← Book details Zabin Iyaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 145

Sashe 68

Zabin Iyaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Share pls
IN IYAYE*
_Parental choice_
*NA*
*JAMEEY*
*BOOK ONE*
_Bissimillahir Rahamanir rahim_
https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ?mode=ac_c
Kallonta yayi yana cewa."Wai ba magana nike maki ba Umaima"Kallonshi tayi sai kuma ta maida kanta bisa tv tana cewa."Ai kunne ke ji ko?"Kallonta kawai yake yama kasa koda matsawa wai shi Usman Umaima take ce ma Kunne ke ji ikon Allah, tabbas ya kai Umaima wuya samun waje yayi ya zauna yana Kallonta da kyau yana cewa."Umaima fushi kike da ni?daman ashe zaki iya yin fushi dani har kina gaya man magana haka?"Murmushi ta saki tana cewa."Akan mai zanyi fushi da kai Yaya Usman?ai a matsayina na karuwa yar'iska yarshayeshaye ban kai matsayin da zan yi fushi da kai ba Yaya Usman."dafe kanshi Usman yayi yana furzar da iskan bakinshi yama rasa mai zai ce mata, innalillahi wa'innalaihirajiun kawai yake nanatawa a zuciyarshi, Kallonta yayi dakyau yana cewa."Dan Allah Umaima kiyi hakuri kiyi hankuri komai ya wuce naji ni mai laifi ne amma kiyi hakuri maganar nan ta wuce karda ki
ara tadota har abada dan Allah."Ta
e baki tayi tana cewa."Ai hakuri ya zama dole tun da na dan lokaci ne kiris ya rage Yaya Usman ni ban damu ba dan ka kirani karuwa har na saba jin haka daga gareka kuma ni aurenka bai damaini ba idan har zaka aure duka matan duniya ba ruwana bai shafeni ba Yaya Usman kuma a haka ma kayi man hallaci da kara da har kayi hakuri ka zauna da karuwa mai shayeshaye naga ko
arinka kuma na jinjina maka dan zama da mai-najasa yar'kwaya marar tarbiyya jahadi ne kuma tabbas kayi jahadi sosai, ko yanzu a shirye nike da ka bani takardar saki ba zan ta
a blaming naka ba sai ma addu'a da zan maka da godiya dan ka bani tarbiyyar da iyayena da kuma yaiyena su gaza bani ka nu....Umaima."Usman ya dakatar da Umaima yana tashi tsaye cikin fa
a yake cewa."Wannan wani irin rashin wayau ne da har kike irin wannan maganganun bana ce maki komai ya wuce ba?hakuri fa nazo ina baki amma kike neman zagina to ni nace baki da tarbiya?idan har baki da tarbiya nima kenan banda ita tunda tarbiyya
aya aka bamu ko?."Itama Umaima tashi tayi tana cewa."Ba tarbiyya
aya aka bamu kowa da tarbiyyarshi kai dai an baka ni kuma nawa iyayen sun gaza bani dan haka ni bance daman ka wani bani hakuri tunda ba abinda kayi man."Girgiza kai yayi yana cewa."To naji a barshi da ban maki komai ba, maiyasa yau baki zo akayi karatu ba?bayan kin san karatun naki yana da matu
ar amfani ko?."Komawa tayi ta zauna tana cewa."Na hutar da kai wanda kayi man a baya Allah ya saka da alheri."Kallonta kawai yake yana mamaki ashe haka daman take bata iya fushi ba? laifi tabbas yayi kuma ya yarda da laifinshi sai ta hakura tunda yazo bada hakuri hakanan kawai yake jin zuciyarsa babu dadi akan fushin nata ya saka kanshi a damuwa sosai bai son
acin ran Umaima bai san dalili ba amma bai son yaga ko ka
an ta chanza fuska yana kasancewa a cikin damuwa, murmushi yayi yana matsawa gabanta ka
an yana koma hannunta yana murzawa a hankali yana cewa."Haba yar'kanwata haba Umaimata nine fa Yaya Usman dinki kina son na shiga damuwa idan har baki bar fushin nan ban iya cin abinci kina son yunwa ta kashe maki ni?kuma ai ba kyau mutum yayi ma kanshi
arin karatu duk ai nine ko?to ba zan sake ba nidai ayi hakuri na tuba a bar wannan fushin haka nan kinji kanwata kefa yanzu Kawata ce ba yanda za'ayi kawa tayi fushi da abokinta ko?."Zare hannunta tayi daga ri
on da yayi mata tana goge hannuta a jikin sofa tana cewa."Ya wuce amma dan Allah Yaya Usman ka kiyaye ta
a ni dan ban san goga maka najasa."tana gama fa
in haka tabar mashi parlon dan bala'in haushinshi take ji har cikin zuciyarta ji take kamar ta yanke hannun da ya ta
a mata akan mai zai ta
a ta bayan yasan ita najasa ce a jikinta?shine fa ya gaya mata yafi karfin ta
a najasa saboda ta shigo gidanshi ta kofar gaba bai shiga ta kofar gaba sai ta baya dan duk kadda ya ta
a najasa ai yanzun ya fara gani ba ruwanta da shi ya kawo amaryar tashi yayi rayuwarshi da ita ya saketa ta koma gidansu tayi rayuwarta daman ai yana yawan gaya mata zai sake ta to Allah ya kawo Dada zata gaya ma Dada bata bukatar zama da Usman a yanzu ta saka ya saketa daman ai ita taji zata iya zama dashi to yanzu ta fasa.

Tunda ta shige room dinta Usman bai motsa daga inda yake tsaye ba dan duk jikinshi yayi sanyi sosai akan kalaman da Umaima tayi mashi sai yau yake jin nadamar duk abubuwan da yayi mata to amma maiye na
in hakuri tunda ya bata hakuri?ai Allah yana tare da maiyin hakuri koda yake harda rashin sani shiyasa har ta
i hakura da ya bata hakurin amma yanzu shi ba zai sake bata hakuri ba da tayi hakuri da Karda tayi hakuri shi ba ruwan shi ai ya bata ya fita hak
inta ya bata hakuri da take kuma maganar saki daman ai zai saketa amma bata isa ta saka shi ya saketa lokacin da shi Usman bai yi niya ba wannan ne bata isa ba kuma tunda abun nata ya zama iskanci da rainin wayau zai bita a yanda ta koma shi da ita wa zai fasa,abinda ya sani dai karatu dole ya koya mata ko tana so ko bata so sai ya ida niyar da ya dauka kanta na koya mata karatu dolenta tabi duk abinda yake so kuma shima ai hakuri yayi da rintse ido da har ya iya kama mata hannu kuma ai baiyi karya ba najasar take yawo da ita a da a yanzu ne bata da najasa a jikinta tunda ya koya mata wankan tsarki ba, tsaki yayi yana tashi ya haye sama dan samun bacci dan anjima akwai islamiyya tunda weekend ne kuma idan har tace zata cigaba da yi mashi wannan haukan a gaban amaryarshi zai
ata mata rai ne dan ba zai
auki raini ba kuma ba zai yarda ta ja mashi raini a wajen amarya ba,idan har ba tashi tsaye yayi ba sai ta
ata mashi tarbiyyar amarya ta koya mata rashin kunya ya samu Allah ya ha
ashi da ustaziya kamila wanda ba ruwanta bata damuwa da duk shirmen duniya ba, lahira kawai take nema tsab Umaima zata
atata dan ma Allah yaso shi ya kulle duk wata hanyar da za'a kawo mashi she
anu a cikin gida, wanka yayo ya samu ya kwanta dan damuwar da Umaima ta saka mashi ta janyo mashi ciwon kai har bacci ya kwashe Usman yana mamakin yanda Umaima ta iya Kallonshi tana mashi tsiwa.
Chapter 68 · 0% Book details