← Book details Zabin Iyaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 137 OF 145

Sashe 137

Zabin Iyaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kasa zama da natsuwa Hamad yayi tunda Usman ya gaya mashi sakin da yayi ma Umaima bai sake gane mai ke damunshi ba saboda zuciyarshi tana mashi zafi da ra
adin sakin da yayi ma Umaima,dan shi ya tabbata duk da ba'a shedar mutum amma ya tabbatar da Umaima ba zata ta
a neman Malika ba dan Umaima tana da hankali da natsuwa abarshi baya Umaima tayi yawace yawacenta na zuwa club da shayeshaye hakan bai zai sa a kirata da sunan Karuwa ko yar'iska ba yana mamakin maike damun Usman yana mamakin abunda ke damun Usman da har yanzu ya saka natsuwa ya gane cewa wacece Umaima maiye zatayi da wanda ba zatayi ba duk da iska baya kama ba'a gane dan'iska a fuska balle kace wannan dan iskane,amma yanayin Umaima zaka kalla ka gane cewa Umaima ba yar'iska bace Umaima bata iya karya ba daidai da magana ma Umaima bayi take ba,yaushe ma Umaima ta fara magana?shi har mamaki yake idan Usman na cewa Umaima tayi mashi kaza duba da bata shiga sabgar kowa bata shiga hul
ar kowa abun na bala'in bashi mamaki idan yace Umaima tayi kaza,ita dai Umaima barta daga zuwa club sai zuwa club,Usman yayi wasa da damarsa sosai damar da har ya mutu ba zai daina nadama ba
aya ce bai amfani da damarshi ba Allah ya bashi dama ya saka ma Umaima son Usman,maimakon Usman yayi amfani da zallar son da take mashi ya juyata yanda ya so suyi zaman aure na har abada cike da soyayya da kaunar juna,amma Usman hankalinshi bai kai ga yayi haka ba ya zauna yana ta shirmen banza da wofi wai shi ustaz,ustaz ta ina?ta ina Usman ya zama ustaz bayan ilimin shi ya zama na banza kuma yana ta wani cika baki akan Malika ustaziya mahaddaciyar Alkur'ani kamila,to ai Malikar da yake cika baki kanta ya tabbata har ga Allah tunda Umaima tace Malika ta nemata tabbas malika ta nemata kuma Umaima tayi mashi dai-dai da tayi ma Malika dukan mutuwa dukan kawo wu
a hakan da tayi daidai ita Malika idan ta tashi gobe ta sake haye Umaima kuma bai ma Usman fata bai mashi mugun baki a matsayinshi na babban abokinsa,amma Usman zaiyi nadama ta har abada na sakin Umaima da yayi kuma zaiyi nadama lokacin da Umaima tayi mashi nisa dan a juri zuwa rafi watarana tulun zai fashe,ba baki yayi ba amma ya tabbata komin daren da
ewa gaskiya zatayi halinta kuma yana fata Usman ya gane cewa wacece Malika duk da shi bai ta
a zargin Malika da aikata wani abu duba da yanda Usman ce tarbiyyarta hankalinta natsuwarta kamallarta ba mai Kallonta yace mata yar'iska amma mai ba'a shedar mutum dan ba zuciya bata da
ashi,ba zuciyar da shedan baya shiga yakwa
aita ma mutum aikata wani abun na asshe sai wanda Allah ya tsare ya kuma tsarar da aikata haka,da
a kuma zata iya aikata abinda Umaima tace wata ila tana budurwar zuciya da har shedan zai raya mata sha'awar Umaima dan Umaima mai kyau ce tana da sura da kyau ba abinda Allah ya ragi Umaima dashi dan kallo
aya zakayi ma Umaima kaji kana sonta amma Allah shi yasan gaibu shi yasan gaskiya Allah shi baiyana gaskiya, furzar da numfashi yayi mai nauyi yana ha
a kayanshi dan tashi zai yi ya tafi gida zaman office din ya fice mashi daga rai baki daya duba da abinda Usman yayi.

Tunda suka je exclusive mall Umaima take daukar manyan abaja masu kyau da tsada dan Umaima ta dauki abaya kama daga Dubai Saudiya da ejif da kuma babbar waya da ta
auka iPhone16promax sai kuma veils medium size ,saboda tana son saka veil dan ta duba taga saka veil ba laifi bane, dan wai mace na saka veil ba shi yake nuna ita yar'iska bace kamar yanda Yaya Usman yake cewa a'a,abinda ake so
aya ne tsoron Allah kuma mace ta kama mutuncin kanta a matsayinta na mace ta kuma kulle tsiraicinta dan babu kyau fitar da tsirarci amma dan ka saka veil ka fita babu zunubi a ciki kuma ai tsoron Allah a zuci yake, harda hijab ma masu kyau suma ta
auka dan zata ringa mix idan tana ra'ayi inzata fita ta saka veil idan kuma hijab din ne shima ta saka har da himar masu kyau yan sudan duk ta dauko,dan ita ta tuba har ga Allah ta tuba akan rayuwar da tayi a baya kuma tubanta ba zai hanata saka veil ba ko himar imani a zuci yake kuma Allah yana ansar tuban bayinsa dan Allah gafurul-rahim ne kuma tana kyautata zaton Allah ya anshi tubanta,maida Kallonta wajen Umma tayi tana cewa."Umma ni yanzu abunda nike son kiyi man
aya ne isilamiya nike son shiga ban san na zauna babu tilawar karatu kuma na kusa saukewa dan saura ka
an na sauke Allah ya kawo wannan abun."Kallonta Umma tayi tana murmushi tana cewa."Allah sarki Umaima Allah yayi maku albarka kuma Allah ya saka maki akan abinda Usman yayi maki,ni na haifi Usman ba zan mashi baki ba amma tabbas sai Allah ya saka maki tun a duniya akan abinda yayi maki,dan kuwa ina jin ba
inciki ina jin ba dadi ina jin zafi da
aci gami da ra
adi a zuciyata akan abinda Usman yayi maki kuma tabbas Usman yayi asarar mata ya rasa mace ta gari ni na hango abinda na hango a tattare dake shiyasa na taya Usman murna da farincki da ya aureki amma ba komai Allah ya baki miji nagari wanda zai share maki hawayenki ya tarairayeki ya kula dake tamkar tsoka
aya a miya ko kuma nace kwai,in shaa Allah za'a saka ki isilamiya kuma Allah shike da shiriya Umaima naji dadin shiriyar da kikayi Umaima Allah ya yafe mana baki
aya, kuma ni Umaima na tabbata duk abunda kike fadi gaskiya ne ba zaki ta
a yi ma Malika karya ba,amma abinda zamu ce Allah ya shiryeta ya nuna mata gaskiya ta bar
azantar da take tun Allah baiyi fushi da ita ba,kuma Allah ya kubutar da Usman daga kai
inta dan yanzu
addarar Usman kenan zama da mace irin Malika dan ni daman can hankalina bai kwanta da Malika ba ina jin a jikina kamar ba alkhari bace a rayuwar Usman."Gya
a kai Umaima tayi tana sauke naunauyen numfashi tana dan yin jum ta kalli Umma tana sakin murmushi tace."Allah sarki Umma ai ni tuni na yafe ma Yaya Usman na yafe mashi komai yayi man,Yaya Usman dan'uwana ne jini
aya muke na yafe mashi komai yayi man nidai fatana Allah ya kubutar dashi daga kai
in Malika zamu cigaba da yi mashi addu'a kuma Allah ya yafe mana baki
aya itama Malika din zamuyi mata addu'a Allah ya shiryeta ya nuna mata gaskiya gaskiya ce ta tuba ta daina abinda take."Shiru tayi tana girgiza kai tana cigaba da cewa."Malika ta cuci kanta Umma Allah yayi ma Malika baiwar ilimi gata da hankali hafiza ce kamar yanda Yaya Usman yace kamila ce sai dai kash duk a fuska take kamila hafiza amma zuciyar ta ba
irin take babu tsoron Allah a cikinta dan gaskiya zuwan ta gidanmu na
aru da abubuwan da suka shafi addini da yawa a wajenta amma duk a wanann sanin ya tashi a banza tunda bata amfani da sanin kyaun
an maciji,idan Malika tana man karatu sai naji inama ace nice dan Allah ya bata baiwar karatu ga sani bata amfani da sani Allah karka bamu ilimin da ba zamuyi amfani da shi ba."Girgiza kai Umma tayi ta numfasa tana cewa."Amin ya Allah ai daman wasu basu aiki da ilimi gasu da tarin sani amma basu amfani da sanin,kiga suna amfani da rigar ilimi suna aikata
arna bakiji ana cewa ba kayi amfani da abinda mallan ya gaya maka karkayi amfani da abinda mallan yake?to Malika kalarsu ne gata dai Malama ta sani tasan abinda take aikatawa masifa ne Allah baya so amma take aikatawa,shi kuma galhomaho sakaran banza ana son a nuna mashi wacece matarsa yake ya fahimta,Usman Allah da ban kai zuciyata nesa ba da da tuni na tsine ma Usman."Girgiza kai Umaima tayi tana cewa."A'a Umma tsinuwa ba masalaha bace kamar yanda Baba yace addu'ar dai ce za'ayi Allah ya ganar dashi wacece matarshi,dan ba'a son iyaye suna yawan tsinuwa ga
ansu addu'a dai ce gaba, Umma hausawa na cewa Allah yayi albarka idan tayi yawa ya aka
are balle Allah ya tsine, addu'ar dai itace dan Allah inason duk komai ya wuce ku fidda komai a zuciyarku ku maida komai kamar ba'a yi ba Yaya Usman dai ya sake ni kuma wallahi bakomai ni na dauki hakan a matsayin jarabawa kuma
addararta Allah ya bani ikon cinye wa."Amin Umaima in shaa Allahu yanzu akwai wata isilamiya a cikin estate dinmu sai kiyi register ki cigaba da zuwa."murmushi Umaima tayi tana cewa."Alhmdulh kinga ma kuwa."
aga kai Umma tayi tana cewa.'Eh kusa ne idan ma mota kike son zuwa ba damuwa dan bai wuce gida biyar zuwa shidda zaki wuce sai isilamiyar ba."To Umma suna yin hadda ne?dan ina son na haddace Alkur'ani mai girma."Jinjina kai Umma tayi tana cewa."Da ma haddar ce zalla daga baya aka ha
a da normal karatu."Godiya Umaima tayi tana jindadin samun isilamiya mafi kusa da gida..koda suka koma gida apartment din Dada ta sauka ta jera kayanta a room dinta har da wanda aka kwaso mata a gidan Usman gyara komai tayi tana yin wanka taci ta ha
a wayarta tana setting din komai yanda ya dace amma koda ta bu
e tiktok bata wani bibiyi shirmen da ake a tiktok din ba malamai kawai tayi following dan karu da addini dan yanzu mafarkin Umaima
aya ne ta zama babbar malama wadda har channel zata bu
e tanayin wa'azi kuma akan mata kawai ya ma zaki yi rayuwarki mai ya dace kiyi wane miji ma ya dace ace kin aura mafarkinta kenan kuma tana san in shaa Allah Abbanta zai goya mata baya...
Chapter 137 · 0% Book details