fidduwa komai za'ayi tana shiga tafa shiga kenan ba mai fiddata kuma zata cire kowa ya zamana ita da'ya ce a ciki babu kishiya."Dafe kirji Haulat tayi tana cewa."Ai kuwa ba zata ta'ba shiga a cikin zuciyar Raihan ba dan babu wani mai waje a cikin zuciyar Raihan sai Daulah ita da'ya zata kasance a cikin zuciyarshi har ya mutu dan haka yankan wuk'a a kara nisantata da zuciyar Raihan a kuma kara dasa masu tsanar juna tsantsar tsana Ina son suji idan har suka ga junansu suji kamar zasu kashe junansu ba ma kamar shi Raihan din yaji baya son ko sunan Raihana yaji so nike a fara da wannan kafin muzo aiki na gaba Yankar wuk'a."Wata uwar dariya Yankan wuka ya sheke da ita yana wasu irin gurnani yana mazure da kananun idanunshi can Kuma ya da'go yana murtuke fuska yana cewa."Raihan ba zai ta'ba son Raihana ba haka itama Raihana ba zata ta'ba son Raihan ba zasu kasance kamar Annabi da kafiri ne an gama wannan."Murmushi Haulat tayi tana mashi godiya akan kokarinshi na share masu hawaye da yake tashi taje mota ta dauko jikkar da ta lissafo kudin da zata bashi naira million goma ne ta ajiye mashi sannan ta tafi dan tasan waye yankar wuk'a idan har yace yayi to yayi kaje kayi bacci zaka ga results amma duk mai zuwa anjima wajen yankar wuk'a baya sallah dokarshi kenan idan kana yi to daga ranar da ka fara zuwa wajen shi Kuma kana bukatarka ta biya to ka daina sallah kenan daga ranar idan har kuwa kayi kuskuren yin sallah Koda tadawa kayi ka tuna ka fasa duk aikin da yayi maka ya wargaze kenan sai ka sha wuya zai ma sake kulaka har yayi maka Wani sabon aikin idan ma bakayi sa'a ba haukace kake baki da'ya shiyasa duk wani mashiriki da yake zuwa wajenshi baya sallah..bayan ta ajiye mashi kudin ta taso ba inda ta sauka sai gidan Daulah zaune ta tadda Daulah ta buga tagumi a cikin da'kin ta dan ma bata ji shigowarta ba sai da ta ta'ba ta sannan ta da'go a firgice ganin Haulat ce yasa ta tashi tana kamota ta zaunar da ita saman sofa din dake bedroom dinta ta rufo kofar tana cewa.
Chapter 69 · 0% Book details