← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 171

Sashe 54

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Zazaune suke gaba dayan su a gaban,mai sudan, Inda mai Sudan yasa akara fadar abin da sukazo dashi
Yusuf na sauraren yai shiru saboda ladabi har lokacin da aka gama bayani akan komai,
Maimartaba ya kurawa Yusuf ido har nawani dan lokaci,
Sai yagano cewa Yusuf wayayye ne bazai ce Yes ba, yace No ba kuma
Don haka sai sarki yace mai samari kaji bayanin da iyayyen ka sukazo, dashi,
Zaman shi ya gyara cikin ladabi yakalli inda maimartaba yake, yace,
Assalamu Alaikum warahamatullah,
Sauran musulamai dake gurin suka karba mai kamar yafda sharia ta ce ayi,
Suko gaba dayan su suna jin wanan kalaman da ya fara magana da ita, suka dau da cewa
Emba, Juses crisis,
Oluwa, inji wani pastor yan olumba,olumba, yace cikin kada kai alamar takaici wai,,
Yusuf yace a gaskiya babu gaskita daga cikin zancen su,
Saboda ni yanzu nakai munzalin da ,zan daukar wa kaina duk abinda nake ra,ayi,
Heh Joseph come to your sense pls ?
Don't deceive your self
Magan ganu iri iri suka dan fara cikin, jin haushi da takai ci,
Nan da na fadawa suka daka masu tsawa dole suka natsu sukayi shiru
Yusuf yaci gaba dacewa,
Nazama musulmine ba tare da sda shawaran kowa ba,,
Ra,ayinane kawai yabani shawar gane hanya afificiya ta isalama,
Kai Na, lie, woo,
Wani bafade dake, kusa da mai maganar ya watsamai bulala tauuu,
Yace mai cikin daka tsawa behavi your self
Ganin haka yasa du natsuwa dole zuciyar su na suya
Yusuf yaci gaba da cewa, banzama musulumi ba saida nasamu kwararar hujjoji daga Alkur,ani maigirma,
Eyy,Eyyyy, he's finish wooo,
Abinda sukace gabadaya kusan lokaci guda ke nan,
Watau, Joseph ysi nisa har da Alkur,ani ya,yarda dashi,,
Yusuf yace saida na hada duk wani hujja wanda zanyi depending a kai sanan nida kaina nakai kaina wurin limamin central mosque na Abuja ya musuluntar da ni,
Saboda haka duk wani wanda ke zargin cewa wani ne yajani zuwa cikin islama ba gaskiya bane,
Ni YUSUF ban musulunta akan abin duniya ba ko mace ko aboki,
Na musuluntane saboda Alkur,ani maigirma,
Sai duk wanda ke cikin fadar musulumi suka dauka gaba daya dafadin Allahu Akbar,
Yace nakai lokacin da zan zabawa kaina abinda nake so daga addini, sana,a da kuma iyali,
Cheer, God wooo,
He, don go far,

A nan maimartaba yai masu warning akan cewa duk wani wanda ke son kawo mai fitina ko tashin hankali acikin kasa ashirye yake da yadauki mataki akan mai shi tunda har wanda suke magana yace ra,ayin shine shiga addinin da yakeso don yakai shekara talatin, yanzu,
Kuka sosai Mr Ema yadinga yi acikin fadar mai martaba yana fadin cewa a taimake shi amayar mai da danshi cikin Christianity,
Amma ba wanda ya bashi goyon baya haka suka tallabe shi zuwa bakin motar dasukazo dashi yana kuka, wi,wi,
Yana kiranan sunan joseph yana zuba gwalancin su,
Shiko yusuf dama yarigasu barin gurin don haka gidan Anty Dije yakoma,
Saboda yadan samu relief of mind, din shi sai,dai kana ganin yadda idon shi ya rine kamar garwashi zaka gane cewa, yana cikin tashin hankali,
Yadan dade yana waya da Alhaji sabo inda yake fada mai abinda yafaru dashi yau da mahaifin shi,
Maryam wace ke cikin bayi a lokacin tana jin abinda yake fadi har zuwa lokacin da yashigo ciki da rinanun idon shi,
Falo yazauna jagab saman kujera two siter dake cikin falo,
Maryam wace kafin yashigo,,tafito ko daga bayin
Tana cikin shigar atamfa, buje da riga masu ruwan multi, colour,
Dinkin yai mugun karban jikin ta kayan da tasane tai adon jin ma,a dasu, da rana,
Taso taje ziyara gidan su safiya amma sai taga yau Anty bata jin dadin jikin ta sai tafasa shine tashiga bayi ta gyara jikinta don tana fashin sallah,
Acan ne taji muryan Yusuf din yana waya dawani yana fada mai irin yadda yaji gamay da mahaifin shi,
Wani irin tausayin sa taji don tasan da zafi ace mahaifinka na kuka akan ka,
Inbadon addinin gaskiyabace kamar yadda Yusuf din yace da sai ya fasa yakoma gurin mahaifin shi
To amma ba,zai iyaba sam ya shiga isalama kenan har mutuwar shi acewar,
Bashiga bafita shiga sojan badakkare,
Tana bude labulen dakun tafitowa suka hada ido, ya sakar mata rinanun idanun shi da suka kada sukai ja ,
Kan ta, takawar gefe cike da jin tausayin shi alokacin,
Direct gurin fridge tanufa tabude tadauko kwalin madarar youghot mai sanyi mai hoton bafillata, na company Mrs Ghali, youghot,
Ta hado da cup din glass bata tsaya ba sai,gurin shi direct,
Ta, dan rage tsawonta ta fara zuba wa acikin cup din a hankali,
Sai a likacin yuduf ya bude idon shi dasuke lumshe yasauke su akanta,
Ta mika masa youghot din a hankali, batare da ce mata kala ba yakarba ,
Yakafa kai a hankali yana lumshe ido don sanyi da gardin youghot din,
Saida ya shanye glass guda a hankali ya cire cup din abakin shi murya kamar mai rada yace nagode Maryam,,,
Maryam ta mike daniyar barin gurin don jin ajiyar zuciyar da yayi,
Yace may ye sunan wanan madarar,
A, hankali tace Mrs Ghali, youghot,
Masha Allah yana da kyau,,,

ZEEEE MAKAWA

[3/11, 10:18 AM] ‪+234 808 968 1079‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
3⃣5⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA,
Chapter 54 · 0% Book details