← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 171

Sashe 66

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

ZEEE MAKAWA,,
[3/7, 1:15 PM] ‪+234 803 381 3188‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
4⃣3⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

Malam mijin mama yadan gyara tsuwar shi yadan kalli inda Yusuf yake zaune Assalam yana saman kafar shi,
Yace wasa wasa wanan abin tafara mata har sai,da ya kaita kwance daga karshe,
Yanzu dai an wanke mata makoshi ko zata iya cin abinci, koda kadan ne yafi zama haka nan,
Maryam wace ta kurawa mahaifiyar ta ido cikin tausayi don tasan ba karamin wuya tasha ba daga kwance,
Gashi babu wani kulawa na kwarai da take samu,
da ganin yadda ta koma,
Muryam Yusuf ya dan dawo da ita dai,dai, taji shi yana cewa,mijin mama,
May likita yace, sai da yai dan murmushi sanan yace andai kaita,gurin chemist an mata allura biyu,
Dan iska yafitae a bakin shi batare da ya kara magana ba yai shiru,
Tari mama tati mai kama da sarkewa,
Da sauri maryam tai kanta kamar zata, fadi tadan tallabo tana mai gyara mata kwanciyar ta,
Tace mata,, mama zaki sha ruwa ne, kai ta girgiza mata,
YUSUF ya mike kamar wanda zai fita waje, daya daga cikin multinan da suka zo dashi yadauko guda dama yana da dan sanyi ya hado da gwangwanin peak milk guda naruwa daga cikin kayan da suka zo dasu wanda kusan rabin yan gidan suna can tsaye daga gefe guda ana kidaya yawan abin da aka kawo,
Cikin dakin yadawi dauke da gwangwani mult da na peak,
Inda maryam take yadan kalla batare da yadaga idon shi garetaba ya ce,
Miko min cup mai kyau da spoon,
Maryam ta hau dan dube dube cikin dakin ko,zata samu wani cup ko kwano mai dan dama dama,
Wani kwanon sha na silver tagani can duk yadan yi kura shita dauko,
Gyalen da ke jikin ta ta cire, ta aje saman katifar da mama take kwance sama,
Da sauri tafita zuwa waje don daurayo kwanon
Sai yau, hannun shi taba jikin Maryam wanda yaji kamar ya taba kada,
Da kyat ya samu ya juye drinks din cikin kwanon sha
A hankali ya dago kanshi yakalli inda maryam takw tsaye sam ta manta cewa bata da gyale a jikin ta ,,,
Da sauri ya kauda idon shi gare ta saboda wani irin abu da idon shi ya hango,
Anya, Maryam ce kuwa ko dai idon shi ne ya hasko mai ita,
Yarinyar da yasani yar karama da ita, bata da komai yau ita ce ta koma haka, kamar irin yan matan hausawar da yake gani ana nuno photos din su a social median,
Ki bata tasha mu gani kafin mu san abin yi, daga fadar haka ya mike tsaye yana kokarin kama hannun Assalam dan su tafi,
Sun kasa kai kofar fita gidan yaji muryan maryam wacce bai masan cewa tana bi ye a bayan su ba,
Nagode sai anjiman ku, Assalam ku gaida Anty sai na dawo ko,
Takarasa zancen cikin muryan tausayi,
Wani irin tausayi yarinyar taba shi dubawa yanayin gidan yakara yi sai kawai yasa kai suka tafi,
Ita kuma ta juya takoma zuwa cikin gida inda ahaifiyar ta take kwance,
Ko wanan karon shi da kanshi ke jan motar komawa kwantagora sai gudu yake shararawa daga shi sai yan yaran guda biyu, aciki,
Tunane fam a zuciyar shi da tausayi ace mutum na irin wanan rayuwar ta talauci kawai zalla batare da wani damuwa ba,
Hannu yasa ya shafo sumar kan shi dake masa kwance ya wani furzar da iska, yadaki sitiyarin motar,

YUSUF ne a gaban Anty Dije wace ke mamakin jin cewa wai sunji kamfanin Bobi da kan su,
Sun kai maryam wai har sun dawo ga kuma yadda hankalin Yusuf ya tashi na yadda yaga halin da mahaifiyar maryam taje ciki,
Inda itama anty Dije nan da nan hankalinta ya tashi so sai , sai,matar ta bata tausayi,
Duk wanan labarin da Yusuf kewa anty Dije bai fada mata irin dawainiyar77 da yakai, masu ba,
Ranañ haka na ya wuni suku,ku baida wani ku,zari a jikin shi,

Jibrin ne ya iso garin saboda yasamu labarin cewa Yusuf yana garin kwantagora,
Da shirin shi ya shigo gari don zuwa ganin iyayen, Safiya, da yake son yi don a tsaida maganar si,
A,kofar gidan su jibrin suke tsaye sai ga Aisha, tare da, Amina,
Cikin wani irin shiga ba classic babies, abin har ya,wuce musali,
Kallo daya yai mata, yaji koda tsayuwa da ita wani zub da mutunci ne a gare don haka ya, tamke fuskan shi,
Cikin yar shagawaba Aisha ke cewa haba Joe ai bata karasa ba taji cikin wani irin murya yana ce mata
Don't ever nerve call me with that name again
Are out of your sense da zaki dan gan tani da wanan sunan a halin yanzu,
Duk wanda ke gurin a cikin mamaki suke kallon Yusuf wanda ke ta faman fada akan kiranshi da Joe,
Direct gurin motar shi ya nufa yana kokarin shiga don ya wuce,
Bakaramin kunya da nauyi Aisha taji ba saidai abinka da wanda ya bushe fitilar shi ,
Tsaye tayi tana yar dariya cikin nuna kulawa, kamar bada ita yai wanan disgawan ba,
Iam sorry na riga da na saba da kira hakane amna zanyi kokari in dai, na,
Jibrin ne ya samu yadan kwantar wa Yusuf da hankali wurin kokarin jan shi da wani hira,
Duk sallon yaudara da iya yi saida Aisha suka samu abinda suke so agurin Yusuf,
Kuma ya mai data gida, da kanshi duk da bawai hira sukeyi da juna ba,
Ita dai gurin ta dama mutane suce mata babban yarinya tunda har takai hurda da Yusuf,
Chapter 66 · 0% Book details