← Book details Zabin Iyaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 145

Sashe 77

Zabin Iyaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Share pls
IN IYAYE*
_Parental choice_
*NA*
*JAMEEY*
*BOOK ONE*
_Bissimillahir Rahamanir rahim_
https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ?mode=ac_c
Kallon Mama Dada tayi tana kallon Umaima tana tafa hannaye tana cewa."Kinga ko Nafisa?Kinga halin maza ko?maza ba tabbas yanzun shi Usman dan wula
anci da rashin mutunci bai gaya maki zai yi aure ba Uwata?wanann wani irin cin amanane haka?"Ta
e baki Umaima tayi tana cewa."Wai auren da Yaya Usman zaiyi Dada?ai idan shine ya gaya man tuni to ni ina ruwana da aurenshi a kaina za'a ajiye matar ko mai?nasani yau da zai tafi wajen daurin auren har ceman yayi shi ya tafi nace a gayas ina ruwana da aurenshi iyaka mata tayi man hauka na zubda mata hakoran gaba."Cike mamaki Dada take kallon Umaima dan kuwa Umaima ta bata mamaki bata yi tunanin haka ba tasa zata zo ta tadda Umaima tana hauka da birgima akan za'ayi mata kishiya kuma hakan da tayi yayi mata daidai da tazo ta tada hankalinta kuma auren dai ba fasawa zai yi ba gwanma ta kwantar da hankalinta ta barshi da
arin aurenshi ya
arata murmushi Dada ta saki tana cewa."Yauwa Uwata uwar da tafi ta kowa kin kyauta kuma kin huta ma kanki da ba ki saka ma kanki damuwa ba har kizo ki kamu da wata cutar a banza dan haka ba ruwanki da ita adai gaisa karda ki zura jiki nesanesa dai ba fada ba kallon banza ina kwana ina wuni ta rabaku bance ki kauce mata cikinki tasan sirrinki tasan halin da kike ciki da mijinki ba,ban yarda da haka ba kiyi zurfin ciki akan sirrinki karena bani baka tuwo na bani korarka haka zata kasance a tsakaninku ai babu wata damuwa a tsakaninki da Usman ko?"Daga kai tayi tana cewa."Babu Dada ni mai ma zai ha
ani dashi kowa yana rayuwarsa."Dan jim Dada tayi tana kallon Umaima tana kallon Nafisa sai kuma ta furzar da naunauyen numfashi tana cewa."Mai kike nufi Uwata?har yanzu kina nufin Usman bai nemi hak
in shi a wajenki ba?".

Girgiza kai tayi tana cewa."Ya ansa mana tuni Dada nufina bai da yahaniyar da har za'a samu damuwa dashi, mutumin da yake fita Office weekend kuma yana isilamiya taya za'a samu damuwa Dada."Sauke numfashi mai karfi Dada tayi tana jin natsuwa na shigarta tana cewa.'To Alhmdulillahi nagane yanzun ki sake kiyayewa Umaima kuma ki zauna da kowa lafiya."Gya
a Umaima tayi tana cewa."In shaa Allah Dada."Dan jim tayi tana cigaba da cewa."Wallahi Dada ban damu da auren Yaya Usman ba ni fa damuwa ta a duniyar nan
aya ce naga na ida sauka na kuma haddace Alqur'ani mai girma shine kawai damuwata kuma Alhmdulh a yanzun haka ina izufi arba'in da biyar ka
an ya rage man na sauke na kuma san litattafan addini Alhmdulh ba laifi ai ko a haka na tsaya na
aru sosai da Yaya Usman akan mai zan
aga hankalina dan kawai zai yi aure?yayi aurenshi Allah ya bamu zaman lafiya shine kawai fatan ba wai rigima ba da tada jijiyoyin wuya."Murmushi Mama Nafisa tayi yana cewa."Kai alhmdulh a gaskiya Umaima kin burgeni kuma Kinyi hankali da hangen nesa kuma ke
in mace ta gari ce Allah yayi maku albarka ya kuma baku zaman lafiya dan kuwa tashin hankalin ba abinda zai kawo sai
acin rai kuma aure ba fasawa za'ayi ba,dan idan har namiji yayi niyar aure ba abinda ke dakatar dashi sai mutuwa ko kuma idan wanda zai aure dine tace ta fasa amma fa masifar uwargida da bala'inta duk ba zai saka a fasa ba sai ma zubewar
iyamarki a wajen miji dan haka ki kauda kanki kiji baki ji ba ki gani baki gani ba shine ribar iya zaman auren idan har akayi maka kishiya kinji Umaima?."
aga kai Umaima tayi tana mai nuna masu wani channel da ake koya dubarun zama da kishiya ba boka ba Malam da kuma dubarun zama da miji ba tare da tashin hankali ba tace duk tana nan take daukar lesson kuma tana
aruwa sosai...la'asar nayi bayan su Dada sunyi sallah dan ita Umaima bayi take ba tana hutu
ara hawa sama sukayi suka gyarashi yanda ya kamata suka baza kamshi iya kamshi dan wani irin turaren wuta ne Momy ta aiko ma Umaima mai girman kamshi da sanyaya zuciya banda humrah da turaruka masu kyau da tsada tun bu
esu suka turnu
e kasa da ruwan kamshi dan ka
an aka turara sama dashi dan ittace biyu ne amma sai da ko ina ya dauki haramin kamshi bayan sun gama wanka Umaima ta sake yi tana zama bakin mirror ta tsara kwalliya ta ban girma daman ita ce Umaima gwanar adoce da iya kwalliya wata chiganvy popolin golden ta dauko light-green da ratsin touching din ash dark da ita su Dada suka zo dan akwati
aya ne babba da sabin kaya dinkuna kala daban daban tun daga kan laces atamfa shadda liffaya Momy ta hado mata kuma ko wane dinki na zamani ne mai kama jiki ka
an da fiddo zallar kyau dan Momy tana sane tasa aka yi mata masu kama jiki yanda zasu fiddo mata da surarta ta
ara daukar hankalin Usman har yaji itama tana da matsayin da har yafi na wanda ya za
a da kanshi a zuciyarshi..sosai kuma atamfar tayi ma Umaima kyau daman abunka da mai kyau sai kyaun ya
ara da
uwa
aura dankwali tayi V-shape mai step sannan ta dauko wani babban gyale santali ta yana sosai ta fito sakawa tayi Momy nafisa tayi mata hotona tace a tura ma Momynta ta ganta haka kuwa akayi an tura ma Momy kamar yanda ta bukata, bayan shiryawar Umaima ba da jimawa ba yan kawo amarya suka baiyana duk da ba wani kwasar mutune akayi ba anyi komai na gayu dan duka yan kawo amaryar basu wuce shidda ba duk da amaryar sun kama bakwai daga kanwar mamarta da yayar mamarta sai kanwar babanta da yayar babanta sai babbar kawar amarya da kanwar amarya su kenan suka zo da gu
a suka shigo sai da aka tsaya amarya tayi addu'a sannan suka shigo da sallama Umaima na tsaye taba kofa baya tana danna remote dan chanza channel daga karatu zuwa wa'azi dan karda ana karatu ana surutu,su Dada ne suka tarbi amarya hannu biyubiyu suna yin sama da ita har dakin da Umaima ta nuna masu tace nan ne dakin amaryar har gado suka ajiyeta Dada na cewa."Maraba lale maraba da zuwa amarya yar kamshi."Murmushi duk sukayi sannu ta sake yi masu suna fita,hawowa sukayi da manyan flask da yake sha
e da Masa
ayan kuma roman kan shanune
ayan kuma pepper chicken ne mai rai da motsi sai
ayan flask din Alale ne da yaji kwai da hanta a ciki haka aka jaresu a gabansu aka kawo plates da spoon sai bottle din ruwa da lemu, numfasawa Momy nafisa tayi tana cewa."To bayin Allah ga abinci nan aci idan kun gama mun dawo maku gabatar da kai ko?"Jinjina kai sukayi suna yin godiya sannan suka fita.

Bayan sun fita Zully ce ta yaye mayafin fuskar Malika tana cewa."To ai kin cire wannan wahalar ko?ko takura maki baki jin yayi."Ta
e baki Malika tayi tana cewa."Bari kawai Zully wai baki ga Umaima ba?baki ga yanda ta chanza ba?"kama baki Zully tayi tana cewa."Anya Umaima ta fara yi maki gezo tayi ba Malika?to ai ni tunda muka shigo gidan nan banga wata Umaima ba wannan tsohuwar da dattijuwar nan kawai nike gani suna shige da fice ai dan su suka tarbemu."Murmushi Malika tayi yana juya bottle din ruwan da ke hannunta tana sauke numfashi tace."Ni kuma sam basu na fara gani ba,Umaimata na fara gani tayi kyau ta
ara cika ta kara zama mace sai dai kash duk wannan kayan duniyar
aton banza yake morarsu wallahi Zully ina jin ban iya jurewa ina jin kishin Umaima na iya fisgata na kashe Usman ba tare da na shirya ba mudun naga zai shiga dakin Umaima ke ko ta
a hannunta yayi ina jin zan iya kashe shi zuciyata zafi take man Zully."Kamota Zully tayi tana dan shafa bayanta ka
an tana cewa."Yanda kika tsara haka zaki karasa Malika daurewa zakiyi ki danne kishinki har sai kin cinma burinki idan har kika ce zaki kashe Usman taya zaki samu shakuwa da Umaima har ta kaiku ga aure? wannan fa babbar dama ce da zaki nuna ma Umaima so da kaunar da ko shi Usman bai nuna mata ba,babbar dama ce da zaki banbance mata dadin less dan na tabbata idan har kikayi mata abubuwan da zasu gigita mata
walwa dan dadi zata soki ta kauna ceki kuyi rayuwa har abada dan haka saki fuskarki mu bar maganar nan muci abinci mu ana yin Sallah zamu tafi."Jinjina kai Malika tayi tana share hawayen da suka zubo mata daman duk matan da suka kawota abokan iskancinta ne shawara suka bata sosai yanda zata janyo Umaima jiki ta nuna mata so da kauna sosai kuma take gamsuwa da shawararsu suna
ara mata kwarin gwiwar soyyaya da Umaima.
Chapter 77 · 0% Book details