← Book details Zabin Iyaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 145

Sashe 7

Zabin Iyaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Allah yasa lafiya dai?."Murmushi yayi yana cewa."lafiya lau Alhmdulillahi danma karda na kawo maka Iv ai da tare da IV ma zanzo sai naga ai ga uban a bari dai nazo na sanar dashi baki da baki."Wani irin kallo Oba yayi mashi yana cewa."Kamar ya IV Umar?Raihan din za'ayi ma aure ban sani ba?."murmusawa yayi yana cewa."Kwarai kuwa ai gashi nazo na gaya maka nan da sati biyu masu zuwa za'a aura auren Raihan Umar Fatah da amaryar Raihana Umar Sanda in shaa Allah."Duhu-duhu Raihan ya fara gani ga wani irin nauyi da zuciyarshi tayi mashi take shigowar shi kenan yaji wanann tashin hankalin dan mutuwar tsaye kawai yayi bai san ma trolly din hannunshi ta fadi ba,sai dai kawai ji yayi an kama hannunshi a karasa dashi kusa da Oba an zaunar dashi da yal ya alo murmushi yana cewa."Thank you Uncle Salisu."Murmushi Jigida ya sakar mashi kawai yana cewa."Kana hanya kenan?." aga kai kawai yayi yana maida Kallonshi wajen Oba yana cewa."Daddy barka da yau."murmushi Oba yayi yana cewa."Barka dai Son ya gajiyar hanya kamar ba'a Flight kazo ba?."Daga kai yayi yana cewa."Eh da moto nazo kuma zanyi ma kwana biyu dan ina son hutu."maida Kallonshi yayi wajen Mr president yana cewa."Ina wuni Abbie?."Cikin fa a Mr president yace."Yaushe ka raina ni Raihan?Yaushe na zama abokin wasanka?bance maka zuwana daban naka daban ba?.maida kanshi asa Raihan yayi ba tare da yace komai ba,cikin acin rai Mr president ya taso zai mari Raihan da Sauri Oba Umar ya tare yana cewa."Haba mana Calmdown Mr president duk mai yayi zafi haka?har sai yaushe zaka rage zafin zuciya irin haka?."kallon Oba Mr president yayi yana cewa."Naso ka barni na koya ma wannan yaron hankali na rasa gane mai ke damun Raihan wallahi okay na gane kuma zan koya maka hankali."Zaunar dashi Oba yayi yana cewa."Dan Allah duk wannan ya wuce kai Raihan bashi hakuri." agowa Raihan yayi yana matsawa gaban Mr president yana cewa."Yi hakuri Abbie wallahi ba zan sake ba kuskure ne aka samu am so sorry."Tsaki kawai Mr president yayi yana cewa."Naji matsa a gabana tunda ba haihuwarka zanyi ba to."ja baya Raihan yayi duk zuciyarshi bata yi mashi dadi yama rasa damai zaiji da auren dolen da suke ko arin yi mashi ko kuwa da fa an Abbie? maganar Oba ce ta maido shi hankalinshi, murmushi ya saki yana gyara zamanshi cike da ladabi tana cewa."Allah ya taimakeka duk yanda kukayi aya ne a wajena nasan ba zaku za aman abinda zai cutar dani ba,sai dai i... aga hannu Mr president yayi yana dakatar da Raihan yana cewa."Sai dai mai Raihan?bani son naji komai daga bakinka inba na yaushe ne daurin aurenka da Raihana ba."Girgiza kai Oba yayi yana cewa."Nan fa aya ba zan yarda da wannan tsananin ba gaskiya Mr president ya zaka hana yaro magana?bayan yana da abun fa a kai Raihan fadi ina saurarenka sai dai mai kenan?."Lumshe ido Raihan yayi yana bu ewa ya kalli Ubaidu yana maida kallonshi wajen Oba yana cewa."Dad ban san da tsarinku na ha a aurena da Raihana ba da ban fara neman aure ba,amma tunda har kuka yanke wanann hukuncin na ha ani da Raihana ita yarinyar zan bata hakuri akan tayi hakuri kawai duk da Allah ya sani banje da sunan yaudara ba duba da gidan da na fito gidan mutunci ba zanso ace ni Raihan Umar Fatah Umar nazo da yaudara ba to ai ba yanda zamuyi haka Allah yaso." Kallon Raihan Mr president yayi yana cewa."Ai wannan zancen banza ne Raihan har yaushe ka dawo kasar da har ka fara kula wata yarinya wannan halin naka ma zai barka ka kula wata Raihan?."Girgiza kai yayi yana cewa."Ba haka bane Abbie muna tare tun Mascow a can tayi B.S.C dinta Abbie."Har Mr president zaiyi magana Oba ya dakatar da shi yana cewa."Ai ba damuwa bane Raihan kai fa mijin mace hudu ne idan har ka koma Abuja kaje kayi magana da ita yarinyar idan har zata iya zuwa a ta biyu a gidanka ai ba damuwa bane bayan aurenka da Raihana kamar da sati biyu zuwa uku sai ayi da ita yarinyar sai naga kamar haka zaifi kaima ba'a tauye maka hak i ba."Kallon Oba Mr president yayi yana cewa."Amma ita Raihana anyi mata adalci ka san adadin masu zuwa neman aurenta da nike hanasu duk saboda Raihan sai ayi mata haka?kuka sani ko itama tana da wanda suke soyayya da shi?to idan har haka ne ba zan bashi ata Raihana ba yaje ya auri *ZA IN RANSHI* itama a barta ta auri *ZA INTA* wannan shine adalci."Cikin son kwantar mashi da hankali Ubaidu yace."Yaya dan Allah abi komai a sannu ayi mashi uzurin auren wanda yace sai ya auresu duka na tabbata Raihan zai kasance mai adalci a garesu balle kuma Raihana da take yar'uwarsa na tabbata zai kula da ita ba zai ta a sata hawaye ba."Kallon Ubaidu Mr president yayi yana cewa."Kema kenan ka goyi da bayan ayi ma Raihana kishiya bayan aurenta da sati biyu Ubaidullahi?."Maida kanshi asa Ubaidu yayi yana cewa."To Yaya ai da a aura mata bare ai gwanma dan gida na tabbata ba zai ta a zama silar zubar hawayenta ba sai dai ya zama silar farincikinta tunda kanwarsa ce kuma itama zata iya zama dashi tunda tasan halinshi Yaya."komai dai Mr president baice ba dan shi sam hankalinshi bai kwanta a lamarin ba ganin sun rinjaye shi kawai ya yarda amma fuskarsa ta kasa boye nuna rashin jindadin haka,bayan an gama maganar Raihan aka kum dawo ya Rahina za'a ha ata da Rayyan Umar Sanda duk za'ayi bakin rana aya,tashi Raihan yayi yana nufar apartment din Rayyan jiki duk sake dan tun da uwar da ta haifeshi ya girma ya kuma yi hankali bai ta a ganin bakar rana irin ta yau ba,bai ta a yin mugun ji irin na yau ba bai ta a yin da na sanin ta a Raihana ba sai yanzun dan ya tabbata kukan da ya sakata yau yasa Abbie yanke wannan ba in hukuncin irin wannan wanda zaizo daga baya kuma azo ana Allah wallahi dan shi ya sani har abada ba zai ta a son Raihana ba kuma ba zai ta a yi mata kallon mata ba kuma mafi girman kuskuren da su Abbie zasu yi a rayuwarsu shine su aura mashi aure da Raihana dan ya tabbata su duka sai sun zubda hawayen ba in ciki dan bai son Raihana bai kaunar ko ganin Raihana a rayuwarshi kuma wallahi ba zai zauna da wanda baya kaunar gani ba kuma shi ba zaice bai so ba kodan Oba da yake ganin mutuncinshi,amma zai samu Ubaidu bayan sun koma abuja ya gaya mashi bai son Raihana ya gaya ma Abbie dan kowa masalaha da farinckin iyayensu suka gina tun kan asan za'a haifesu shi da Raihana din shine fasa auren a haka ya shiga apartment room din shi ya shiga wanda ya watsa ruwa ya sake kaya yana zama bakin beside bed yana auna yanda zai kubuta daga auren Raihana dan ji yake kodai ya ha a nashi ya nashi ya koma Abuja ya dauki Daulah suje wani waje a daura masu aure suyi rayuwarsu cikin aminci da kaunar juna inyaso sun dawo bayan wasu shekaru lokacin Abbie ya huce,shigowar Rayyan room din ya dakatar dashi daga neman masalaha Kallonshi Rayyan yayi yana cewa "Broth daga angaren Abbie nike sun gayaman nan da two weeks ne bikinmu wani shiri to ya dace muyi?."Kallonshi Raihan yayi sai kuma ya saki murmushi dan ko ba komai ganin Rayyan a kusa dashi ya an rage mashi ra in da yake ji a cikin zuciyarshi dan Rayyan yana aya daga cikin mutune masu mahimmanci a rayuwarsa bai da amini ko abokin fira bayan Rayyan da Uncl Ubaidu dan bai cika ma zama da Abbie ba koda sun zauna sun fara magana to da fada zasu rabu,kamo hannun Rayyan yayi yana cewa."Broth kana son Rahina ne ko kuwa dai zaka anshi *ZA IN IYAYENKA* dan kawai baka iya bujure ma umurninsu?."Dan shiru Rayyan yayi sai kuma ya numfasa yana cewa."Ban sani ba ko inasonta ko banso kawai dai banjin haushinta a raina kuma koda ban sonta zan zauna da ita inkula da ita inkyautata mata saboda ita din *ZA IN IYAYENA CE* saboda na tabbata ba zasu ta a cutar dani ba kuma na tabbata sunyi wannan ha in dan farincikina."Shiru Raihan yayi sai kuma ya gya a kai yana cewa."Fine haka ne fa."Da yake shima Rayyan din ba magana ya cika ba dan a wani wajen ma Raihan yafi shi yin magana duba da shi Rayyan jinin sarauta ne yake yawo a jikinshi jinin sarautarta ma na Okeke yana son tambayar Raihan ko yana son Raihana kawai ya fasa dan kuwa maganar da yayi yanzun ma nema saka mashi ciwon kai ma tayi kwanciya kawai yayi yana cewa."Yau a kusa da Broth xan kwana because I really missing you Broth."murmushi kawai Raihan yayi dan yasan daman ai a room din shi zoa kwana dan sun kusa 6month basu hadu ba tun wani visiting da shi Rayyan din da Oba suka kai mashi mascow ai an dade tashi yayi ya koma parlo dan yana son yin waya da Daulah su shawo maganin matsalar su tun cikin daren ba sai gobe ba kuma bai son disturbing din Rayyan shiyasa ya fita zama yayi yana dealing din number Daulah cike da damuwa a zuciyarshi dan bai san yayi bala'in kamuwa da son Daulah ba sai da maganar aurenshi da Raihana ya taso dan jin yake bai iya ha a Daulah da ko wace mace kuma bai ma iya yin adalci a tsakaninsu dan Daulah ce *ZA IN RANSHI* kuma rayuwarshi dole ya samo mafita yanda ran Abbie dama kowa bai zai aci ba idan ya guje ma auren Raihana din.... *Hmm!bakina da goro amma ba ba'ayi komai ba har yanzun shimfidar labarin ZABIN IYAYE muke mai kuke tunanin zai faru a tsakanin Mr president Umar Fatah Umar da kuma ansa Raihan Umar Fatah idan har ya i ZA IN IYAYEN SHI akan ZA IN RANSHI labarin nan cike yake da tausayi da kuma madarar soyayya muje zuwa kawai mutumen kowa dai yasan waye Umar Diga da kuma halinshi na
Chapter 7 · 0% Book details