← Book details Zabin Iyaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 145

Sashe 4

Zabin Iyaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Furzar da naunauyen numfashi yayi yana cewa."Sorry Hub please stop crying."daga
angaren Daulah ta share hawayenta da bayan hannu tana cewa."To ba kai bane Hubby you forget me today at all."a shagwabe ta karasa maganar tana turo baki gaba kamar yana gabanta,gyara zama yayi yana girgiza kai yana cewa."kenan zan iya mantawa da kaina idan har ni Raihan Umar Fatah Umar na manta dake Hub? don't forget you are my sunshine my everything Hub stop it saying kinji mieluv?."
aga kai tayi kawai tana cewa."Umm."cikin son saka ta farinciki yace."Wifety smile I love you." Aikuwa murmushin ya subuce mata dan duk yanda Raihan zaiyi mata abu da yace mata Wifety ta huce ko wani irin laifi ne shima fahimta da yayi da haka bai shan wahalar shawo kanta daman shi ba wani iya shawo kan mace yayi ba ko bada hakuri duka yaushe ma ya fara soyayyar sai da ya research suka ha
u da Daulah har suka fara ma soyayyar ma baki
aya,sunyi 10mn suna wayar kuma rabin wayar Daulah ce ke kawo labari shi nashi uhm da uhmuhm bayan sun gama ya ajiye wayar ya kwanta dan ya gaji sosai tunda yazo bai zauna ba shiyasa shi yafi son zama aboard akan naija dan shi Abbie bai son zama waje yafi son ai ta aiki ba'a can ba'a can shi kuma bai iyawa addu'a yayi ya kwanta.

Koda suka koma room din su kallon Rahina tayi tana cewa."Ukkty banji kince man komai ba akan timetable kuma final drop ce ko kina da interble?."kwanciya Rahina tayi yana cewa."Na manta ne ina da interble kefa?."Girgiza kai tayi tana cewa."Babu amma na gama karatu ni already but wanda basu fara karatu ba suna cikin trouble a cikin sati za'a gama duka exams."Jinjina kai Rahina tayi tana cewa."kuma final ba daga shi sai serve im happy wlh."murmushi tayi dan itama tana jindadin haka idan ta tuna final exams zasuyi a University of Abuja da suna ganin yaushe zasu gama gashi har suna shirin final duk sonsu da fita aboard tunda su Abbie suka hana sai suka hakura gashi zasu ci ribar hakuri tunda har sun kusa gamawa baki
aya,kallonta Rahina tayi tana cewa."Ukkty maiyasa baki gaida Broth ba.?"Ta
e baki tayi tana cewa."Time din da na gaisheshi ai kina can kina gulma taya zaki sani Ukkty?"kama baki Rahina tayi tana kallonta sai kuma can ta girgiza kai tana cewa."Mai karya dai dan'wuta kuma ba kyau karya."Tashi tayi tana cewa."Nidai Ukkty mubar mgnr baki
aya Please."hararar wasa tayi mata tana cewa."Ai dole ki
i maganar Ukkty." Daga haka suka sake sabuwar chapter ba bacci suka koma ba karatu sukayi dan next day ma su duka suna da exams.
*Bayan sati
aya*
Zaune Raihan yake shi da Mr president da Salisu da Ubaidu sai Jabir suna magana akan babban asibitin da Mr president Umar Fatah Umar nahiyata yake ginawa a Katsina wanda duk katsina babu kamarta kuma komai na ciki kyauta ne ba abinda ake ana ansar kudi har katin da marar lafiya zai amsa dan bin layin ganin likita a kyauta ne dan ma'aikatan cikin asibitin ma kwararrune ta ko wane fanni dan an gama komai shirin zuwa bu
eta ake shiyasa suka zauna dan tsara komai dan duk yaran Mr president wanda sukayi rayuwa tare dasu a Katsina wato a *DIGA MISSION* duk wanda ya karanci fannin lafiya to a can ma zai koma da aiki banda wanda ya dauko daga kasar waje manyan likitoci suyi agreement da komai zai basu albashi mai tsoka kuma Diga mission aka
ara gyarawa acan zasu zauna a Matsayin estate nasu sosai suke tsara komai cike da natsuwa a haka Raihana ta shigo da sallama a bakinta duka suka amsa banda Raihan da bai nuna yasan da shigowar mutum ba duba files din gabanshi kawai yake kuma fuskarsa ko chanzawa batayi ba duk da kuwa yasan da wacece ta shigo din
asa ta samu ta zauna tana gaishesu murmushi Ubaidu yayi yana cewa."Tashi
asa Daughter koma ki zauna bisa seater."girgiza kai tayi tana cewa."Haka ma yayi Uncle." Dan kallon Abbie tayi tana cewa."Abbie."kallonta yayi yana cewa."Ina jinki yarinyar kirki."murmushi ta saki fuskarta na nuna farinciki dan tana son suna nan tana jindadi idan har Abbienta ya kirata da yarinyar kirki cikin farinciki take cewa."Abbie gobe ne final exam kuma 8 ne zan shiga ga Faisal bai nan shine nazo na tambayeka nayi driving din da kaina ko?tunda Faisal yaje ganin gida."Girgiza kai Abbie yayi yana cewa."Ba yanzun zaki fara driving da kanki ba Raihana kuma ni ba kowa na yarda da yayi driving dinku ba inba shi Faisal din ba,dan haka tunda ga Yayanku nan sai ya kaiki da kanshi kawai." Tun da suka fara bai nuna yasan suna yi ba sai da yaji an saka shi ya
ago kai yana kallon Mr president zaiyi magana ya daga mashi hannu yana cewa."bani bukatar jin komai daga bakinka Raihan gobe zaka kai Raihana school kuma kai zaka daukota da kanka idan har ta kama exams din."maida kanshi
asa yayi yana cewa."Okay Abbie in shaa Allah I'll." Gyada kai yayi yana kallon Raihana yana cewa."Tashi kije ki cigaba da karatunki Yarinyar kirki Allah yayi maku albarka."kwakwaro murmushin dole tayi tana tashi tana cewa.'Okay Abbie Ameen." Ta tashi ta fita ba tare da sun sake maganar ba suka cigaba da maganarsu sai da suka gama Mr president ya kalli su Ubaidu yana cewa."Gobe zamu je Okeke da kai da Jabir da Salisu sai Jibril ku gaya mashi ya baro
akin network din ya dan sha iska."jinjina kai sukayi suna cewa.'To Yaya in shaa Allah a tashi lafiya."
Bayan sun tafi Raihan ya kalli Abbie yana cewa."Amma Abbie nima inason naje Okeke naga Dad tunda na dawo banje ba."Kallonshi Abbie yayi yana cewa."Ai bakayi niyar zuwa ba Raihan sai da zamuje zaka ce zaka je?to tafiyarmu daban taka daban ka bari idan mun dawo kaje idan ka tashi ma karka dawo ai gidanku ne."gya
a kai yayi yana ha
a file bai sake cewa komai ba dan shi ba haka yaso ba yaso Abbie yace ya bisu a goben yanda ba zai kai yarinyar can makaranta ba,bayan ya gama ha
a file din ya ajiye inda ya dace ya
tashi yana cewa.'Gud night Abbie love you."murmushi Mr president yayi yana cewa."Okay Yaron kirki Allah yayi albarka karka manta da kanwarka tayi missing exams please Raihan." Dan kallon Abbie yayi na second sai kuma ya gya
a kai yana fita yana jin zafin yarinyar a zuciyarshi tsaki yayi yana jin kamar ya hau sama ya hau marin yarinyar haka yake ji amma zaiyi maganinta a goben yanda tasa ba zaiyi baccin safe ba to sai ya kunsa mata ba
in cikin da zata kasa ko rubuta exams din gata a exmas hall amma ta gaza komai dan koda ya koma room din shi yana kallon wayarshi na Ring kuma yasan Daulah ce amma bai
auka ba dan yana a tamper bai son ya huce a kanta laifin da ba nata ba a haka ya kwanta cikin
acin rai.

Tunda Raihana ta koma room din su take zagaye zagaye tana share hawaye da bayan hannu dan duka hankalinta tashe yake tsabar tsoro da tasan Abbie sawa zai yi Yaya Raihan ya kaita school gobe da ta kama bakinta tayi bold kawai ankaita cikin mutunci da kwanciyar hankali ba tare da wani yaji ya gani ba,bata fatan wani abu ya ha
ata da Yaya Raihan dan tasan haduwar ba dadi zatayi mata ba dan tasan halin Raihan idan baiyi niyar abu ba
aura hannu tayi a kai tana cewa."Innalillahi wa'innalaihirajiun ni Raihana na bani shikenan lokacin mutuwa yayi wayyo Abbie maiyasa kace ya kaini bayan kasan ba sona yake ba?."shigowar Rahina kenan room din da pancake turus tayi tana kallon Raihana ganin yanda take ta share hawaye da sauri ta ajiye plate a mini-dinning table tana tahowa wajenta tana cewa."Ukkty lafiya dai ko?wa ya mutu?."fa
awa jikin Rahina tayi tana mai sauke ajiyar zuciya da karfi karfi sai kuma ta
ago tana cewa."What time do you have the exam tomorrow?." Dan shiru Rahina tayi tana cewa."I don't have an exam tomorrow." Zaro ido tayi tana cewa."Shikenan na mutu na mutu Ukkty." Cikin tashin hankali Rahina tace."Gayaman mai ya faru a school din?."share hawayen tayi tana cewa."Gobe Yaya Raihan zai kaini school inji Abbie." Ita kanta Rahina sai da ta tsorata dan ja baya tayi dan tasan halin Raihan ko ita aka ce ya kai school da safe tasan sai ya dugurar mata kai balle kuma Raihana da basu zama inuwa
aya cikin son kwantar mata da hankali tace."Don't worry, Ukkty, nothing will happen.

You're crying just because he's taking you to school.

Keep it in mind, nothing will happen to you."Girgiza kai tayi tana cewa."Nidai Ukkuty kizo ki rakani to."Waro ido tayi tana cewa."A'a ku dai tafi zan raka Ammie gidan Momy Ramlah."komai bata sake cewa ba kawai kwanciya tayi dan ita da tabi Yaya Raihan gobe gwanma tayi spill din course din ta gyara next year dan ita duk abinda zai ha
ata da Yaya Raihan bata so ita ko fuskarsa bata son gani dan tunda ya dawo bata kyali fuskarsa ba dan batason kallon fuskar tashi yace tayi mashi laifi yanda laifi bai da wuyar yi a wajenshi ganin baccin ma ya fita idonta ta tashi ta fara karatu duk da tana jin ba laila taje school din ba,ko kuma tayi bolt kawai tayi tafiyarta.
Chapter 4 · 0% Book details