← Book details Zabin Iyaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 130 OF 145

Sashe 130

Zabin Iyaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Share pls
IN IYAYE*
_Parental choice_
*NA*
*JAMEEY*
*BOOK ONE*
_Bissimillahir Rahamanir rahim_
https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ?mode=ac_c
Kallonta dakyau Baba yayi yana cewa."Kakata."Kallonshi tayi tana share hawayenta tana ansawa, furzar da numfashi Baba yayi yana cewa."Maiyasa kike son Yayanku ya sake ki Kakata?gayaman gaskiya idan har kika gaya man gaskiya na kuma yi bincike na gano ke keda gaskiya ba zan barki ki koma ba zan saka ya sawa
a maki kinji Kakata?."Jinjina kai Umaima tayi tana turo baki tana cewa."Ba matarshi bace take cewa wai wai...kasa fadi tayi sai bin su da ido da tayi tana maida kanta
asa Kunya ma ta kamata tana jin nauyin fa
in abinda Malika take nemanta dashi,gyara zama Baba yayi yana cewa."Ba Matarshi ba mai Kakata? bu
e baki ki gaya mana maike faruwa mai matar tashi tayi maki karki boye mana komai mu nan iyayenki ne kinji."Gya
a kai Umaima tayi tana sake fashewa da wani sabon kukan tana gaya masu duk abunda ya faru a tsakaninta da Malika har da damben da sukayi ta yi mata mugun bugu da marukan da Usman yayi mata daga dawowarshi ba tare da yayi bincike a tsakaninsu ba, cigaba da cewa tayi."Wallahi Baba zan iya kashe ta idan har na koma gidan dan na tsaneta sosai."Duk shiru sukayi duka parlon jikinsu ya dauki mugun shock da maganar da Umaima tazo masu ita,Dada ce tayi salati tana cewa."Wannan ai qaddara ce daman yar'iska Usman ya kwaso mana mai bin mata kamar wata mutuniyar arziki tana sunne kai
asa."Girgiza kai Baba yayi yana cewa."A'a Dada ba'a yin saurin yanke hukunci ba daga anji magana daga bakinta dole itama matar a bincike ta har da masu aikin gidan."Maida Kallonshi kan Umaima yayi yana cewa."ke kuma Kakata wallahi ba zan raga maki ba idan har nayi bincike na gano karya kike ma Malika sai na sa
a maki kin dai jini ko?."
aga kai tayi tana share hawaye tana cewa."Eh wallahi Baba na yarda ba zan ta
a yi mata karya ba,bayan nasan yin karya ga dan'uwanka musulmi ba kyau
aukar hakki ne kuma a ranar da ta fara yi man irin maganar har fita nayi zan dawo gida amma ga
teman ya hanani fita wai Yaya Usman bai ce mashi zamu je ko ina ba nace ya ara man wayarshi na kirashi amma wayar taki shiga daga baya ma neman wayar akayi aka rasa kuma nasan ita zata saka a sace wayar tunda tagan ni da wayarshi hannuna."Shiru kawai Baba yayi sai kuma ya kalli Abba yana cewa."Kaji wata kuma sabuwa Yusuf tashi zakayi yanzu mu fara zuwa gidan nashi muyi magana da su masu aikin gidan sai mu wuce asibitin nasan dai suna wajen Sadiq muga ita matar muji daga bakinta."Jinjina kai Abba yayi yana tashi suka tafi da Baba, Furzar da naunauyen numfashi Umma tayi tana cewa."Shiyasa tun farko ban goyi da bayan Usman ya auri yarinyar nan ba dan hankalina bai kwanta da Yarinyar nan kunga abinda ya auro mana."Girgiza kai Momy tayi tana cewa."Ni kuma ban yarda da maganar Umaima ba kawai ta ha
a maganarta dan kawai ta kashe aurenta ne Yaya Zainab."Kama baki Dada tayi tana kallon Momy tana cewa."Sannu to Sumayya nace sannu kinji har yaushe Uwata ta iya wata karya da zatayi ma matar Usman?nasan halin Uwata tun dacen da take gidan nan kafin tayi aure bata yin karya balle kuma yanzu da tasan hukuncin maiyin karya dan haka su gama duk binciken da zasuyi su gama ina nan zaune Usman zai dawo sai ya saki karuwar yarinyar nan ya kwaso nashi ya nashi ya dawo ya zauna da Uwata a gidan nan daman tun farko ni ban so aka ware mai gida ba fin karfina su Yusuf sukayi."Gya
a kai kawai Momy tayi tana cewa."Allah ya rufa asiri to."Da Amin Momy Nafisa ta ansa tana cewa."Amma Malika tayi wayaun banza tayi kyaun banza tayi ilimin banza tunda tana da sani amma take ta
e sani tana barna."Ta
e baki Dada tayi tana cewa."Uhmm!damuwarta ai mungode Allah tunda bata
ata mana tamu ba,taje Allah ya shiryata idan mai shiryuwace idan kuma bata shiryuwa Allah kai kasan yanda zakayi da ita Allah ya tsare na kowa karda ta
atasu."Da Amin suka amsa suka cigaba da tattaunawa ita dai Umaima jinsu take amma ta kudurtama ranta ba zata koma gidan Usman ba sai ya saketa ba ta iyawa dan ko ta koma sake auro mata wata zai yi karda tana zamanta lami lafiya wajen aure-aurenshi ya auro mata mai tsafi tayi sanadin ajalinta bata iyawa ita dai.

Gidan Usman su Baba suka nufa da suka fito daga gida sosai sukayi ma masu aikin gidan tamboyi sun sheda masu tun randa Usman yayi tafiya suka fahimci gidan ba lafiya dan suna jigo zagezage na fa
a har dai yau da ta kai ga dambe..maigadin ya gaya masu tabbas Umaima tazo fita ya hanata kuma ta ari waya sun kira Usman wayarshi bata shiga a yanda tazo daman ya fahimci babu lafiya yaso ya kira Usman din daga baya ya tadda babu wayar an dau
eta,da bincike yayi bincike wani maiba flowers ruwa yace shi Malika tasa ya dauke wayar mai gadi tace idan har bai dauke wayar ba sai ta koreshi daga gidan shi kuma bai son rasa aikinshi shiyasa ya dauke wayar ya bata tana wajenta, sun dade a gidan kafin su tafi asibiti zuciyarsu cike da mamakin abinda ke shirin faruwa....koda suka iso asibitin tarbarsu Sadiq yayi fitowarshi kenan daga theatre room ya ha
u da su Baba har
asa ya du
a yana gaishesu ansawa sukayi suna isa office dinshi zama sukayi suna
ara amsa gaisuwar da yayi masu Abba na cewa."Ba nan Usman ya kawo matarsa Malika ba?."Furzar da numfashi Sadiq yayi yana cewa."Nan ya kawota wani accident ne aka samu komai ban sani ba amma babu rai aka kawota Allah yayi da rabo ma dan munsa ma ta mutu."Kash!

Allah ya rufa asiri ina suke?."Cewar Baba, tashi Sadiq yayi yana tado Usman da yake bacci yana cewa."Yaya Usman gasu Abba nan."Daga haka ya dawo yana cewa."Kamar fa
a sukayi Baba dan har cizo na gani a cinyarta fa sai da akayi mashi dinki ga kuma hakori da aka cire mata abun dai ba kyaun gani."Komai su Baba basu sake cewa ba sai ansa gaisuwar da Usman yayi masu suna mashi Allah ya kyauta gaba suka nufi rest room din aka kwantar da Malika bacci dai suka tadda take dan bata tashi ba nurse din dake kula da ita tayi masu sannu da zuwa tana fita ta basu waje yanda fuskarta ta chanza halitta zaka yarda da ba
aramin duka tasha a hannun Umaima ba dan bakinta ya kumbura saboda hakorinta
aya da ya fita komai dai a fuskarta ya kumbura yasha duka, kallonsu Baba Usman yayi yana cewa."Umaima ce tayi mata wannan mugun dukan Baba."Numfasawa Baba yayi yana cewa."subuhanalillah to mai ya ha
u su?".

Girgiza kai Usman yayi yana cewa."Shine ban sani ba dan har yanzu ban koma gidan ba balle har na tambayi Umaima naji daga gareta so nike ita Malika
in ta farka naji daga gareta dan dawowata kenan na tadda Umaima saman ruwan cikin Malika tana dukanta tana cewa sai tayi ajalinta daman ta gaya mata."Numfasawa Baba yayi yana cewa."Umaima tana gida ta kuma gaya mana abinda ya ha
asu,amma ba zakaji komai daga bakinmu ba Usman sai matarka ta samu lafiya a ha
asu waje
aya ayi magana muji komai kenan."kallon Baba Usman yayi sai kuma ya gyada kai yana cewa."Amma Baba komai ya ha
asu ya dace Umaima tayi mata haka?dubi yanda tayi mata ta kamar wanda ta kashe ma ta wani gaskiya ya dace ayi ma Umaima hukunci a nuna mata kuskurenta dan karda tayi mata abinda take cewa azo ana kuka dan yanzun ma Allah ne ya tsare ai da tayi ajalinta."Babu wasa akan Fuskar Baba yake cewa."Kai ai ba zaka gayaman yin abinda ya dace ba Usman yanda nace haka za'ayi Allah ya bata lafiya ka bari kaga idan ba'a yi hukuncin gaskiya ba sai kace duk yanda zaka ce."du
ar da kanshi Usman yayi yana cewa."Ayi hakuri a bisa kalaman dani Baba na tuba."daga haka bai sake cewa komai ba,amma tabbas dole ya hukunta Umaima idan har yaga za'ayi sankai da nuna banbanci a tsakanin Malika da Umaima ba zai lamunta ba dole ya tsaya ma gaskiya dan ko Umaima ce Malika tayi ma haka ba zai barta ba dan shi bai da gwana a cikinsu dukansu matansa ne kuma ko wace tana da mahimmanci a wajen shi ,da ace bai zo ba da kisan kai Umaima zatayi idan kasheta tayi cewa za'ayi sai anyi binciken mai ya ha
a komai?
Chapter 130 · 0% Book details