← Book details Zabin Iyaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 144 OF 145

Sashe 144

Zabin Iyaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan ya koma gida wanka ya sake yana fitowa ya shirya cikin wani danyen boyal milk maisanyaiyar tsada da laushi a hankali ya dauki cumb yana gyara
asumbarsa da take jin gyara dan ba
ananun ku
i Hamad yake kashe ma fuskarsa ba turaruka masu sanyin kamshi da tsada na alfarma ya saka tana fitowa koda ya sauko main parlo bai tadda kowa a ciki ba sai tv da yake aiki wani wa'azi suke kallo daman Maminshi bata cika zaman main parlo ba tafi zama parlon apartment din uncle Ubaidu idan har yana kasa to can take tarewa wajen mijinta ficewarsa yayi a hankali yake tafiyar yana sakin murmushi dan zuciyarsa dadi take masa idan Umaima ta fado mashi a zuciya haka kawai sakin murmushi yake yana jindadi to wannan wani irin sone haka a cikin lokaci guda yayi nisa a kogin son Umaima ashe haka so yake?so ba wasa ba kuma soyayya ba karya ba a hankali ya bu
e motarsa da aka saka *NAHIYATA 011* a jiki yana fita dan gidansu Hamad ha
e yake da na su Raihan gid
aya suke sai dai kowa sa bangarenshi kuma ko wane apartment da gate din da zaka shigeshi kuma akwai Maingate din da zaka shiga ko wane apartment shiyasa motocinsu duk
aya ne a hankali yake driving din yana sakin murmushin da yake
ara fiddo da zallar sonshi wakar auta waziri yasa mai taken aljannata duniya yana bi yana hango Umaima na sakin murmushi a cikin kwayar idonshi bayan ya iso gidan wajen Umma ya sauka yana gaya mata abinda ya kawo shi dan bai boye mata komai ba har yanda sukayi da Usman, murmushi Umma tayi tana cewa."Hamad kaji tsoron Allah ka gaya man gaskiya kaima zuciyarka ta yarda da Umaima Yar'iska ce?."gyara zamanshi Hamad yayi yana cewa."Wallahi Umma tunda nike ban ta
a yi ma Umaima kallon yar'iska ba shima Usman din nasha gaya mai ya daina abinda yake na kiranta da Yar'iska wallahi Umma koda haihuwa Umaima tayi a waje karshe kenan naji inasonta zan rayu da ita har abada babu gori kuma a tsakaninmu."Firzar da naunauyen numfashi Umma tayi dan Usman ya fado mata a rai tana jin tausayinsa na rasa mace da yake ko
arin yi tabbas Usman yayi nisa baya jin kira tunda har ya yarje ma abokinsa akan ya nemi tsohuwar matarsa hakan da yayi ya
ara nuna masu ba zai maida Umaima ba daman rabon da taga Usman ko yayi mata waya ya gaisheta tun randa ya saki Umaima addu'ar shiriya tayi mashi, sannan tayi ma Hamad wa'azi sosai akan yaji tsoron Allah ya rike amanar Umaima karda yaci mata zarafi kamar yanda abokinsa yaci mata idan har ta yadda da soyayyarshi ta aureshi dan Baba ya yanke hukunci yace ba zasu sake mata auren ha
i ba zasu barta ta aure ZA
IN RAITA duk randa Allah ya fiddo mata dan ana yin sakin washe gari aka ce a maida auren ga Sadiq Baba ya hana yace ai baice yana so ba daga kan Usman ya gama auren ha
i inba yaran ne suka kawo maganar da kansu ba suka ce suna son juna,bayan ta gama yi mashi wa'azi ta kira Umaima akan tazo bangarenta yanzun tana son ganinta...lokacin da Umma ta kira Umaima tsaye take bakin mirror ta gama shafa cream ne ta shafa sai poder da kwali da man baki dan shirin islamiya take lokaci na matsowa turaren ka masu da
in kamshi ta fesa yanda dace dan bata son tana fita kamshinta na tashi babu kyau shiyasa yake kiyayewa sai ta fesa da wuri kafin ta tafi isilamiyar sanda zata isa kamshin ya rage ba kamar yanda tasa da farko na,riga da sikart ne jikinta teabubu da stress sikart
aurin kwali kawai tayi mai kyau na zamani tana
aukar veil dinta ta gala ta fito tana cema Dada."Zan tafi wajen Umma kafin lokacin isilamiyar ya
arasa."Murmushi Dada tayi tana cewa."To Uwata uwar da tafi ta kowa a dawo lafiya Allah yayi albarka."Murmushi tayi tana ansawa da amin ta fita,da kallo Dada tabi Umaima tana share hawayen da suka zubo mata na farincikin shiryar da Umaima tayi wai Umaima ce bata iya fita compound ta shiga
angaren Zainab sai ya yafa mayafi Alhmdulh Allah abun godiya Allah ya
ara shiryawa da
an kowa.

A hankali ta tura kofar ta shiga bakinta da sallama,
agowa Hamad yayi yana sauke fuskarsa a kanta ya amsa sallamar yana sakin murmushi dan wani sanyi da dadi ne suka shiga zuciyarsa yana jin sonta da kaunarta suna mashi yawo a zuciya, murmushi ta sakar mashi tana cewa."Ina wuni?".dabarbarcewa Hamad yayi yana ansawa a jarrabe yana cewa."Fatan kina lafiya?."Da Alhmdulh kawai ta ansa fuska sake tana hayewa sama wajen Umma da sallama ta shiga dakin Umma tana gaisheta tana cewa."Allah yasa ban da
e ba Umma kin kirani lokacin ina shiryawa saboda lokacin isilamiya na gabatowa."Gyara zamanta Umma tayi tana sakar mata murmushi tana cewa."Ko
aya baki makara ba yarlbarka daman bako Kikayi yana
asa."Bako ta maimaita a zuciyarta tana kallon Umma tana cewa."Ai ni da shigo banga wani bako ba Umma Yaya Hamad ne na gani yana danna waya."Murmushi mai sauti Umma tayi tana cewa."To ai Hamad a bako yake a gidan nan kuma wajenki yazo dan yana tafe da magana mai girma a bakinshi shawarar da zan baki
aya ce karki yanke hukuncin cikin gaugawa ki
natsu kiyi nazari Umaima tashi kije Allah yayi maki albarka."Firzar da naunauyen numfashi tayi sai kuma ta gya
a ma Umma kai tana saukowa tasan maganar bata wuce ta Yaya Usman to zata biye mashi warning ne dan tana ganin girman shi to ya kama girmansa duk randa ya sake yi mata maganar Yaya Usman zata iya zaginsa ne dan bata ba Yaya Usman bata komawa gidansa har abada koda kuwa sakin yar'iskar matarsa yayi dan ta komawa saukowa tayi tana sake yi mashi sallama ta samu kujera nesa da shi tana zama tana
ara gaisheshi..sake ansawa yayi yana gyarawa da kyau yana Kallonta murmushi ya saki yana kiran sunanta ansawa tayi ba tare da ta kalleshi ba dan ta fara takura da irin kallon da yake bin ta da shi ba duk da ba Kallonshi take ba amma tana jin yanda idanunsa ke yawo a jikinta numfasawa yayi yana cewa."Daman Umaima daman...kasa idawa yayi dan samun kanshi da tsoron Karda taki ansar tayin soyayarsa kuma shi yana da tabbacin mudun Umaima tayi facali da tayin soyayyarsa zai iya shiga cikin wani mayuwacin hali wanda shi ba zai iya ma kwatantata shi ba, shahada yayi yana cewa."Daman Umaima nazo ne dan na fallasa maki sirrin dake raina Umaima,Allah ya jarabeni da tsananin sonki ina sonki Umaima ina son na aureki ki zamo matata uwar
ana Umaima."Tashi Umaima tayi tana kallonshi idanu waje hawaye na zubo mata ido kamar an kunna famfo tana jan baya tana girgiza kai ta fice parlon da gudu tana rushewa da kuka, tashi Hamad yayi yana kiran sunanta amma har tayi nisa ta kusa cinma
angaren Dada tsaye yayi jiki sanye yana jin shima hawayen suna zubo mashi saman fuskarsa zuciyarsa ba dadi yana jin ba zai ta
a barin gidan ba har sai Umaima tazo ta gaya mashi matsayinshi a zuciyarsa saukowa Umma tayi dan yanda taji yana kiran sunan Umaima yasa ta fito dan ganin lafiya,ganin Umma yasa Hamad zuwa ya kama hannun Umma yana hawaye yana cewa."Ki taimakeni Umma Wallahi ina son Umaima ba zan ta
a iya yin rayuwa babu Umaima ba dan Allah Umma ki taimakeni."Share mashi hawayen Umma tayi tana cewa."Naji daina hawaye sai kace ba jarumin maza ba Hamad?

Yanzun ka tafi gida zamuyi magana gobe dan yanzu Umaima isilamiya zata idan ta dawo zanje muyi magana da ita komai kenan zaka ji."Sauke numfashi Hamad yayi yana cewa."To Umma amma Umma ina sonta dan Allah ki taimakeni ta mallaka man zuciyarta zan rayu da ita har abada Wallahi Umma."Jinjina mashi kai kawai Umma take dan ta lura da bai ma cikin hankalinshi duba da yanda yake maganganun dakyal ta lailasheshi tasa cikin drivers din gidansu wani ya maida Hamad dan da gani bai iya driving a yanayin da yake ciki karda a samu damuwa.
Chapter 144 · 0% Book details