← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 171

Sashe 75

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Tun da ya shaka shake yake wani irin atishawa mai karfi, babu kakautawa,
Sai ya baka tausayi idon shi sun rine sunyi ja jajari kamar garwa shin wuta,
Sai hayakin da tsohon ya bayar yace ai, mai shi gaba daya a ranan,
Daga gidan Anty Dije akazo da gawayi wuta saboda basu san mutane su san cewa, Yusuf baida lafiya haka, har labari yakai wa mahaifin shi,
Wanan malam tsoho din shi da kanshi yazo tare da wasu yaran shi,
Duk wanda ke cikin dakin akace yafito waje ya samu guri kada ya tsaya kuma tsaye,
Idan ma son samu ne dan Allah duk su watse subar malm Abdulsamad da , mahaifin Jibrin,
Haka akayi kuwa don su KB da su jibrin da Ibrahim duk barin uguwar su kayi, gaba dayan su,,
Fara karaun su malam bada wani nisa ba sai murya sukaji da yare ana magana,
Malam tsoho yadaga kai ya kalli Abdulsamad don ya yi magana,
A cikin harshen IBO suke ta gwalancin su da malam Abdulsamad din,
Abinda suke cewa shi idan ba yabar kasar kwantagora ba bazasu bashi peace of mind ba zasu jagula mai lissafi,
Yai ma malam tsoho bayanin abinda suka ce, sai kuma cewa da sukayi saida a ka yanka masu katuwar bajimin shanu suka sha jinin shi sunyi ma wanda yasa alkawarin cewa za su yi mai aikin shi kamar yadda ya kamata,
Malam yaba yaran shi umurni suci gaba da karatun alkur,ani kawai, babu tsayawa,
Wani irin ihu suka tsala saida wasu suka firigita murya sak na irin IBO din nan tipical one wa yanda basu da imani sam,
Sai suraitai sukeyi da yaren su na IBO suna ta zun duma asharrr,
Duk wanda ke tare da Yusuf hankalin shi ya tashi a lokacin don ganin irin yadda yadinga yi,
Sun jima akan shi sosai sai daga bisani suka ji muryan su suna cewa sun bar shi har abada
Duk da haka ba,a daina karatun ba saida sukaga cewa ya daina komai da yake dazun sanan su ka dakata,
Kwana biyu suna sintiri akan shi tare da bashi addu,oin da zasu taimaka mashi,
Sai yau da yaciki kwana biyu da samun sauki, Jibrin ya kwaso su Anty tare da Safiyar shi da maryam sukazo gaida Yusuf a gidan shi dake Abu,lolo,Eastern,
Maryam da Anty da yaran su , suna bayan mota zaune inda Safiya ke zaune gaban mota tare da Jibrin,
Iyakar burgewa sun burge Maryam sosai tun lokacin da Anty tace wa Safiya ta zaune gaba tare da Jibrin din,
Saida suka tsaya wani shago sukayi mai tsaraban kayan fruits kala,kala shake a leda duk da Jibrin yace kada su saye, akwai shi cike a gidan,
Amma sai Anty Dije ta, ce su dai saye tunda ba,a zuwa gaida mutum hannu saje,
Zaune yake saman sallaya a folon shi ya kunna tashar madina yana sauraron kira,a,
Yana saye cikin wata yar farar jallabiya mai guntun hannu,
Da sallama suka shiga inda Ibrahim yatare su cikin mutumci,
Ànty Dije tace a,a lalai Yusuf jiki yai kyau, tunda yau gaka zaune,
Yana kokarin tashi zaune don tariyae su hannun shi yana dauke da casbaha, yana ja,
Da murmushin maganar da anty tayi yakai zaune da kyau saidai bayan shi na jingine a kujeraa,
Kafin ya kai karshen murmushi sai Anty Dije takara cewa gaskiya dai ya kamata yanzu ace Yusuf ka aje mata kodon taimaka maka da wani abu,
Yar dariya mai sauti yakarati daidai lokacin da ya zauna da kyau Assalam yana kusa dashi zaune,
Jibrin wanda ke shigowa adaidai lokacin yaji maganar da Anty taiwa Yusuf sai ya cabe zancen da cewa ai barshi kawai anty,
Dama akwai wata Cousin sister dina da ta sani gaba da zancen Yusuf tunda dadewa,
Ibrahim dake ta gurin fridge yana aje ledojin da suka shigo da su yace,
Aiko zakayi fada da Aisha idan taji ka da wanan zancen,
Kai Aishan may can inji Jibrin wanda ke kokarin zama saman kujerar da Yusuf ya jingina akai,
Daidai lokacin yadago kai inda Safiya da Maryam suke zaune guda saman kujera guda tana zaune a hannun kujerar,
Murmushi yai masu yana mai ansa gaisuwar da safiya tai mai,
Itama maryam gaishe shi tayi a hankali tare da tambayar shi karfin jikin shi,
Duk hiran da akeyi daga Maryam har safiya babu mai cewa komai daga cikin su,
Sannan ita Maryam bata jinko mai gamay da Yusuf har kasan zuciyar ta,
Kamar yadda shima Yusuf din bai, jin komai gamay da maryam azuciyar shi sam,.
Dan daukar ta yajeyi a matsayin yan uwa kawai daga ita har Anty Dije,
Daga kofar shigowa gidan suke jin murya ana sallama,
Ibrahim ne ya leka dan ganin mai yin sallaman alokacin
Baban su maryam ne da Anty wai yatafi gida ake cemai sun zo nan mai,gidan bai jin dadi shi ne,
Duk sunyi mamakin ganin baba amma sai suka ga cewa kanin ya illiya ne ashe yakawo shi,
Baba yai mai fatan alheri tare da fatan samun sauki,
Anty Dije ce take cewa baba yau ba,a fita kasuwa ba ke nan ko ?
Kaiyya Dije ai kasuwan sai a hankali yanzu, mutum ya fita tun safe karshe baifi yasamu abin sayen abincin rana ba kawai,
Yanzu kinga aiduk dan jarin ya karae sai maneji nakeyi, kawai,
Allah ma ya taimakeni nasamu makwaci mai albarka shike taimaka min watarana,
Baba bai dade ba ya mike yana cewa to shi zai koma, inda su Assalam ke cewa baba tsoho ka sayo muna mangwaro a kasuwa,
Maryam tace akin a saya maku nawa kuka bashi jari,
Baba yace a,a yar Baba kyale su ai zan sayo masu ko kadan ne,
Saidai ba kamar da ba leda ce ya miko wa Yusuf yace abin gyaran baki nagani a hanya nasiyo ma,
Jibrin ne yamike yabi bayan baba da yara suka bishi har kofa suna cewa ya sayo masu abu kaza da kaza,
Sai ga baba yadawo cikin mamaki da kudi rike a hqnnun shi yana gwadawa Anty dije kudin zaikai dubu biyar,
Yadinga sa masu albarja dafatan alheri a rayuwan su,
Sai da baba ya wuce Anty dije tacewa maryam ta dauko wa Yusuf fruit ya sha,
Yadan daga kai yakalli anty yace da na anbarshi ai, don ban dafe da sha ba,
Maryam wace a lokacin har ta dauko wani plate ko daga ciin basket din abincin da suka shigo da shi,
A gaban shi ta aje fruit din har zata juya sai Anty tace mata,
Bude ledar da baba yakawo mugani, ko may ye acikin shi haka, ?
Zogala, ne mai yawa hade da kayan gyaran shi
Wani plate ta,dauko ta juye aciki inda Anty, ta bukaci a zuba mata,
Tayi hakane don Yusuf ya sake jiki yaci zogalar don zai gyara mai bakun shi,
Har safiya saida suka vi zogalan amma banda maryam wace ke zaune ta kura ma tv ido tana kallon yadda ake rubuta haruffa kira,ar da akeyi,
Ke baza kici ba ne, yatan baye ta a hankali saida safiya tadan tabo ta sannan tagane da ita yake yi,
Kan ta dake kasa ta girgiza tana wasa da wani dan stone da ke makale a gefen kujera,
Idon ta kem akan shi sai yanzu ta ga irin raman da yayi cikin kwana biyun nan,
Harda wani dan kwarmi kwarmin gurin idanun shi yayi,
A hankali yake cin zogalar shi hankali kwance ba abin da ya damay shi,
Kallon shi sosai taba da himmar yi, hakan yai daidai da dago idon shi daya don yace ta miko mashi ruwa,
Kanta ta mayar kasa da sauri, cike da jin kunyar shi na kama ta da yayi tana mai kallon kurulla,
Maryam help me with water pls,
Yace alokacin da ya kura mata ido,
A kunyace ta ansa mashi da to,
Tamike a hankali har zata fara tafiya sai kuma ta tsaya tadan kalli inda yake tace mai sanyi ko kuwa,
Kai ya girgiza mata alamar a,a mara sanyi yake so,
Goran ruwan majidadi water ta aje mai a gaban shi, ruwa mai kyau da tsabtar sha,
Sai cup da ta hado mai dashi nan yaron anty Abubakar yaga ruwa sai yaron ya hau tsalen cewa abashi ruwan yasha shi ma,
Yaron na,ta kokarin zillowa daga jikin uwar shi,
Abubakar sadiq ko ruwan kake son shane inji Yusuf wanda hankalin shi ya kai ga yaron,
Kyale shi kawai, a,a haba anty ruwa fa yake so, ko banza aikin san mai sunan ba abin wasa bane fa,
Sunan amin ma,aikin manzon Allah ne, shiyasa nake girma ma duk mai wanan sunan,
Ruwan ya tsiyaya a cup ya cewa Maryam miki min shi yasha,
Yaron ke faman kwankwadar ruwan amma ita maryam duk wani irin shock ke jan ta,
Saboda dan hucin numfashin Yusuf dake bugo ta,
Shima bangaren Yusuf din hakane yake ji kamshin turaren Bushrah da black oud din data shafa duk ya wanu susuta shi,
Zogalar da yadaina ci ke nan saboda wani irn mugun kasalar da ya sauka i a lokaci guda,
Assalam ne ya cinye duk sauran zogalar
Idon shi yana a lumshe bayan shi da wuyar shi suna jingine da kujera,
Kamshin yakara dukan hancin shi abinda ya sanar mai da cewa maryam takara zuwa kusa dashi ke nan,
Muryan tace tana ce mai ga ruwa ya wanke hannuwar shi,
Thanks a lot ya furta a yar siririyar murya ta yadda ba kowa ne zai iya jin shi ba,
Bayan ta yabi da kan lo nadan second sai yai sauri ya kauda kan shi dan guda shiga hakkin ido,
Ita ko maryam tana shigowa falon daga gurin da taje zubar da ruwan
Sai ce masu tayi tana mai kokarin daukar gyakenta anty mutafi ko,?
Jibrin muke jira yadawo dafa sayen magani ai, ko,
Dole ta koma ta zauna saman hannun kushin din again zaman da yai daidai da kiran wayar ta,
Kamar kada ta dauka saidai ta daure ta ciro dan ganin kallon da Safiya tai mata,
A,A ne kiran ta saidai kuma ta tsinci kanta da jin nauyin ansa kiran nashi,
Har kiran ya katse bata dauka ba, tana kokarin mayarwa a jakanta ne wani sabon kiran yakara shigowa,
Dole badon taso ba tadauka tana mai cewa Assalamu Alaikum,
A hankali take ansa mai maganar sai kuma tamike tsam daidai lokacin da take cewa mun fitane zuwa unguwa, duk kan mu
Idon kusan duk suka bita da, bishi a lokacin kowa da abinda yake sakawa a ranshi,
Shiru yadan biyu baya a falon sai Yusuf ne ke, cewa Assalam gobe tare zamu tafi massalaci ko,
Sai a lokacin Anty Dije wace ke wani tunane can ta dan nisa tana mai cewa,
Har ka ji saukin fitane Yusuf aidade ka bari har ka, kara, ji sauki, ko,?
A haba no,no,no Anty ai zan iya zuwa insha Allah I am ok now,
Kaiwa a shirya min shi, mutafi,
Chapter 75 · 0% Book details