Sashe 105
Zabin Iyaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Allah ya baka hakuri tunda gaskiya ce baka son na fada tunda yana lafiya ai sai masu aure su tafi wajen matayensu mararsa aure kuma Allah ya basu zuciya suyi."Murmushi Hamad yayi yana cewa."Ai da in abun bani aya bane banda mata a wajen."Dariya Kk yayi yana cewa."Rabu dashi Hama an kusa daina yi mana gorin aure,Raihana dan shiga room din shi akwai wani briefcase white ki kawo mana shi pls dan gobe jiranshi ba zamu tsaya yi ba wallahi zamu tafi kuma zai ha u dani ne ata lokacin da yayi akan wata Daulah can."ita dai Raihana murmushi tayi tana zuwa saman tv stage ta dauko briefcase din dan anan parlon yayi Wurgi dashi ya kama gabanshi ansa sukayi suna mata arin ku i a account dinta sannan suka tafi tsalle ta kama yi da murna dan ta samu sama da million biyar a wajensu...Dogon tsaki Kk yaja yana cewa."Ina yin magana yanzu zaku ce kishi ne bayan kuma bi ba kishin da nike tun randa Daulah ta za i Raihan kaina na cireta a zuciyata ina hango girman rainin da Raihan yayi mana yau wallahi guys yasan mahimmancin aikin da zamuyi yau fa amma ya biye ma matarshi yanzu haka suna wani guest house din shi suna soyayyarsu mu ya barmu da zaman jiranshi amma gaskiya idan har ya sake yi mana haka gaskiya ni ban zan shiru ba,haba mana ai soyyaya daban aiki kuma daban."Kallon KK Usman yayi yana cewa."Ai ko wannan ma ba kyaleshi zamuyi ba sai mun nuna mashi abinda yayi bai kyauta ba Saboda Karda ya sake maimaita mana ina mamakin yanda ma yake wata rawar kafa akan Daulah bayan ga Raihana Allah ya ba shi mace kamila da ilimi da kuma kamun kai."Dariya Hamad yayi yana cewa."To ya za'ayi bar zuciya da abinda take so kawai,kai yanzu zuciyarka duk kyaun Umaima ba so kake ka rabu da ita ba kuma duk yanda Raihana tayi kyau bata kai Umaima ba idan basu zo tangan ba to aya tafi amma a haka kake cewa baka so tun a kanka ai ya dace kasan shi so ba ruwan shi da kyau."Shiru Usman yayi yana kallon Hamad ta Kasan ido wato shi bai da ikon magana sai Hamad ya dakatar da shi akan dai Umaima ne ba gwanma Daulah sau dubu ba da Umaima dan ita Daulah duk lalacewarta ta yawon iskancinta tana kwana gidansu kuma bata fiddo tsiraici ta tura ma duniya ita kuwa Umaima fa?ba sai dai a tayata da nema mata gafarar Allah ba,ai shi iyayenshi da suka tashi yi mashi za i basu za a mashi mace ta gari ba kamila hafiza irin Raihana ba sai suka za a mashi Umaima taya zai zauna da Za in iyayenshi bayan kango ce sauran wasu mazan dole ya nemi za in ranshi wanda ta dace da daidai da rayuwarsa kuma ko yanzu bai da niyar zama da Umaima a gidanshi jira yake dai ta karasa saukewa dan ta kusa shintin tana saukewa zasu yi hannun riga a dai gaisa babu maganar aure dan ba zai iya zama da ita ba,komai basu sake cewa ba Usman aka fara saukewa gida sannan suka wuce gidan su Kk dan a can Hamad zai kwana...Zaune Raihan yake a cikin mota a gidan Haulat ba dan tunda yazo ya buga tagumi na abinda ya iya tadashi dan ko sallah da ake kira kasa tashi yayi yaje yayi zauna dai zaune yana auna irin rashin mutuncin da zai yi ma Raihana idan har ya samu ya maida Daulah gida Raihana ba zata sake kwanar mashi gida ba daidai da second ba zata sake kwanar mashi gida ba dan ya fahimci ita ce take neman kashe mashi aure yayi biyun babu dan wallahi idan har ta kashe mashi aure itama ba zata ga da kyau ba dan shi yana iya kasheta akan Daulah ya gwammace ayi mashi komai za'ayi mashi bayan ya kashe Raihana,kuma komai ya faru iyayensu ne suka ja masu komai dan da tun farko basu ha a auren ba da duk abinda ya faru bai faru ba kuma ba yanda bai nuna bai son auren ba amma Abbie ya i saurarenshi to zasu yi kukan nadama da kuma dana sanin hada auren komai zaizo karshe ne hakurinshi ya are zai tabbatar ma da Raihana cewa zai iya rabuwa da kowa akan Za in ranshi jin ana kiran mangarib ya tashi yayo alwallah da sallah bai dawo ba sai da akayi isha'i shiru shiru gwada kira yayi kashe hakuri yayi yana konawa gida yaga ko ma ta koma gida bai sani ba bari yaje ya gani idan bata nan yaje gidansu a karo na biyu ya gani ko za'a dace..