← Book details Zabin Iyaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 145

Sashe 72

Zabin Iyaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Saukowa yayi hannushi dauke da Alkur'ani yana samun waje ya zauna babu wasa a saman fuskarsa yana cewa."Umaima."Kallonshi tayi tana watsarwa tana ansawa ba tare da ta kalleshi ba, numfasawa yayi yana mai cewa."Sauko muyi karatu na lura idan na saka maki ido karatunki lalacewa zai yi kwana biyu ba'a yi karatu ba kuma hankalinki kwance."gyara zamanta tayi tana kallon Tv ba tare da ta kalleshi ba tana cewa."Aa ni kullum sai nayi karatu ai."cikin fa
a ya fara cewa."Wai Umaima maike damunki?wata irin zuciya ce gareki wanda bata jin yi hakuri kuma ta ina kikayi karatun bayan ni ke
ara maki?"rage volume din wa'azin da take ji tayi tana Kallonshi tana cewa."Yaya Usman nifa ba abinda kayi man,kuma ban kai matsayin da zakayi man laifi ba batun karatu kuma ai ina da quri'an channel anan nike bi kuma ina ganewa."Furzar da numfashi yayi yana cewa."Naji baki kai kiyi laifi ba Umaima nidai sauko nayi maki karatu da marece zani isilamiya."Ta
e baki tayi tana cewa."Ka barshi nagde Yaya kaje kayi shirin zuwanka isilamiya kawai."cikin fa
a yake cewa."To wallahi baki isa ba,dolenki ko kinaso ko baki so sai nayi maki
ari,Umaima karki yarda ki kaini bango zan
ata maki rai fa,karki maidani sakaran dole mana ina maki magana kina maidani wani sakarai."komai bata ce mai ba sai ma maida hankalinta da yayi a saman Tv tana cigaba da kallon wa'azinta tana nuna ta manta da zamanshi a wajen ran Usman ne yayi bala'in
aci yana jin kamar yayi mata mugun bugu dan rainin hankalin da Umaima take mashi ya fara isarshi yarinyar kamar kafirai farko yana ta bata hakuri ana bin ta amma ta
i hakura kuma shi baijin dadin irin wannan zaman da suke ko sallama yayi shi baijin ma tana amsa mashi daman duk son da take fadi tana mashi duk karya ne tunda bata damu a damuwar da ta jefa shi ba,tsawa ya buga mata yana cewa."Zaki tashi kije ki dauko Alqur'ani nayi maki
ari ko sai na tattaki a nan wajen Umaima."Sun
uro baki tayi tana dira
afafu ta shiga room dinta ta dauko jikkar ta fiddo Alqur'anin tana bu
ewa komai bata ce mashi ba, girgiza kai yayi yana fara yi mata
arin bayan sun gama ya fara yi mata wa'azi akan hakuri da yafiya,dakatar dashi tayi tana
aga mashi hannu tana cewa."Dakata dan Allah Yaya Usman."Wani kallo yayi mata yana cewa."Ke Umaima dan ubanki ni zaki dakatar haka? wa'azin ne baki so komai?anya kuwa aljannu basu shigeki ba."Komai bata ce mashi ba sai da ya buga mata tsawa sannan ta kalleshi tana cewa."wa'azin ne bani bu
ata Yaya Usman dan ko kayi man ba shiga zai yi ba ka manta wacece a gabanka?Umaima Yusuf ce fa yarinyar marar tarbiyya yar-kwalta karuwa kaga ba amfanin ka
ata lokacinka wajen yi ma karuwa wa'azi wanda take fama da najasa."Tasowa Usman yayi yana
aga hannu zai wanka mata mari, rintse ido tayi tana jiran saukar mari a saman fuskarta gani tayi hannu
age amma bai
aura mata marin ba,tasowa tayi tana cewa."Mararni mana Yaya Usman mai yasa ka fasa marin nawa?daman ai ni ba kowa bace a wajenka banda mutunci da kima dole ka iya daukar hannu ka mareni."Kuka ta fashe dashi tana cewa."Wallahi sai ka sakeni Yaya Usman na gaji ban san zama da kai yanzu sai ka sakeni kayi rayuwarka da za
in ranka nima naje nayi rayuwata har na ha
u da za
in raina nima na aura."Tsaki yaja yana cewa."Sakin ki zan sake ki amma ba dai yanzu ba dan wallahi karya kike na sakeki yanzu idan har kina son na sake ki dolenki ki natsu mu gama karatu nayi maki al
awarin kina saukewa zan sakeki daman mai zanyi dake ai ko mata suka
ara ba zan ta
a zaman aure dake ba dan ni Usman ba zan ta
a cin saura ba nafi karfin sauran gardawa yan'iska kuma karya nayi da kike ta wani kumfar baki dan ance maki karuwa to ba
aruwar bace?"Sauke nunfashi yayi yana nuna ta da tsaya yana cewa."Wallahi Umaima ki kiyayeni ki fita idona na kulle na lura kina son raina man wayau a gidan nan to zan karyaki dan wallahi zan maki wula
ancin da ba zaki ta
a mantawa dani ba a rayuwarki dan baki isa ki tadaman hankali ba ina zaman lafiya tun wuri ki dawo a hankalinki idan ba haka ba nayi pieces dake."
Murmushi Umaima ta saki tana cewa."Daman ai ni karuwa ce ko baka fadi ba Yaya Usman ni karuwa sai dai Alhmdulh tun da Allahn da ya halliceni yana ansar tuban bayinsa ai alhmdulh kuma na tuba na tubanma dadin abun Allah yake ansar tuba ba wani ba da wani ke ansar tuba da an bani kuma banji komai dan kace man karuwa Yaya Usman tunda idan aka tsaga jinin karuwa za'a ga naka a ciki."Haka ai kaki ce ko?kuma aure sai nayi babu fashi duk wannan haukan da kike duk akan zan yi aure kuma baki isa ki hananin auren za
in raina ba mace kamila mai ilmi da tarbiyya ga hankali uwa uba natsuwa bata maida ma manya magana ita bata san gardama ba ina maki fatan kiyi koyi da halin Malika saboda gaba dan mace ta gari ce Malika hafizar Alkur'ani."Daukar jikkata tayi tana bar mashi wajen komai bata sake ce mashi ba dan
ata lokaci ne ma ta bu
e baki tace mashi wai bata kishishi tayi aikin banza kenan yin kishin wanda bai sonta ai ita wahalace ai wallahi dolenshi ma ya saketa ai yana cewa sai ta sauke ko?ai ta kusa saukewa tana saukewa zasu rabu kuma rabuwa ta har abada yaje ya auri za
inshi daman ita ina ruwanta ya kawo ukku bayan Malika ko a jikinta dan ta kusa rabuwa da Usman...Zama Usman yayi yana dafe kanshi wai mai Umaima take nufi dashi ne daman haka take? yarinya ta sauya lokaci guda ta zama wata boss shi har tsoro take bashi ma,tashi yayi ganin lokaci ma yana kure mashi karda ya makara wanka yayi yana saukowa dan tafiya Kallonta yayi dan har ta fito tana maimaita karatun da yayi mata dan dakatawa yayi yana cewa."Umaima na tafi isilamiya."Kallonshi batayi ba ta cigaba da karatunta girgiza kai yayi yana fita zuciyarshi batayi mashi dadi ko ka
an dan shi da wannan shariyar da take mashi gwanma ta saka shi gaba tana kuka amma daga yace zaiyi aure shikenan yarinyar sai ta
auke mashi yar maganar ma da suke a da duk ta daina da wannan tunanin ya isa isilamiya.
Chapter 72 · 0% Book details