← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 171

Sashe 78

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Yusuf ya iso kofar gidan Anty Dije, bayan sati biyu, da misalin karfe biyar na yamma,
Da sallama ya shigo cikin gidan alokacin maryam tana zaune cikin shigar shadda kamfala,
Shiri takeyi zata gurin bukin wata abokiyar ta na tun secondary school,
Zaune ta a saman kujera yar tsuguno tana ta faman gyaran fuska,
Dawani guntun broking mirrow, sallamar shi ce tasa ta tsaya wa daga fente fenten fuskan da takeyi,
Da yar fara,ar ta, a fuskan ta ,tare shi
Sannu da zuwa ta iya furtawa a hankali amma tana mai dukar da kai,,
Kallo guda yai mata yaga yadda ta koma kamar wata, classic baby,
Yaji wani yarrr amma sai bai ba da wanan abin yaji wani ma,ana ba,
Kafin ya karba mata anty dije ce tafito, a lokacin,
Ànty Dije ce ta fito daga ciki tana dariya da murnan ganin Yusuf a wanan lokacin,
Oyo, yo da mutane Lagos ne ko Abuja, sai da yai yar dariya na nuna farin ciki, yace ai nafi zama a Abuja yanzu,
Maryam ce ta tashi daga inda take ta dauko yar jakar kayan make,up din ta,
Tagaban Yusuf tayi bi inda kamshin nan nata kamar kulun yadaki hancin shi,
Ga dikin purple shadda kamfalan da tasa ya karbi jikin ta, tsab,
Daidai da zaman shi a lokacin ta dauko mai ruwa a cikin gora, hade da cup
A gaban shi ta dire kayan karo nabiyu kenan da wanan kamshin da ta budawa jikin ta yasa shi lunshe idon shi,
Thanks ya,furta a hakali kamar yadda ako yaushe maganar shi mai rowa ce,
Idon shi a lumshe kamar mai barci taji muryan shi yana cewa, maryam ga key a,dauko wa an nan kayan dake cikin motar,
Wani irin haushin taji don tasan zai bata mata lokaci ke nan,
Da sauri ta kalle shi tace saidai kila ba yara a wajen ko, ?
Daga shi har anty ido suka zuba mata dn jin maganar ta ,
Wanda ya nuna tana uzuri ne hakan yasa tace masu ba yara,
Anty Dije tace maryam sai kace ba wace iyakarta cikin kwantagora ba,
Wallahi Anty bana son in makara ne saboda sun riga sun sa cewa bazan zo ba ma sam,
Nikuma ina son basu mamakine su ga na riga kowa isa gurin,
Takara sa fada cikin shagwaba kamar yar karmar yariya mai shirin yin kuka,
Da ga ida yaje zaune ido kawai ya zuba mata alokacin ,
Don yadda take maganar kamar wata yar goye,
Anty ce tace inbanda abinki maryam tun da ga sauki Allah yakawo maki kawai da kin kwaso sai kibi Yusuf ya sauke ki tun da hanyar su zaki bi,
Kai kasa cike da jin nauyi likamata bin shi da antu tayi tace,
Ai basai na bishi tun da bai tashi ba kawai zanbi motar kasuwa,
Muje in sauke ki idan nadawo zan samu yara su sauke kayan,
Wani irin nauyi maryam taji a lokacin sosai, don jin ansar shi,
Ba musu dole ta jawo gyalen ta ta yafa tare da murza mai turare tako ina
Tsaye yake a bakin motar shi yana waya fuskan shi na kallon ta cikin gidan nasu,
A nutse ta ke takowa zuwa ida motar shi take, waya yaje yi amma kallon tsab yake kara mata ,
Tsayawa tayi daga dan nesa dashi kadan ta yadda bazata ji may yaje cewa ba,
Yagane nufinta don haka ya tsaida wayar yana ce mata bissimillah mana mutafi ko,
Mamakin irin saurin kwashe dabi,un shi na hausawa,musulumai da yayi da sauri takeyi,
Bayan motar ta tukara inda yace mata haba dai ai bayan ba guri duk kayane a ciki,
Dawo gaba kawai ki shiga ina ga zai fi,
A hankali ta saje hannun ta nufi dayan bangaren ta bude,
Kamar kullun sanyi da kamshi dai yana nan a motar nashi,
Ya na kokarin tada motar ne yake ce mata ina,ne gurin da zaki din,?
Tace mai MARAFA parks,
A takai ce tai maganar don haka bai kara tambayar ta ba,
A marairaice kamar mai shirin kuka tace, don Allah ina son zan dan tsaya Blue, sea, super market,
Batare da ya kalli inda take ba yace mata ok kawai, .,,,,,,,,,, ,

ZEEE MAKAWA,,,,,,

[3/24, 2:21 PM] 0mmer Farouk: .🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
5⃣0⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA,

UBANGIJI ALLAH YASA MUGAMA DA DUNIYA LAFIYA BAKI DAYAN MU YAN UWA MUSULMAI,,,,
👏👏👏👏👏👏👏
Chapter 78 · 0% Book details