← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 162 OF 171

Sashe 162

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Lokacin sanyi ne, don haka kusan goma na safe amma Yusuf ya na kwance makale da matar shi wace bata da wani hutu idan yana gida,
Barci sukeyi amma ajikin shi take kwance saboda jikin su akwai gajiya,
Wayan Yusuf wace ke yashe a gefe guda tai kara har wayan ya kusa karewa suna kwasan barcin su a lokacin,
Maryam ce tai kokarin dagowa daga saman kirjin Yusuf, din,
Itace tadan dauko wayan daga inda yake a yashe,
Idon shi da dan sauran barci a kai sai kuma haushin wanda ya tada shi daga barcin shi da yake yi na safe mai dadi
Samuel ne ya gani a rubuce saman screen din wayan shi,
Samuel how are you ?
Brother we are coming to Abuja this morning with papa,
Yusuf din wanda yaji maganar kamar daga sama zubur ya mike daga inda yake kwance,
Maryam wace a lokacin tana cikin bathroom shi kadai yai zaune a bakin gado yana tunane da nazari,
Shawara guda shine ya kai su gidan shi guda kawai ya kai masu masu aiki can,
Ganin shi a bakin gado cikin yanayin damuwa ya sa maryam saurin karasowa gurin shi da,sauri tana cewa uncle lafiya,
Kan shi yadaga a hankali ya kalle ta kamar kada ya fada mata sai yaga ai sani zatayi,
A hankali kamar wanda zai fadi wani mugun zance rai a dan bace
Hakan yasa maryam wurgat da dan towel din dake a hannun ta kasa,
Da sauri takaraso gu4in shikin tambaya take cewa
May yafaru ne wai batare da ya kalle ta ba yace wai baba da yan uwana zasu yau din na,
Maimakon maryan ta nuna razanan ta afili sai Yusuf yaga tana murmushi,
Tace ashe barin fita in fara abin taron baki yau muna da bakine haka agidan,
Kallo yabita dashi na mamaki don yazaci ta nuna mai kyamar ta karar akan su
Ta mike da niyar ta wuce taji ya riko hannun ta, ta baya cak ta tsaya guri guda
Muryan Yusuf ne da yajawo ta zuwa jikin shi yana cewa maryam baki tsoron zuwan su gidan nan,
Tsoro ta tambaya cikin mamakin jin maganar shi tana mai wani irin kallo
A kwai matsalane halan, gazuwan su tatambaya cikin nuna rashin damuwa,
Bai ce komai ba shima mikewa yayi batare cewa komai ba,
Sai sai maryam tai masu girki inda takuma sa a,gyara masu dakunan kwana, amma Yusuf bai da labarin haka,,
Sun iso garin bayan sallan la,asar alokacin maryam tana dakin ta na sallah,
Azaton Yusuf sukadai ne zasu zo yan gidan su sai gashi ya ga mutane masu yawa,
Yan manyan church din su ne tare da mahaifin shi wai sun zo wani taro ne a wani church irin nasu,
Duk yawan abincin nan sun cinye abinsu sai kari suke bida,
Nan ihu yatashi da kiran sunan Jesus, maryam tun daga dakin ta na sama take jin wanan ihun nasu,
Sai kalman Innalillahi take iya maimaitawa kawai, a bakin ta,
Yusuf wanda yaso yakai su masauki amma fafir sukace su a an zasu sauka,
Sau guda maryam din ta sauko kasa gaida su suna zaune ga kwala be a gaban su sai dai bazata iya tantance kona maye ba,
Cikin zulunbun Hijab din ta har kasa baka ganin komai nata sai dan round face din ta kawai,
A natse take tafe Yusuf na gaba tana bin shi baya cikin natsuwa,
Duk kunya takama shi ganin irin yadda suka baje tumbi da kuma sake jiki suna ta faman dura giya a cikkin,
Duk kunya da nauyi ya kama Yusuf wanda rayuwan shi duk yabaci amma bai,da yadda zai yi ne kawai,
Kowa sai kallon maryam din yakeyi kamar zasu cinye ta danya,
Tundaga wanan ranan maryam batakara saukowa ba,
Saidai Yusuf yasayo mata abinda za ta ci ko take bukata,
Kwanan su goma sanan sukabar masu gida inda kafin su wuce baban Yusuf yake cewa shi yafi son Yusuf ya auro yar yaren su,
Tafiyan su ba karamin dadi yaiwa Yusuf ba wanda ya dinga ji tankar yai kuka saboda ansha mai giya a gida,
Masu gyaran gida yaturo sukai wa gidan nashi, kwal komai saida aka wanke,
Yafara zuwa office bayan dawowan su a can KB yasamu Yusuf yana bashi labarin yadda Jibrin ya auri Sadiya,
A cewan KB wai harda mahaifin shi yace kada ya yi wanan auren amma Jibrin din ya dage akan sai yayi,,
Kuma yanzu ga shi sai sukan Yusuf da maryam yake yi duk inda ya zauna,
Yusuf yaso ya bata rayuwan shi akan yadda Jibrin din yai mai sai dai yaga cewa babu abinda a gwada mai a rayuwa yanzu,
Baiwa maryam zancen ba sai bayan kwana biyu a lokacin yana aiki a cikin computer shi
Maryam tana zaune a kasa ta sa fruit a plate sai sha takeyi
Idan ta sha tabare ta sawa Yusuf a baki yana yi yana aikin shi,,
Maryam Yusuf ya kirata batare da yadago kan shi daga aikin da yakeyi ba,
May kika sani akan rabuwan Jibrin da safiya ?
Tambayar ya bata mamaki sosai a lokacin don bata zaci zai kara maganar ba,
Uncle gaskiya ni abinda safiya tafada min bawai nayarda bane,
Fada min may ta fada maki maryam bata boyewa mijin nata komai ba azancen da safiya ta fada mata,
Hmmmm kawai yace bayan da ya fahinci maryam tagama zancen ta,
Maganar tasa Yusuf ya kasa aikin dake a gaban shi yadan dago daga duken dayake,
Hannayen shi ya hada guri guda yadan fura iska ta tsakiyan su,,,,

Dasafe idan Yusuf yafita gurin aiki sai shida yake dawowa gida wata rana yakan dawo daguri kuma,
Yau ma sun rabu lafiya tsakanin su Yusuf yatafi yabar maryam tana daga mai hannu
Ta koma ciki ba a dauki wani lokaci ba barci ya kwashe ta,
Kaman ance ta bude idon ta sai wata budurwa tagani a dakin,
Ta na saye da dan guntun buje daidai cinyar ta, sai rigar jikin ta baki mai kama da shimi,
Tashi maryam tayi taga kwancen da take cikin mamaki don budurwan ta gaban mirrow tana shafa jan baki a bakin ta,
Cikin hausa mai surki da yare tace kin tashi matan yayan mu,
Murmushi maryam tasake mata, nashigo kina barci shine nace barin kyale ki,
Har nai wanka baki farka ba sai yanzu dama zan fitane akwai saurayi da zai zo,
Zaune maryam takai inda ta sako kafafun ta kasa cikin mamaki,
Amma ga yadda taga budurwan na murmushi sai tadan sake ranta itama,
Yanzu dai mu gaisa sunana Ruth ni kaunan mijim kine da fatan ya baki labarina,
Takarashe zan cen da son jin ansan da maryam zata bayar
Cikin murmushi maryam tace kece Ruth ashe ko yau she yana zance a kanki kuwa
Ruth taji dadin hakan don sai da ta dan yi murmushi mai baiyyana hakora,
Maryam tace barin kawo maki abinci ko kafin ki fita,
Cikin daga hannun ta tace da sauri No, no no ki barshi kawai
Sai nadawo idan brother ya dawo saiki fada mashi pls,
Daga haka tafita kusan a tsirara take maryam ta sauke ajiyan zuciya bayan fitan ta,
Hamdallah ta yi ga ubangiji da yayo ta musulma,
Abinda maryam ta lura dashi shine Yusuf naji da sister shi Ruth sosai don haka tadauki alwashin kyautawa Ruth din itama,
Chapter 162 · 0% Book details