← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 171

Sashe 67

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maryam tana shiga gida ta tsaya da mamaki tana karewa Kayan dake zube a kofar, dakin mahaifiyar ta,
Muryan mijin maman taji ya na ce cewa kai maryam ban san bakin da zanyi godiya akai ba wallahi,
Kusan kwana, biyu nan duk yan dabaru mukeyi wallahi saboda duk dan abin dake gare ni jinyar mahaifiyar ki ya cinye shi,
Murmushin yake tayi kamar gaske amma sai malam din yaci gaba da fadin
A cikin kwantagora yake dan gidan waye shi halan da wanan da wai,niyar haka,
Baba wallahi ban san gidan su gidan mu kawai yake zuwa
Zancen ta baisa sun yarda da ita ba sun dauka wai kunya take ji,
Shiyasa bazata iya fada masu gaskiyan zancen ba saboda nauyi,
Dakin mama ta fada bayan ta gaishe ta sai kuma ta fara kokarin ganin ta gyara dakin ko banza su shaki iska mai dadi ai,
Duk wani abinda yakamata tayiwa dakin tayi cikin dan lokaci guda ta kwashe kayan wanki daniyar zuwa tasai ruwa ta wanke,
Kudin da Baba ya bata ta shiga mota da wanda, Anty dije ta bata don tasamu na dawo wa,
Dashi tai niyar sayen ruwan, jawo jakar dazatayi ta dauko kudi ,
Sai ganin kudi tayi zasu kai kimanin dubu hamsin a jakar ta,
Wani iri taji a cikin zuciyar tta duk inda tashin hankali yake hankalin maryam ya wuce nan,
Da gagawa ta mike zuwa inda wayar ta yake a cikin jakar ta yar pos,
Anty takara tambayar maryam lafiya jikin mama,inda take cewa maryam
Ashe su Yusuf ne suka kaiki, har kamfani maryam daga rakiya tasha sai kawai ace antafi har bobi,
Ànty cikin wata murya mai kama data kuka tace, kin san ko may Yusuf yakawo masu kuwa anty ?
Yakai masu maryam shi Yusuf din ?
Nan maryam ta shiga zayyano mata duk irin a binda yakai,masu
Saiku tadan sasauta muryan ta kamar ta marada tace,
Yanzu nazo zanyi wanki nasamu wasu kudi masu yawa acikin jaka ta anty,
Shiru nadan wani lokaci anty Dije ta dauka tana tunane sai tace Yusuf ne nasan yasa maki su aciki don yasan cewa bazaki karba ba,
To Anty ni may zai sa ya kashe kanshi haka wallahi ni bban son takurawa mutum sam,
Haba Maryam yakamata fa sce kin san kowaye Yusuf zuwa yanzu,
Bai kamata ki dinga irin wa yan nan maganganun ba dan Allah
Wanan bawan Allah duk wani damuwa namu yana kokarin nuna concern din shi akai,
Shiru Maryam tayi tana sauraron Anty dake magana cikin bacin rai,
Rai a,bace Anty Dijen taci gaba dayiwa maryam fada
Kara na biyu da Anty Dije takira sunan maryam again tace abinda nake so dake shine ki buga masa ki mai godiya,
Nima idan ya shigo cin abincin dare zan mashi nawa godiyar,
Sai tai magana cikin tausa murya tace, Maryam Yusuf mutum ne mai son taimakawa na kasa dashi ko yaushe,
Baki ga yadda yazo tana nunamun damuwar shi akan matsalar rashin kai ta asibitin da ba,ayi ba,
Wani irin sanyi maryam taji a ranta na cewa yadamu so sai da uwar ta,
Yanzu kinsan yadda zakiyi kudin nan dan Allah kiyi kokari ki diba kiwa mama amfani dasu yadda ya kamata kinji,
A sanyaye Maryam tace wa Anty Dije to na gode Anty,
Amma duka kudin saidai in rago maki wani abu daga ciki ko,tafa ciki wata irin murya mai ban tausayi,
Subbahanallahi maryam muda yakewa alheri ko yaushe muna ci,
Sai dan wanan da yaiwa mama zan sa rai kuma haba dai,
A sanyayae takara fadin to anty zanyi yadda kikace din,
Kafin sukashe wayar Anty takara jaddada wa Maryam takira Yusuf taimai godiya dan Allah,
Kayan wanki take hadawa amma tunanen yadda zata kira layin Yusuf da anty ta turo mata, takeyi,
Aikin ta tacigaba dayi inda yan kannen ta maza da mama tahaifa a wanan gidan ke taya ta,
Har zuwa dare takasa aiwatar da abinda aka umuce ta tayi,
Gashi kuma Anty tace mata don Allah dai takira tayi godiya,
Ita kuma bata son a hadata da Allah tayi abu taki yin sa,
Saida tagama komai har yar fitilar kwan dake makale a dakin mama yau tasamu wanki ta kuma sa ancika shi da kallanzur,
Yau mama tadan ji dama don har ta dan dago daga kwanciyae da takeyi kullun,
Abincin da kishiryar ta tayi ne aka dan zubo mata awani plate na silver
Ta danci shi sosai don har tana, yar lasar miyar dake a kwano duk da bataci wani abu mai yawa ba,
Wayan ta tadauko, tafar lalubar nobar Yusuf da aka turo mata,
Yusuf yana tsaye a dakin shi na hotel shi kadai bayan fitar Jibrin wanda, suka gama shirin yadda zasu tafi gidan su, Safiya gobe,
Wanka yafito a lokacin yana dauke da wani dan farin towel a wuyan shi,
Karar kira ce tashigo mai, alokacin saidai bakuwar noba ce yagani
Kamar ya aje saidai kuma wata zuciya tace mai,
Amsa kawai kaji kowaye a wanan lokacin da duk wani mahaluki ke bukatar hutu,
Cikin yar siririyar muryan ta tayi mashi sallama,
Saibkuma tai shiru wayar yadan daga yagani ko ankashe ne ,,,
Amma sai yaji muryan muryan nacewa dazu kun dawo lafiya,
Nagode kwarai Allah ya saka da alheri Allah ya bar zumunci, sosai
Dama anty ce tace in bugo ma in maka godiya abin da kayi muna dazu din,
Murmushin da maganar ta yasa shiyi yasa tace nagode sai anjima,
Sai kawai ta kashe wayar nata batare da jiran taji ko da abinda zai ce,
Wayan nashi yakara dagawa sai ya wurgata saman gado yaci faba da taje gashin shi da yakeyi,
Sai mamakin zancen yarinyar yake yi nacewa anty ce tace taimai godiya,
Wata ajiyar zuciya ta sauke gami da fesar da wata iska irin ta relief din nan,
Bakin katifan da mahaifiyar ta take kwance ta zauna sai wani bala,in tausanyi ta yakama ta,
A hankali takai hannun ta asaman wuyar mahaifiyar nata sai taji da zafi, har yanzu,
Shin kodai malaria ne ya kama ta haka, ba wani kula, balle a yi treating,
Gawani ruwan kwata kusa da kofar dakunan su daje fitowa daga wani lungun gidan,
A zuciyar maryam tace gaskiya insha Allah gobe zan gwada gyara wanan gurin mugani ko zai rage aje ruwa haka,
Tana kojarin kwanciya sai taji wayar ta na kara, mamakin may kiranta a wanan lokacin tayi,
Don azaton ta ko A,A masugan ta ne yakira ta, nobar Safiyace
Zagi tafara jefa mata da iskanci yanzun ne lokacin kiran mutum,
Darita safiyan tayi tace ke dan Allah niki saurara koda yake ma nasan kin sani kawai dai zan fada maki ne dan karkice ban fada maki da baki na ba,
Gobe Jibrin yace zasu zo su gana da mahaifina, kafin ya koma
Wani irin dadi maryam taji, taitawa safiya din ba,a dakuma fatan alheri
Safiya tace amma dai zaki shigo gobe din ko,maryam,?
Maryam tace bani ma cikin gari safiya ina nan gurin mamana bata da lafiya,
Safiya tace cikin mamaki maryam mama bata da lafiya shine baki fada min ba,
A haka dai suka yi sallama bayan sun dan taba hira,a tsakani,
Tana aje wayar sai zancen A, A yafado mata wanda tun jiya takirashi taje sheda mai abin da baba yaxo ya fada masu gamay da maman ta,
Sauguda yakirata da safe yana tambayar ta koza ta dawo yau ne ,
Azaton ta ko zai ce zai tafine saitaji yace idan bazata dawo ba sai ya sani don kada yazo ace bata nan,
Tsuki tayi wanda har sai da mahaifiyar ta cikin dakusasshen muryan ta irin na marasa lafiya tace,
Baki ji dadin kwanci saman tabar ma ko yar baba,?
Sai alokacin matasan cewa idon ta biyu zafin ciwo ne kawai yasa ta yin shiru da lafewa,
Maryam tace mata aa mama mantuwa ne dai kawai nayi,
Daga haka har dan barci yadan kwashe ta tana maicike da jin haushin A,A wanda tarasa ko wace irin soyayya ce yake gwada mata,,,,,

Washe gari duk zancen boyar Allah da yagani acikin wahala ya cika mai zuciyar shi sosai, don da zancen ta ya kwana,
Sai karfe hudu na marance zasu tafi ganin iyayyen safiya,
Don haka, ya yanke shawaran cewa gara ya koma ya taimakawa matar yasa suzo asibiti adibata,
Maryam tana tsakar gidan saye da wani tsohon zanin mahaifiyar tasai aikin gyaran kwatan sukeyi tunda sanyin safiyar nan
Wani yaro yashigo yake cewa kishiyar mama wai wani mai mota yanawa, baba sallama a waje,
Kafin tabada amsa sai gashi yafito yana cewa guri nako aka aiko ka mai motafa kace,
Fitar shi ba,afi minti gomaba saiga su tare da Yusuf sun shigo,
Yana saye da wata bakar rigar sanyi a jikin mai kama da leda bayan shi, yasa wandon Jean's,
Mamaki ko rudewa yasa maryam tai saurin sake tsintsiyar dake hannun ta,
Tana kallon shi cikin mamaki,
Muyan mijin mamane ke kiran ta daga inda take tana wanke kafar ta,
Cikin sauri da ladabi ta isa dakin kara gaida Yusuf din tayi tana mai tambayar lafiyan su antyn ta,
Mijin mama yace maryama, asibiti za,akai mahaifiyar ki yanzu,
Don haka sai ki yi kokari kishiryata kada mu makara ko,?
Da mamaki ta waiga inda yake zaune kamar jiya, don har yau kujerar tana gurin,
Wani yaro ya shigo dauke da wani ckofin silver mai marfi,da kosai acikin leda yace wai ance ga kunin ki, inji mamana,
Karba tayi tace kace angode,ko kaji,
Cup din kunun ta aje agaban Yusuf tace ga kunu da kosai,
Sai ko taga ya aje wayan shi ya jawo kofin , sosai yasha kunun, yaraga mata saura,
Yana gamawa yatashi zuwa waje, don ya jirasu su shir ya,

ZEEE. MAKAWA
[3/7, 1:15 PM] ‪+234 803 381 3188‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
4⃣4⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA,
Chapter 67 · 0% Book details