Sashe 62
Zabin Iyaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Share pls IN IYAYE* _Parental choice_ *NA* *JAMEEY* *BOOK ONE* _Bissimillahir Rahamanir rahim_ https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ?mode=ac_c Tun da suka taho yake surfa mata bala'i yana cewa."Kin maidani abokinki ko?maiyasa ke wai bakya jin magana?wannan ai maitace da naci ance ba'a sonki ba'a bu atarki amma saboda rashin zuciya kin nace to komin maitarki wallahi nafi karfinki kuma dole wannan auren sai ya mutu ko kina so ko baki so sai na sakeki dan bani ra'ayinki a rayuwata nafi karfinki marar zuciya."Girgiza kai tayi tana cewa."Yaya Raihan kenan ya dace ace a yanzu ka fahimci cewa kai baka gabana kuma ba sonka nike ba,yanda baka sona nima bani sonka yanda baka bu ata ta a rayuwarka nima wallahi bani bu atarka."Dan shiru tayi tana maida numfashi tana mai cigaba da cewa."Wallahi Yaya Raihan da kan san yanda nike jin tsanar wannan auren a zuciyata da duk baka wahalar da kanka ba sai dai mai koda zan mutu wallahi ba zan ta a ce ma Abbie ban san aurenka ba dan kuwa iyayena sunfi karfin komai a wajena,nasha gaya maka kuma zan sake maimaita maka na saukar da farincikina ga iyayena na tabbata suna jindadi da farinciki sanadin wannan auren ni kuma zan zauna dakai a haka idan har zasu dauwama a farincikin."taune kasan le enshi yayi da karfi yana lumshe ido ya bu e yana cewa."Haka ai kika za a ko?"gya a kai tayi tana cewa."Eh."gangarawa yayi da mota gefe yayi parking yana mai cewa."Ni kuma nayi maki alkawarin zaki zauna cikin hukuba da bala'i nayi maki al awarin zaki mutu ba tare da kin san da in aure ba dan ke ban maki kallon mutum ina maki kallon wawiya dabba marar zuciya wanda bata san yancin kanta ba,in banda rashin sanin yancin kai wa yake yarda da auren dole bayan you have a right da zaki fadi ra'ayin kanki,to ni kuma a shirye nike da na ata ma kowa mudun zan are wannan ba in auren naki zan iya rabuwa da kowa,kowa ina nufin har Abbie indai zan rayu da za in raina."Waro ido waje Raihana tayi tana cewa."saboda soyayya har kake cewa zaka iya rabuwa da Abbie Yaya Raihan?"Daulah ce tayi murmushi tana cewa."Gashi kinji ai shi yasan daraja da martabar soyayya,keda kuwa baki san zafin so ba baki san maiye so ba saboda babu mashinshini ba wanda ya taya ganin zakiyi kwantai ki tsufa ki mutu babu aure shiyasa ai aka li a mashi ke kuma yace bayaso dan karya da cika baki kina wani cewa bakyaso ba wani munafunci ne da kina da wanda kike so da kauna kema ba zaki ta a bari a rabaku ba zaki za i za in ranki ne akan za in iyayenki to yake ba mashinshini ai dole ki nace kamar taska ance ba'a sonki ba'a bu atarki ba'a ra'ayinki amma kin nace bayan ba'a tillas a so tunda ba'a sonki ai sai ki hakura ko Madam?"Cikin masifa Raihana tace."Kinga baiwar Allah wa ya sako dake a maganar yan'uwa?da kike ta wani cika baki kina kumfar baki akan Yaya Raihan karki manta blood is thinker than water ni ko da aure ko ba aure ni dai dolenshi ce yar'uwarsa koda ban aureshi ba ina da yancin ha o kayana nayi rayuwa a gidan Yaya Raihan har sai sanda naso zan barshi ko shi wallahi bai isa ya hanani ba,ke kuwa fa?aure ne darajar aure ne idan yanzu yace ya sakeki ha a naki da naki zakiyi ki koma gidan father a cigaba da cin tuwo dan haka daga yau karki kuskura ina magana da Yayana kuma mijina kice zaki saka man baki fatan kina fahimta kwalkwarki bata kifi bace?"Ke Raihana Matar tawa kike gaya ma magana haka?dan ubanki ban gaya maki duk randa kika yi ma Matata rashin kunya sai naci ubanki ba?kuma karya tayi nace kayar tayi?idan da kina sa saurayi ba zaki ta a yarda a rabaku ba amma da yake baki da kowa anyi kwantai ai gashi kin makale man kuma kinzo inda ba'a bu atarki idan ke kin cika mai zuciya ba zuciyar kaza gareki ba kisa Abbie ya raba auren inbanda maita da ba in naci wannan wata irin masifa ce ga dama kina da ita kina da dama a hannunki amma kin nace to ba zan ta a sonki ba har abada dan haka tun wuri kin san abun yi idan har kuwa baki yi abinda nike so ba ni I'll show you my trues color." Key yayi ma motar yana mai cigaba da cewa."Dan wallahi Allah ba zan ta zama dake a gida ba ni ko kallonki bansan yi kinyi man zaune a gida kuma kice zakiyi ma matar gidan rashin kunya,daman ba kunya gareki ba kuma akan Daulah sai na karya ki dan akan Daulah zan iya atama kowa rai wallahi."Turo baki Raihana tayi can ciki tana cewa."Sai kace wata Daulah goal matar da ko kyau ma babu."Ta mirror ya hango bakinta na motsi tsaki yayi yana girgiza kai dan dole ne ma ya koya ma Raihana hankali rashin kunyar tata tayi yawa dolenta ko tana so ko bata so sai tayi respecting din Daulah dolenta,itama Daulah komai bata sake cewa ba jin su kawai take amma ita tasan takuncin da zata auka yarinyar ta lura da yarinyar ba kunya gareta ba kuma dole ne tabar gidan koda Raihan yana sonta sai tabar gidan balle ma da baya sonta zatayi maganin duk isakanci yarinyar rawar kanta yayi kuma ai ita taji mai take cewa kuma zata nuna mata a bata da kyau din ta anshe gida tayi bake-bake a zuciyar Raihan ta mallake ko ina ta hana ko wani space da zata samu ta shigo,ita kuwa Raihana a yanzu ta shirya daukar ko wani irin hukunci a wajen Raihan koda kuwa zai yankata amma ba zata ta aga matarshi afa ba, dole idan har matarshi ta shigar mata gona ta fiddota dan tafi arfin raini da cin zarafi a wajen Daulah ba zata lamunta ba karshe dai yace zai mur e mata kunne dan arshen muguntarshi kenan to idan ya tashi ya cire kunne nan ma duka ita dai abu aya ta sani bata raga ma Daulah...koda suka isa gida fitowa tayi tana niyar yin gaba cikin gida tana ko arin shiga room dinta Daulah ta sha ota daga baya tana cewa."Ke dan ubanki wa kike gaya ma magana?ni kawarki ce?koni kanwar uwarki ce da ta ubanki?"Waigowa Raihana tayi tana fisgewa daga rikon da Daulah tayi mata tana cewa."Ke din banza ke din wofi da har zakiyi jerking dina ke wacece ke zan iya karyaki idan har kika ce zaki ringa shiga gonata sai naci ubanki naci uban banza kuma ke baki da matsayin da zaki kasance kanwar Uwata dan kaf dangin Raihana Umar Sanda Tasan babu matsiyaci dukanmu ashin arzikine damu."Hannu Daulah ta kawo zata mari Raihana sai Raihana ta ri e tana mai faska mata marin take Daulah ta fasa ara dan wani irin ihu ta kurma har wasu taurari take ganin suna wurga mata da sauri ya shigo cikin parlon yana yin gun Daulah da ta ru e tana kewaye parlon tana cewa."Na bani na shiga ukku ta cire man ido ta cire man kunne ta kashe ni ta kasheni."baki aya Daulah ta gigice ta fita daga haiyacinta dan azabar da take ji, ji take kamar ma bata a duniyar,rikota Raihan yayi yana cewa."Babe lafiya maike faruwa?"Fa awa kawai tayi jikinshi tana rusa kuka tana cewa."Ta cire man kunne."kallon kunnen yayi sai kuma ya agota daga jikinshi yana cewa."Daina kuka ki gaya man maike faruwa."Daga mashi kai tayi tana cewa."Daga nace ma Raihana abinda take bata kyautawa rashin kunya ba inda zata kaita idan ma sonka take tazo ta baka hakuri ta nemi soyayyarka zamu zauna lafiya da ita amma yi ma babba rashin kunya ba tarbiya bane shi kenan kawai naji saukar maruka a fuskata nidai gaskiya ka sake ni gida zani ba zan iya zaman auren nan ba dan yarinyar nan kashe ni take neman yi." aga mashi hannu Daulah tayi tana kuka tana cewa."Wallahi ba zan zauna da wannan yarinyar a gidan nan ba ni ba zan iya ba dan kasheni zatayi watarana dan haka ni na hakura na bar mata kai ni kawai ka sawa e mani."Girgiza mata kai yayi yana cewa."Ba inda zaki Daulah kina nan tare dani ba mai rabamu sai mutuwa ita ka ai ce zata rabamu amma Raihana bata isa ta rabamu ba sai dai ita ta fita ta bar maki gidanki dan nan gidanki ne ba wanda ta isa ta takaki a gidanki ina da rai da lafiya ba wanda ya isa yace zai wula antaki ban taka shi ba."Da gudu ta shige room dinta tana kuka tana cewa."Nidai kawai ka sakeni ban iyawa wannan rayuwar ban iyata."Bayan Daulah yabi yana bata hakuri yana cewa."Karda kice zaki rabu dani idan kika ce zaki rabu dani Babe zan iya mutuwa,ba zan iya rayuwa babu ke ba nayi maki al awarin wannan ne last rashin kunyar da Raihana zatayi maki a gidan nan zan koya mata hankali."Kuka Daulah take tana ha a kayanta tana girgiza kai tana cewa."Nima ina sonka Babe ina kaunarka amma mafarkina na rayuwa da kai har abada ba zai tabbatu ba kaddarar auren da iyayenka sukayi maka ta gitta ta wargaza komai dan ba zan so nayi sanadin rabuwarka da iyayenka ba."Rumgumota yayi ta fisge tana durkushewa tana kuka,ru ewa Raihan yayi yama rasa ina zai saka kanshi dan shi bai iya lailashi ba kuma bai ta a shiga damuwa irin wannan ba dan kukanta jinshi yake har saman zuciyarsa haka yake jin zafin kukan nata,take idanunsa suke jajir suka kankance fita yayi daga dakin yana nufar dakin Raihana yana saka afa ya banka shi ya i bu ewa remote ya auka ya danna nan ma ya i bu ewa juyawa yayi yana bin wata hanya wani room ya shiga da ya gaji da kayan duniya wani waje ya ta a yana danna wani abu take kofa ta bu e ya shiga zaune ya taddata tsakiyar gado sai zufa take kawai ganinshi tayi kamar an jefoshi tashi tayi tana kuka tana cewa."Wallahi Yaya Raihan karya take ni ba abinda nayi mata itace ta takule ni da fa a fa." Fisgota yayi