← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 171

Sashe 73

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Maryam takai wani lokaci tsaya daga inda take,
A hankali tace mai cikin sanyi murya mara sautin furtawa
Ga abin karyawa nan a falo, nakawo ma,, Anty tace ya jikin naka?
Saida yadan gyara zaman shi yakara dan dunkulewa guri daya, sanan
Ya dago jajayen idon shi da suka rine sukai mai ja jajir kamar garwashi,
Gabantane yakara ba da dam sai ji tayi tankar ba Yusuf wanda ta sani bane take kallo a lokacin,
A hankali Maryam ta isa har kusa dashi, kai kasa cike da jin nauyi Maryam, tace mai kasa hannun ka a goshin ka kadinga karanta,
Falaq da Nas da Iklas,, kowani uku, uku, katofa, a hannu, kashafe kan ka da shi,
Har zuwa jikin ka, sai,ka kara karantawa a cup kasa a ruwa, tare da Ayatul,qursiyyu,
Sai kuma a samu wanda zai karanta ma suratul,Jinn, gaba dayan,ta
Duk gankali shi ya tattara yake sauraron ta, don jin bayanin da take mai,
Tana kai nan tace mai Allah yasa mu dace Allah ya bada sauki,
Ibrahim wanda ke tsaya tun fara,zancen ya ce ma ogan shi ya kawo mai abin karyawa ne, a falon, aka aje,
Da kyat ya iya dan girgiza mai kai, a,alamar a,a,
Marayam tace mai a kwai kunu da kosai a ciki da ta damo mai,
A hankali yace wa Ibrahim yakawo mai kunun kawai bada kosai ba,
Ya,dan yunkura a hankali ya zauna da kyau,
Dan karamin kofi ne amma sai ya kasa shanyewa duk,
Da sauri maryam ta fita zuwa falon sai gata dauke da cup da goran ruwa,
A hankali ta dan durkusa gefen shi ta balle goran ruwan ta tsiya,ya ruwan kusan rabin cup din,
Ta kai cup din daidai bakin ta tafara jero mai addau,oi acikin ruwan,
Tsawon yan mintoci tana tofe ruwan dasu har zuwa inda takai aya takara dan tofawa,
Mika mashi cup din tayi tace ya sha yadan shafa saura,
Ido takafa mai har saida taga ya shanye ruwan saura kadan sai tace wa Ibrahim ya shafa mai aduk jikin shi,
Mikewa tayi a hankali da niyar barin kuryan dakin cikin mutuwar jiki,
Ido ya,bita dashi don bai taba sanin tana dakirki ba haka sai yau dayaga ta tausayawa ciwon shi sosai, har da bashi addu,a,
Muryan ta yaji tana cewa Ibrahim yai mai kamu a goshin shi ,
Daga haka tasa kai, zuwa waje, inda ta ke kokarin barin gidan don komawa,
Babu wani sallama taji kawai tayi karo da mace, tana kokarin shigowa gidan,
Aisha ce cikin wani dogon rigar dinkin material ja mai laushi, dinkin mai dogon hannu ya dane mata cas,
Ganin Maryam yasa Aisha yi mata wani irin mugun kallo naje wace,
Inda ta aje yar pos din ta da ta sa kudin mashin din ta tanufa,
Ke, daga, ina kike haka,?
May ya kawo ki,nan,? Zata kara magana sai ga Ibrahim ya budo labulen kofar yana cewa Maryam wai yace kice ai,mashi tuwon dawa ya ke so,
Wani mugun kallon ke baki isa bada amsa ba Maryam ta watsawa, Aisha wace ke tsaye tana mamakin ina wanan tsaleliyar budurwan mai zubin fulani tafi nan,
Jin muryan Maryam, yakara ruda ta a lokacin da taji Maryam nace wata irin miya za ai mai,
Juyawa Ibrahim yayi zuwa cikin dakin yadan leko yace wa maryam wai ta shigo,
Kusan a tare suka shiga dakin da Aisha wace ke wani irin shu,umin kamshi, duk gidan ya bure da shi,
A kwance tasa mashi kasan dan karami carpet din dake tsakiyar dakin ya kifa kan shi a filo,
Da kyat ya dan iya juyowa inda take yana ce mata,
Ki min irin wanan miyar da kika taba yiwa mama a Bobi,
Aisha wacce a lokacin har ta kara inda yake kwance tana kokarin zama, gefen shi gab da shi,
Maryam ta kara watsa mata harara tasa kai abinta zuwa gida,
Zuciyar ta fam da Allah waddai da irin halin rayuwa irin ta,su Aisha,

Maryam na barin gidan Aisha ta waigo inda Ibrahim ke kokarin kawar da cups din da aka bata,
Sai ce mai Aisha tayi wanan yarinyar yar gidan waye ita,?
Yar gidan Anty ce Ibrahim yabata amsa a,takaice,
Yusuf wanda tunda ta shigo bai,yi magana ba yace mai ya faru da kike tambaya, ?
A hankali tana kokarin kai hannu gare shi don wai ta taba lafiyar jikin ta ji inda sanyi ko zafi,
Cikin wani irin karfi ya hankade hannun nata tun kafin takarasa kaiwa a jikin shi,
Cikin wani irin murya yace mata
May ye haka pls, ?
Murya irin ta mai shagwaba, tace, to ba zan ji inda zafi bane jikin naka,
Tsuki ya ja yana mai juya kwanciyar shi ya kauda kan shi gefe guda,
Idon ta yakai ka inda yar brief case din shi take a yashe can gefen gado a kasa,
A hankali kuma takara daga ido tana mai karewa dakin kallon tsab,
Shigowar yan dattijan biyu ya banna wa Aisha tsari a lokacin,
Sam batai farinciki da shigar su a daidai wanan lokacin ba
Dattijo Abdulsamad na ganin ta ya ran shi ya baci don baya ra,ayin irin yaran nan sam, masu zubar da mutuncin su, haka,
Don yanayin shigar ta kawai ya ishi mutum yagane kowace iri ce ita don ba kunya a tare da ita sai fitsara

Dole tabar dakin cikin fushi don ganin manya suzo,
Gaisawa sukayi da shi cikin cijewa yake magana
Don shi kadai yasan yadda yake ji a jikin shi lokacin,
Sai wani zufa daya tarso mai daga jikin shi duk da sanyi A,C dake dakin,
Sun tambaye yadda yake ji tanzu sai yake sheda masu yadda ya kwana,
Sai kuma zuwan Maryam da taimai addua yashe sai yaji wani irin abu kamar a fisge mai wani abu daga cikin kun,nuwar shi,
Yace saikuma wanda tace Ibrahim ya shafa mai ajikin shi
Shi tun lokacin yake jin wanan zufan na tartso mashi, daga ko ina na jikin shi,
Juna suka kalla suka kada kai, don jin maganar tashi,
Mahaifin Jibrin yakalli kofa inda Aisha tabi yanzu zuwa waje yace,
Ita wanan din dai da naga ta fita yanzu, tai maka addu,an,
Ibrahim' da shi kan shi Yusuf sukace a,a a lokaci guda,
Ibrahim ne ke fada masu cewa Maryam kaunar Anty Dijen shi inda yake zuwa cin abinci idan yazo,
Yusuf din ne ya mike zaune a hankali yana maida numfashi guda guda gami da yin ajiyar zuciya,

A, kamshin gaskiya wanan al,amari akwai jinnu a cikin shi, ko sihiri,
Duk da halin da Yusuf ke ciki na jin jiki bai hana shi yin yar murmushi ba,
Ya dan kalli inda suke yana mai yin murmushin karfin hali ya ce ciwo ne kawai dai zo min a haka, baba,
Su ma dai murmushin sukai mai a lokacin don, sun san bai san komai ba, tukun daga sheri dan adam,
Ibrahim ya kalle cikin yar karamar murya yace mai ya kuna mai hearter yai wanka,
Da tai makon Ibrahim yasa mu ya mike zuwa cikin makewayi don ya dan watso ruwa ko zai ji sanyi a jikin shi,
Ita,ko Aisha ganin cewa wa yan,nan yan dattawan biyu basu da niyar fitowa yasa ta cewa bari taje ta dawo idan sun wuce,
Don ta sa rai acikin yar briefcase din nan nashi da tagani a yashe,
Ibrahim ko yana ganin Yusuf ya shiga wanka shima sai ya hau gyaran dakin
Inda ya kwashe sauran kaya yasa acikin wardrobe din bangon dake dakin,
Ya kule ya tura keys din a cikin aljihun shi ya koma falo don ya karya,
Sai a lokacin ya lura da cewa Aisha ta ta,fi kila don bai ganta ba,
Har waje ya leka yagani ko zai ganta sai dai babu ita babu alamar ta ya ja yar guntuwar tsuki yakoma cikin don shi sam batai mai ba,
Yusuf yafito yasamu babu kowa a dakin dan haka sai yadan zauna a bakin gado,
Cikin shigar jallabiya yadan samu yafito falon shi yazauna,
Remote din TV ya dauko ya kuna TV, inda ya kamo NTA kwantagora,
Ya soma kallo,
A inda yake a hankali ya soma jin kan shi na wani juyawa kamar za,a kife shi a gurin,
Addu,an da ta koya mai ne yazo mai arai don haka yadan lumshe idon shi yana mai rike kan shi da hannu guda,
Sannu a hankali yake yi yana tofawa a hannun shi ya shafawa asaman kan shi har bayan shi,
Kamar an wallawale shi yaji saidai kuma yaji baya kaunar kallon TV don haka yabar shi a kunne ya koma ciki,
Chapter 73 · 0% Book details