Sashe 50
Zabin Iyaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
ya zama hoto dan haka kibar saka kyau a batun aure kawai kice na dace ina da ilimi mijina yaji dadi kamar yanda Kema mijinki ya dace da kike da ilimi Kinga ai mu duka mazajenmu sun dad'i duk da ke Kinyi auren ni kuwa muna ta addu'a dai Allah ya kawo mana na gari masu imani da tsoron Allah kuma masu aiki da ilimi kin san wasu ga ilimin basu aiki dashi suna ake kira da ga sani ga barna." Jinjina kai Zainab tayi tana cewa."haka ne kuma Malama Malika dan wallahi mijin Yayata ga dai ilimin yasan komai amma baya aiki dashi sai dai hakuri da addu'a dan yafi mijina zurfi a ilimin addini amma mijina yanda yake kyautata man yake kiyaye duk abinda ya dace ga addini amma ita nata mijin sai addu'a kawai Allah dai ya fiddo maki da na gari zamu sha biki kam."Murmushi kawai tayi tana cewa."Amin ya Allah na gode sosai bari a kai mashi wayarshi ko?."Murmushi Usman yayi dan tunda suka fara maganar duk a kunnenshi har suka gama da sallama ya shigo yana daukar wayar yana kallon Malika yace."Malam Malika idan babu damuwa ina son magana dake."cikin mamaki take kallon Usman tana cewa."Ni Malan?." aga mata kai yayi yana ficewa daga Office din ba tare da ya jira ansarta ba, ta ata Zainab tayi tana cewa."Ke kuwa ki tashi kije Allah yasa abinda nike addu'a ne zai faru dan Allah Malama Malika kun dace da Malan Usman sosai."Girgiza kai Malika tayi tana cewa."Rufan asiri ai Malan Usman yafi karfina wace ni?kika san ko yana da mata?."Kamo hannunta Zainab tayi tana cewa."Ba namijin da yafi karfin mace kamar yanda babu macen da tafi arfin namiji kedai ki nemi za in Allah kuma maganar mata gaskiya malan Usman bai da mata taya ma zai yi aure bamu sani ba bayan duk weekend a makaranta muke rayuwarmu dashi gaskiya bai da mata."Jinjina kai tayi tana cewa."Nidai kibar wannan maganar nasan ma ba ita bace kawai dai wata magana ce ta daban kuma dake zan ma tafi."Girgiza kai Zainab tayi tana cewa."Ke dai ki tafi Malama Malika in shaa Allah khair ne."tashi Malika tayi tana nufar office din Usman a bakin kofa ta tsaya tana yin sallama ansawa yayi yana cewa."Bissimillah malan Malika."shigowa tayi tana tsayawa daga baya murmushi ya sakar mata yana cewa."Daman ce maki zanyi idan ba damuwa ki tambaya man gidanku zan turo manya na a nema man iznin neman aurenki dan ni gaskiya Malika na yaba da hankalinki da kuma natsuwarki daman irin matar da nike mafarkin nema da samu kenan a rayuwata ba zan so ace mun fara soyayya ba har sai da sanin iyaye kamar yanda Muslunci yace."Numfasawa tayi tana maida kanta asa tana cewa."To Malan ba damuwa zan masu maganar in shaa Allah fatanmu Allah ya za a mana abinda yafi Zama alkhari a rayuwarmu."Murmushi ya sakar mata yana cewa."Amin ya Allah ki ban number dinki idan kin tambayar man kinga sai ki gaya man ko?."gya a kai tayi ta saka mashi number tana tafiya cike da nuna jin kunya dan ta i yadda da ko Kallonshi tayi da kallo ya bita yana sakin murmushi arasa abun da yake yi yana taitarawa ya tafi dan sai ya biya main house dinsu dan kai maganar Malika dan ya da e da auna hankalin yarinyar da natsuwarta kuma gaskiya dabi'unta da tarbiyyarta gami da hankalinta sun kwanta mashi tabbas Malika mace ta gari ce ga ilimi ga natsuwa Allah ya anshi addu'arshi kuma yana gode ma Allah...koda Malika ta koma class dinsu gaya ma Zainab yanda sukayi tayi sosai tayi murna kuma Malika ta hanata gaya ma kowa dan yace mata ana son ka boye nema ka baiyana samu kuma ta gamsu da maganarta bayan sunyi sallah aka tashi a bakin mota ta raka Zainab sannan ta wuce gida.