← Book details Zabin Iyaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 145

Sashe 63

Zabin Iyaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

tana faduwa asa take mata wuya yayi yana cewa."Kasheki kawai zanyi na huta sai nayi ajalinki tunda baki da kunya ban maki tsakani da matata ba?ban gaya maki ba ruwanki da matata ba?kin rainani ai ko zan maganinki yanzu."kuka Raihana take kawai dan har ta sa akas da sake numfashi a duniyar dan yanda ya take mata wuya ko numfashi gagararta yayi, mi ar da ita yayi yana cewa."Biyoni ko naci ubanki dan ubanki yanzu nan."Bin bayanshi tayi ta hanyar da ya shigo dan ita bata ta a tunanin akwai hanya a wajen ba ashe duk adon da akayi ma wajen akwai hanya,zama yayi saman kujera yana cewa."Tun da magana batayi maki haka bugu shima duk bai maki ko?baki daina rashin kunyar da kike mata kullum to dan ubanki kama man kunnenki."Zaro ido Raihana tayi tana yarfa hannu tana kuka tana cewa."Dan Allah Yaya Raihan dan girman Allah na tuba ba zan sake ba kayi man rai ba zan ara ba karda kasani kamun kunne wallahi zan iya mutuwa ban ta a yi ba."Tashi yayi yana zare belt yana yin kanta yana cewa."Zaki kama kunnenki ko sai fasa maki baya?"Girgiza mashi kai tayi tana ha a hannayenta waje aya alamun ban hakuri da lailashi tana cewa."Wallahi ba zan sake ba Yaya Raihan na tuba dan Allah ka yafe man."Amma duk kukan da Raihana take tana ba Raihan hakuri hakan bai sa yaji tausayinta ba a zuciyarshi tsula mata belt din yayi ban arewa tayi tana kama kafafunshi tana bashi hakuri amma ya i sai da ya sakata kama kunnen komawa yayi ya zauna yana cewa."Idan gobe zaki sake yi mata rashin kunya ba zan fasa saka ki kama kunne ba,tunda baki da kunya na gama bugunki sakara wawiya ni banda kaddara da tsotsayi mai ya ha a biri da gada dole na sakeki dole ki barman gida dan ba zaki kashe man aure ba."ita dai Raihana kuka kawai take tana durkushe tana kama kai, Daulah ce ta fito janye da trolly zata wuce ta gefensu Raihan ya riko trolly din yana cewa."Babe kin san ina sonki ba zan iya rayuwa babu ke ba idan har kika barni kamar kin tafi da numfashi na ne daga gangar jikina dan Allah ki rufan asiri ki koma kinga ina hukunta ta zan mata tsakani dake dan Allah Daulah karki barni ina kaunarki."kallon Raihana Daulah tayi da take kama kunne sai kuma ta kalli Raihan fuskarta babu annashuwa duk tasha kuka tana cewa."A gaskiya Babe idan har ta sake yi man abun da tayi man yau komai zakayi mata sai na rabu dakai dan ba zan iya zama da mace mai irin halinta ba na rashin kunya ai ko ba komai idan ba zata auki ni a matsayin matar yayarta ba ai ta bani girma nafinta a shekarun da nayi."Hakuri sosai Raihan ya bata yana maida trollyn da kanshi sannan ya dawo ya cigaba da gadin Raihana ita kuma Daulah tana kwance saman cinyarshi tana sakin murmushin farinciki dan ko haka aka tsaya Raihan ya biyata balle ba haka zata tsaya ba dan sai Raihana ta gane ta mareta tana jiran zuwan Haulat ne sai ta saka yarinyar a masifa da bala'i,tun Raihana na ganin abun zai zo da sauki har kafafunta sun gaza jure kamun kunnen da take ga hannayenta da suka sage dan ta kusa 30mn tana abu aya faduwa tayi tana rushewa da kuka tana cewa."Dan Allah Yaya Raihan na tuba zan mutu hannuna kafa zasu karya."Tsaki yayi yana cewa."Su karye mana dan ubanwa keda asara?Ba dai rashin kunya bace aikinki?kin raina man mata har kike marinta ko?"Girgiza kai tayi tana ta tuba ita ba zata sake ba,sosai yayi mata fa a sannan yasa ta matso dan ba Daulah hakuri, agowa tayi tana kallon Daulah dake kwance a saman cinyar Raihan tana danna waya kallon Raihan tayi sai kawai ta ara fashewa da kuka ita bata ce bata bada hakurin ba, gya a kai Raihan yayi yana cewa."Okay baki iya bada hakuri ko?oya go and continue your work."Girgiza kai tayi tana mata matsawa tana cewa."A'a zan iya."dan shiru tayi sai kuma tace."Kiyi hakuri."Tsawa Raihan ya buga mata yana cewa."Maza koma ki cigaba da kama kunnenki lokacin da kika shirya bata hakurin kin taso."cikin kuka Raihana ta matsa tana ba Daulah hakuri cikin biyayya sai da ta bata hakuri kusan sau biyar sannan Daulah tayi mata kallon sama da asa tana cewa."A kiyaye gaba dan rashin kunya ba abun ne mai kyau babu riba a cikinta."daga haka bata sake cewa komai ba,hawaye ne masu zafi da ra i suka zubo ma Raihana dan tafi jin zafin hakurin da ta ba Daulah akan kamun kunnen da ya sakata duk da kuwa ita ka an tasan masifar da kafafunta suke mata,ganin irin kallon da Raihan yake mata yasa ta furzar da naunauyen numfashi tana cewa."To Nagode."Tashi tayi tana angwashi zata shiga room dinta Raihan ne ya dakatar da ita yana cewa."Hado mana tea da sandwich."Waigowa tayi tana Kallonshi sai kuma ta gya a kai tana kuka ta shiga kitchen din,daura kanta tayi jikin freeze tana mai rushewa da kukan ba inciki sai da tayi mai isarta sannan ta fara ha a abinda ya bu ata ta kawo masu ta wuce room dinta fa awa tayi saman sofar dake cikin dakin tana mai rushewa da kuka tana dukan kanta tana cewa."Never impossible ba zan yarda da cutar da akayi man ba."kuka kawai take tana wurgi da sweet-pillows din dake a room din...Hakuri ya ara ba Daulah yana bata Sandwich da kanshi yana cewa."Abinda nayi mata da kanta zata bar gidan nan,ba dai tace ta sadaukar da farincikinta ba to wannan punishment din kawai zan dinga sata zata gudu ne rabu da ita Babe dole ta fita ta bar maki gidanki.'kissing dinshi tayi tana cewa."Shiyasa nike sonka Masoyina a kullum godema Allah nike da ya bani miji mai sona da kishina wanda bai son ganin acin raina much love."Sosai ya bata dinner din taci suna gaya ma juna kalamai masu dadi cikin so da kauna.
Chapter 63 · 0% Book details