← Book details Zabin Iyaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 145

Sashe 42

Zabin Iyaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiga kitchen din
asa yayi yana kallon yanda duk ta
ata plate babu wankewa babu komai girgiza kai Usman ya yi tana kwala mata kira fitowa tayi daga ta sai wata halfvest mai flowers da unding gashin ta yasha gyara sai tashin kamshi yake,kallo
aya yayi mata yana kauda kanshi yana cewa."Je ki saka kaya."Kallonta kanta tayi daga sama har
asa tana cewa."To Yaya Usman mai wa'nnan kayan sukayi kuma dan Allah."cikin rashin wasa yake cewa."Cewa nayi kije ki saka kaya, wa'anan kayane daman haka ake saka kaya maza ki sako kaya ko nayi ball dake idan har ina maki magana kina man gardama sai na falfalla maki maruka."Maida kanta
asa tayi tana cewa."To yi hakuri ba zan sake ba."daga haka ta juya ta sako wasu kayan dogon wando ne sai farar riga marar dogon hannu, Kallonta yayi sai kuma yace."Ai baki da kayan hausawa ko?."Turo baki tayi tana cewa."Ai ban iya sakawa ba."tsaki yayi yana cewa."shigo nan ni ke kika sani ai amma daga yau karda na sake ganinki da shiga irin ta arna na dai gaya maki."To tace tana matsawa kusa dashi harararta yayi yana cewa."Matsa can ji yanda kika wani shigeman sai kace ciki zan maida ki."dan shiru yayi yana cewa."Yanzun wanann plate din wa kika ajiye ya wanke maki su?a haka kike son shiga aljanna babu tsafta?."hakuri dai ta bashi sannan ta wanke duk da ba wasu wankuwa sukayi ba sosai sai da ya taimaka mata sannan suka fito zaunar da ita yayi yana yi mata bayanin yanda ake yin wankan tsarki tun daga
aukar niya da yin alwalah da kuma wanke kai ta tabbatar ruwa ya shiga ko ina a kanta sannan ta raba jikinta gida biyu ta fara da bangaren dama ta wanke har sau ukku sannan ta dawo ma haggu itama tayi mata sau ukku sannan ta watsa ma bayanta ruwa sosai ya kuma murza da cu
a jikinta ta ta tabbatar da ko ina yaji ruwa sai ta wanke kafafu ta barma Allah, sannan yace na janaba ba haka ake yi da na haihuwa kawai niyace banbanci yayi mata karatu sosai akan wanka da kuma koya mata sallah duk da ta iya Sallah amma sai da ya
ara nuna mata ya tambayeta inda ta tsaya a karatu izufi
aya shima ba gam ba kuma hidisai ba tasan ko
aya ba take yayi mata
ari bayan ya saka ta saka hijab sannan kuma sukayi arba'iuna da
awa'idi sannan kuma yayi mata wa'azi sosai wata channel ya nuna mata yace tayi kokari tana kallo ana saka wa'azi masu mahimmanci da amfani sosai jikin Umaima yayi sanyi duba da yanda Usman yayi mata wa'azi cikin hankali mai ratsa jiki ya nuna mata ilar fiddo tsiraici sannan kuma ya gaya mata irin shigar da ya dace matar aure tayi da kuma budurwa ganin lokacin zuwa islamiyya yayi ya tashi yana cewa."To zan je na shirya dan zuwa islamiyya kafin na dawo ki tabbatar da kin iya karatun da nayi maki kuma kice abinci."Murmushi ta saki tana cewa."To Yaya Usman ina sonka."Kallonta kawai yayi yana hayewa sama wanka yayi cikin sauri sauri yana fitowa ya saka farar jallabiya ya na
a veil dinsu na maza sannan kuma ya
auki key dinshi da abinda ya ke bu
ata ya sauko karatu take bata tashi daga inda ya barta ba,ce mata yayi."Sai na dawo idan za'ayi la'asar ki tabbatar da kinyi wankan tsarki kafin kiyi sallah." To tace mashi tana binshi da kallo har sai da ya fita sanna ta maida kanta akan karatun da take dan tana son ta iya sosai.

Ganin lokacin sallah yayi ta tashi kamar yanda yace sai da ta fara wanka sannan ta shirya cikin abaya wata dark blue sosai tayi mata kyau dan ita zata iya lissafa saka abaya da tayi a rayuwarta tana da su amma bata iya sakawa dan ji take sun yi mata nauyi sosai,carpet ta shimfida ta dauko counter ta ajiye sannan ta kafbara sallah bayan ta gama tayi addu'a sannan ta tashi ta kitchen ta shiga ta samun abinda ta ha
a daidai cikinta tana son tayi abincin dashi amma tasan baci zaiyi ba dan tana sane da yanda Yaya Usman yake gudunta ta tabbata ba zai ta
a cin girkinta ba zama tayi tana kunna kallo tana kallon wa'azin da ake haskawa kuma tana fahimta sosai....koda Usman ya isa islamiyya kafin su shiga aji sai da sukayi sallah kuma shi yake jan sallar bayan sun gama headmaster ya kiranshi zuwa yayi suka gaisa dan shi Usman kyauta yake koyawa baya bu
atar a bashi komai shi wani lokacin ma yana rabama Malaman ku
i da kayan sawa harda na abinci dan shi ya taso cikin ku
i koda bai aikin gwamnati to dukiyar Abba ta ishe su kaf family din su har da jikoki balle kuma dukansu kowa yana aiki shiyasa salary dinshi yake rabarwa dan duk da yana ansar salary hakan bai hana Abba yi masu
arin ku
i a account ba dan ba'a sati sai yabi kowa da ku
i sama da 20M yace su suka mai dan zuwa office kuma duk da haka duka motocin gidan duk gidan man da zasuje saka mai ba'a ansar ku
insu dan already Abba yayi bill shiyasa baya cin salary dinshi sai dai yayi kyauta dasu,bayan sun gaisa da Headmaster yayi mashi bayanin sabuwar dalibar da sukayi kuma ga inda take a hadda,dan shiru Usman yayi yana kallon headmaster yana cewa."ba
i taka ba Ranka shi da
e amma kana da tabbacin tayi hadda maikyau da har take arba'in?."Jinjina kai yayi yana cewa."Kaima kuma kayi magana nima nayi mamaki sosai."Shigowa Malika tayi cikin natsuwa da shigar kamala murmushi headmaster yayi yana cewa."Shkenan ma Malam Usman gama tanan ai daman nace ta dawo yanzun duk yanda kace kuma haka za'ayi."
agowa Usman baiyi ba balle har ya kalleta sai ma kallon Headmaster da yayi yana cewa."Msha Allah hakan ma yayi yanzun kafin mu ansheta sai munyi mata interview dan gane haddar tata ta zauna ko tana rawa idan har tana rawa sai mu ga wani aji ya dace a ajiyeta sai naga kamar haka zaifi."jinjina kai headmaster yayi yana cewa."Ai ba damuwa duk yanda kace ai dai-dai ne."Tashi yayi yana cewa."Yanzun sai ta biyoni zamu je a hall sai a ha
a malamai su bamu minti talatin har da ma
aliban dan ayi a gabansu zatayi mana karatu anan sai a san ajin da ya dace da ita." Da haka ya fita Kallonta headmaster yayi yana cewa to kinji dai Malama sai ki bishi Allah yasa a dace."murmushi Malika tayi tana mashi godiya sannan ta tafi tana jinjina girman kai da isa da izzah irin na Usman tabbas sai tayi da gaske wajen cinma burinta akan shi dole Umaima zata anshi auren Usman dan yafi Umaima din kyau ga aji ga kuma natsuwa amma zatayi maganinshi kuwa da haka ta isa hall din waje aka bata ta zauna bayan kowa ya zauna aka gabatar da ita matsayin sabuwar daliba sannan aka gabatar da karatu Usman ne yake ja mata karatu sai ta dauka ta cigaba yi cikiya yake ja mata amma sai ta anshe ta cigaba yanda take karatun take raira karatu dole kaji ta burgeka ga natsuwa da kamaiwa haka take karatun har lumshe ido take sosai ya gwadata yayi mata tambayoyi ta bashi ansa sannan suka gama bayan sun gama headmaster ya ba mata sannan kuma suka
auke ta a matsayin sabuwar daliba kuma a babban aji wato ajin Malam Usman, sauke nauyin nunfashi Malika tayi tana jin sanyi a ranta dan kuwa yanzu za'a fara wasan ta aiyana a cikin zuciyarta duk da ba mai cewa tana kallon kowa dan kanta a kasa yake amma kaf idanunta suna kan Usman tana
ara nazarta waye shi ta kuma ina zata bullo mashi har suyi soyayya mai
arfi da zai kai su ga aure wannan kenan...

Share pls
IN IYAYE*
_Parental choice_
*NA*
*JAMEEY*
*BOOK ONE*
_Bissimillahir Rahamanir rahim_
https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ?mode=ac_c
Cikin fa
a da masifa Dada ke cewa."Nidai wallahi Abubakar na kasa gane inda Usman ya dosa haba wannan wani irin kulle ne ace tunda aka
auki yarinyar nan aka bashi ko sau
aya bai kawo ta gida ba sai kace bata a kowa nidai yau din nan sai naje naga a wani hali Uwata take ciki karda ina nan zaune sake da baki shi kuma yana can yana ko
arin kashe man Uwa dan ni tuni na lura zuciyar Usman ta rage tausayi da imani."Murmushi Baba yayi yana cewa."To Dada ai ba cewa akayi ba karda kije ba, kiyi hakuri garin ya
ara haske amma kinje masu da safe haka ai ko bacci basu tashi ba."daukar hijab din ta tayi tana cewa."Kanka ake ji ai sai kai ta yi to ina ruwana da rashin tashinsu daga bacci idan ma basu tashi ba ni sai na tadasu,ina dalili tunda ita Sumayya ta sallama mashi yarinyar ni ba zan zuba ido ya kashe man Uwa ba,ba zan yarda ba wani irin bacci ne suke da basu tashi har yanzu ba Abubakar."Tashi yayi yana cewa."To Dada muje sai a kaiki amma yanzun duka ko takwas ai baka kai ga yi ba."komai bata ce mashi ba sai ma gaba kawai da tayi tana cewa."Karda takwas din tayi kai ka damu da wata takwas ni ta Uwata nike."bin bayanta kawai yayi yana jin yanda take ta fa
a bai dai ce komai ba karda ya sake tamkawa ya sake sabon laifin yasan halin Dada balle ma akan Umaima dan tun auren da kwana
aya take nacin son zuwa yake hanata da dubara da wayau har anyi sati ukku da auren ai tayi ko
ari ma...koda suka fito compound drive din Dada ya taso dan daman a shirye yake akan tafiyar tun jiya da dare ta kira shi ta gaya mashi zai kaita gidan Umaima ana fitowa sallar asuba su dauki hanya sanda gari zai waye sun isa,shi yayi mamaki da har suka kai yanzu basu tafi ba, bu
e mata motar Baba yayi ta shiga a dawo lfy yayi masu har sai da suka fita get na farko sannan ya sauke ajiyar zuciya yana nufar tashi motar dan tafiya office shima.
Chapter 42 · 0% Book details