← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 171

Sashe 17

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Musalin biyar na na yamma ya shigo garin kwantagira bayan dan banzan gudun da ya dinga shararawa shi kadai acikin mota,
Tun kwanar shiga gidan su yafara ganin abin hawan su duk ya cika kifar gidan su,
Hankali shi ya tashi matuka daga ganin taron IBO haka,
Hon yayi mai karfi wanda dole suka bude mai get,
Da kyat yasamu inda yadan parker motar shi a can gefen cikin gida,
Tun bai fito daga cikin motan ba ya hango wata yarinya a tsugune gaban elders nasu,
Yana ganin haka ya san cewa wani case sukeyi mai karfi,
A hankali ya fito daga ccikin motar saidai ganin mutane a gidan ya hana shi bude bayan motar don ya fitar da tsaraban da yazo da shi,,,
Tun daga nesa yake jin yadda yarinyar ke gumza ta na ihu da kuka mai ban tausayi,
Tana, mai ba da hakkuri sai kawai yaji wani iri a zuciyar shi
Don komadai may tayi yakamata,su yi considering din ta a mace ce fa,
Ko kallon su baiti ba ya wuce ta gefen su batare da ya tsaya gaishe su yadda ya saba ba,
Wanan ya kalli wanan wancan ya kalli wan can,
Su na mamakin shi don basu san shi da halin rashin mutunci ba,
Samuel wanda ke labe tunda aka fara case din shine ya ke taron dan uwan shi cikin mutunci,
Nan yake washe baki babu ko ga ruwa ya fara labarta ma Joseph cewa
Na, Ejoma Ebere one hausa boy givern bele,,,
D hausa boy now say no b him do amm,
Na yin d elders wan punish har,,,
Y ,she, give her self to musulim boy,
Me ,I know ask u ooo,
Joseph ya ce ma Samuel wanda da har zai ci gaba da zubawa,
Roban ruwa yadauko ma kan shi daga cikin fridge din,
Ganin cewa Samuel baida niyar kawo mai komai
Eanka yafada don ya sauke gajiyar shi,
Daga cikin bayin yakre jin karar motocin su da mashunar su suna watsewa
Saida ya shirya tsab yafito cikin wasu kananan kaya,
Abin mamaki wanan yarinyar Ejoma yagani rakube bayan kujera a falon su, har yanzu tana dan sheshekan kuka,
Sai a lokacin yake gaisawa da mahaifin shi wanda ke zaune ya mike kafar dake mai ciwo saman wani tsohon tebur,
Joseph y u know greet my people,?
Baba me i don't have problem with dem woo,,
Waiting dis girl do here Dad ?
Yace mai zata zauna har asan yadda za,ayi da ita ne,
Don ta je tana bin yaran hausawa ga irin hawalan da wo mata, nan,
Wayan Joseph din ce tai kara a lokacin wanda hakan ne yasa shi samun sararin guda daga fadan baban,
Motar shi ya shiga ya bar gidan nasu don yasan cewa fadan sai ya kawo kan shi a karshe,,,,
Tafiya yake yi kawai don yasan cewa KB bai gari kuma ,
Don haka zuciyar shi ta raya mai cewa yaje wurin little friend kawai ya ganshi,,
Anty Dije ta gama abinci kenan tana ko gyara ko ina na gidan,
Daga waje yadan tsaya duk da cewa an bashi umarni akan ya shigo ko yaushe yake bukata,,,,
Amma sai yaji cewa bazai iya shiga ciki kai tsaye ba
Don haka daga daga,waje kadan yadan tsaya yace Salamu Alaikum don Allah ko Assalam na ciki,
Cikin mamaki mai ma Assalam sallama duk suke
Shiko Assalam har yagane murya da wani irin ihu yafita kofa inda Joseph ke tsaye yadaga shi sama cak yana dan juya shi,
Sai suka kama dariya a tsakanin su, daidai lokacin da duk sauran yan gidan suka leko ta kifar falo suna kallon su,
Ànty Dije ke cewa a, Joseph shine baka shigo ba ka tsaya daga nan kana cewa kana ma Assalam sallama,
Dan sosai kai yayi da key din motar shi yace ai zan shigo nakira Assalam ne yai min jagora,
Falon anty ta bude mai yashigo daidai lokacin da maryam ta dauki buta don zuwa yin alwalar sallah magrib,,
Bayan sun gaisa da Anty dije sai kwai ta fara gabatar mai da abincin a lokacin don dama har ta gama komai,,,
Cikin nuna jin kunya yace mata ya gode bazai ci ba
To ke nan kai kana jin tsoron cin abincin mu Joseph shine shi Assalam, ka ke kawo mai sweet, time to time,
No haba Anty gaskiya ba hakana bane,
Kawai dai naga cewa nashigo late evening ne kin rida kin gama cooking din ki ko
Idanzaka ci kaci kawai don sama mu a aje extra ko yaushe,
Badon yaso ba yadan dauki spoon ya fara ci a hankali,
Yamai yar jin nauyi da kunya duk da cewa daga shi sai Assalam ne a falon zaune,

ZEEE MAKAWA
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
1⃣2⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
Chapter 17 · 0% Book details