← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 171

Sashe 95

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun bayan tafiyar Yusuf maganar ta tsayawa maryam arai so sai,
Sai dai kuma ta rasa hanyar da zata fadawa antyn ta cewa ga halin da ake ciki a zancen,
Da bara ce ta fado mata na ta ba wa Anty shawaran zuwa dubo Sadiya din,
Suna zaune a tsakar gida tana,wasa da Abubakar din Anty,
Sai ga kiran yusuf ya ahigo a wayar Anty Dije sun kai wani lokaci dashi su na dan hira,
Inda yake sheda mata cewa ya je gurin ya Iliya mijin Anty yace zai shigo kafin Azumi,
Tai mamakin jin cewa ya tafi gurin shi nan yake sheda mata cewa akwai wasu kayan su da za,a shigo da su sune yaje yin clearing,
Nan yake tambayar lafiyan su Assalam da sauran su amma dai bai tambayi maryam ba,
Itama dai anty sam bata dauki wanan a bakin komai ba ,
Sai zuwa dan lokaci da kare wayan na su ne maryam take cewa Antyn ta
Gaskiya Anty yakamata mu tafi gidan Sadiya mu diba ta kada tace ba ki taba zuwa,
Haka dai tai ta cusawa Anty Dije ra,ayi har dai daga karshe ta amince da cewa zasu, tafi su uku da yara,
Bayan kwana biyu da zancen shiri sosai sukayi i dan ka gansu zaka zata wani guri can zasu,
Ashe wai duk shirin zuwa duban budurwan Yusuf ce,
Kai su akayi a,cikin wata motar da maigidan Anty ya saya ya barta a gida,
Sadiya tana zaune tare da wasu kan,nenta suka kallon tv a dakin mahaifiyar, su,
Suka ji sallaman mutane, kallon su suke yi a cikin rashin sani,
Sadiya din ce tagane su ta ganin Assalam a cikin su,
Nan aka shiga gaisawa a tsakani inda Sadiya din ke nuna yar jin kunya, a tsakani,
Mahaifiyar ta tasa aka kawo masu kunun zaki mai sanyi yaji kayan kamshi sai tashi yakeyi a ciki,
Maryam sai kallon gidan takeyi irin kallon kwam din nan,
Bayan fitar mahaifiyar sadiya da kannen ta ne, suka dan kara gaisawa da Anty
Inda Anty kewa Sadiya kewar Yusuf, din ?
Jin maganar Sadiya tayi kamar don zolaya suka zo mata,
Amma kuma, sai ta tuna da yadda Yusuf ke fada mata halaiyar Anty dakuma irin yadda take son alakar su,
Dago kai tayi tanawa Abubakar dake hannunta wasa,
Sai kuma ta sauke kan ta cikin kwantar da murya tace
Anty Yusuf bai fada maki yana fushi dani bane aiko da ya wuce bamuyi sallama da shi ba,
Kuma nai ta kiran wayan shi bai daga wa,
Nan da nan an nurin fuskan Anty Dije ya sauya lokaci guda,
Cikin damuwa anty ke tambayar sadiya abin da ke faruwa,
Bata boye mata komai ba na yadda kanin mahaifin ta yaiwa Yusuf din daren da yazo zance gurin ta,
Na,imat ba tasan lokacin da tasa kuka ba alokacin,
Tana cewa abin da mutanen su ke yawan fadi ke nan cewa koda Christian ya musulunta gori da hattara da musulumai zasu dinga mai har sai yafi na lokacin da bai shiga cikkn su ba, zàfi da ciwo,
Nan kuma hankalin su yakara tashi ganin yadda Na,imat ke fidda hawaye,
Abu ya taru lokaci guda yai wa Anty Dije yawa, tarasa da,wani zataji,
Sai,da suka samu Naimat (Ejoma) tai shiru san nan suka fara magana,
Maryam na zaune a gefe tai shiru tun da akafara zancen ta na mai jin zafin irin kalamin da aka ta jefawa Yusuf din,
Sadiya ki yi hakkuri zan kirashi in ji may ke faruwa ne ai bai kamata yai saurin fushi ba haka,
Mahaifiyar ta wace itace yar uwan Jibrin din tashigo dakin
Inda take kara fada masu halin kanin mahaifin nasu dan cin mutunci,
Tun a hanya Anty Dije ke ta zabga wa maryam godiya don badon ita da takawo shawaran zuwa diban Sadiyar ba da ba zasu san abin da ke nan ba,,
Cikin ikon Allah ranan Yusuf bai kira anty ba sam tankar yasan da zancen,
Ita ko Na,imat duk hankalin ta ya tashi saboda ji takeyi kawai ta zauna a cikkn yan uwan ta zaifi mata
Kada sai sunyi aure da Ibrahim irin wanan gorin ya biyo baya,
Ji tayi an dafa mata kafada
A hankali ta juya don ganin kowaye maryam ce ke mata murmushi,
A hankali maryam ta zagayo in da Na,imat din take zaune,
Saman hannun kushin din ta zauna a hankali maryam tace
Na imat kada ki sa komai a rayuwan ki pls saboda dama kin san sai an samu irin wanan challenges din,
Saboda wasu basu da tauhidi atare da su just dai suna ansa sunan su musulmai ne kawai,
Ki sani cewa Ibrahim dai kabilar ku guda dashi kin ga ke nan wanan irin challenges din zai zo maki da sauki,
Unlike na ya Yusuf wanda in dai ba haushe mutun ne koda ace shi ya Yusuf din a cikjn musulunci aka haife shi,
Zaman shi na dan kabilar ibo ko bayerabe sai sunyi suka akai,
Kai koma da ace yaren da ke anan cikin arewa ne tare da mu,
Kawai ke dai imani azuciya take ba,a baki ba,
Don haka duk wani tunane ki daina kawai ki sa Allah a gaba kin ji sister,
Kai Naimat ta daga alamar gamsuwa da zancen maryam din duk da tagirmay ma maryam din sosai amma dai yarinyar na bala,in bata shawa saboda irin halaiyar ta,
Ga kuma irin yadda ita da yar ta suke kokarin koya mata addini akoda yaushe acikin sauki,
Sai washe gari ya kira Anty Dije tun daga maganar ta yagane cew akwai matsala don ba haka take mai ba idan suna waya,
Antyna lafiya kuke kuwa naji muryan ki wani iri kamar ba dadi yau azuciyar ki
Anty Dije ce ta katse shi da cewa Yusuf may ke faruwa a tsakanin ka da Sadiya ne ?
Shiru yayi na dan wani lokaci sai kuma can yace tazo gurin ki ne,
Anty Dije bata boye mai komai ba tafada mai yadda maryam taga cewa ya kamata suje su kai mata ziyara,
Nandai ta bashi duk wani bayanin da yadace tai mai alokacin,
Tsawon wani dan lokaci bai yi magana ba sai zuwa can yace,
Ànty Dije gaskiya bazan boye maki ba bazan iya auren Sadiya ba kuma yanzu,
Saboda ko munyi aure za,a samu matsala sosai, daga yan uwan ta,
Katse shi tayi da cewa kai Yusuf yan uwanta zaka aura kodai ita,
? ,
Murmushi yayi kawai yace bazaki gane bane anty kawai abar wanan zancen zai fi,
Yusuf ko da sunyi challenge din ka ne ai ba yarinyar bace tayi ko ?
Zan dai kira ki anty yanzu zan tafi sallah lokaci yayi, pls,,,

Saida ya idar da sallah shi sanan ya kira layin maryam
Maryam wace a lokacin tana daki zaune ta idar da salla itama saboda time akwai dan tazara tsakanin yadda ake sallah a kwantagira da Abuja,
Cikin mamakin ganin layin Yusuf na kiran ta, ta mika hannu akai ta dau ko wayan,
Da muryan nan nata zakwaikwai ta,ansa sallamar tashi,
Gaisuwa ta fara yi mai tana mai kara wayar a,kunnen ta,
Sunan ta yakira cikin wani irin muryan nan cikin golden voice,
Maryam ta amsa da na,am
Yace may ye hikimar ki na kai anty gidan su sadiya pls ?
Shiru tayi kamar bazata ce mai komai ba,
Wani irin nauyi da kunya ne ya lullubeta don may anty zata bari yasan cewa itace ta bada shawaran a,tafi gidan su sadiya,
Karo na biyu ya kara kiran sunan ta cikin wani soft voice da yafi na farko taushi,
Yace kina ji na pls karki boye min komai akai, ki fada min dan Allah,?
Sani sanyi taji don ya hada ta da Allah akai,
Nan take ce mai ya Yusuf a gaskiya dai ka san cewa mutumin bai kyauta maka ba ko ,
Bai kamata ace yai maka wanan cin fuskan ba gaskiya,
Zataci gaba sai ya tare da cewa cikin yar murmushi maryam ai ba karya ya fadi ba ko,?
Tunda dai ni din duk yan uwana kafirai ne ni kadaine Allah ya cire a cikin su,
Kinga ii dole ne in ta samun wanan challenges din ko, ?
Ta gumi tayi da hannayen ta bibiyu tana sauraren shi cikin tausayi
Tana ji tankar ace itace a kusa dashi a lokacin a matsayin ta nadan uwan ta,
Amma afili sai tace to ya yusuf dan Allah kayi hakuri bazan sake ba
Abin ne yaci min rai sosai wallahi shi yasa nakai anty taji da kan ta don a dauki mataki akai,
Murmushi yayi yace aa maryam wani mataki kuma kawai na bar masu diyar su kawai,
Cikin sauri tace subbahanallah dan Allah ya Yusuf kadakayi haka pls,
Saboda may maryam kinfi son ta dani yayan ki ke nan,,?
Ya yariny ce wallahi akwai tausayi idan ka ganta
Nan dai yaci gaba da bata musalai akai har ta dan gam su sukayi sallama,,,,,,

ZEEE. MAKAWA,

[3/24, 10:09 PM] Zainab Makawa: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
5⃣9⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA,

Wanan shafin nasadaukar ga Shahararen Admin of Admins na,COOL NOVEL MAKEUP AND KITCHEN 1,2,3,4,&5
Hayatu Baba Zubuiru (Ya Hayatu), daukacin masoya Novel din FuREN JUJI muna tayaka murnan zagayowar ranan haihuwar ka,🎂🎂🎂 Ubangiji Allah yasa albarka ga shekarun da aka diba,
Babu shakka ka kai a yaba maka musanman ta yadda kake ilmantar da koyarwa uwa uba girki da kwaliya ga nishadantarwa mai karatu Allah ya kara daukaka da Basira 👏👏👏
Chapter 95 · 0% Book details