← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 171

Sashe 120

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Jibrin ne yakira shi a waya yana mai complain akan KB wanda yanzu sam ya canza sosai,
Har zuwa lokacin da Jibrin din yakai karshen maganar shi Yusuf bai ce mai ufan ba,
Sai ma murmushin da yai mai alokacin da yaji cewa ya kai karshen korafin,
Yace Jibrin kafi kowa sanin halina a halin yanzu ,
Nai maku hanyar wanan business din ne don ku samu madogara har ku taimaka ma wasu daga cikin mutanen ku,
Tun a wanan lokacin ni ban kara damuwa ko wani irin hali kuke ciki ba ,
Idan har nace zan dinga bin didigin may kuke ciki da aiyukan ku ke nan badon Allah natai maka maku ba.
So kamai don Allah kafita batun shi kasa mai ido kawai , nadade da sanin irin halin da yake acikin tun lokacin da yai aure,
Addua kawai nake mai akan Allah ya sa ya gane gaskiya batare da yafada acikin halakaba
Kaiwai mu bishi da addua kaji pls ka dai na yiwa dan uwanka mugun fata,
Tsigar da yake magana ne yasa Jibrin jin wani irin nauyi don shi ya,kamata ace yai wanan maganar amatsayin shi na dan uwa kb da sukafito cikin kabila daya,
Nan yake shedawa Jibrin cewa ai yana kwantagora saboda yana son yai spending din sometimes with his Dad,
Wanka ya fada don ya dan ji dadin jikin shi ko zai rage jin kasalan da yada may shi, tun dazun,
Wasu kananan kaya yasa wando da riga duk bakake sai kwalar rigar ce kawai ke da ja,
Kamshi turaren shi na THE da JOJOBA yana nan kamar kulun,
Saida yafitane yasamu yadan ba masu gadin shi wmai dan ihi sani kamar yadda ya saba yi masu idan yazo,
Su ko sai addu,a suke zabga mai tankar yau yafara masu irin haka,
Indai har yana gari to sun yake talauci ke nan su sai dai kuma in bayan ya wuce,
Maryam wace a lokacin tana daki zaune tafito daga wanka tana saka riga don shiryawa saboda tasan cewa yau fita dole akan ta,,,,
Muryan shi taji yana sallama tuni zuciyar ta ya tsinke, saboda addu,an ta na fatan kada ya shigo bai ciba,
Muryan yaran Anty Dije taji suna mai sannu da zuwa tare da fada mai cewa zai fita da su da little Mum,
A tsorace maryam ta sake tsaki saboda yawan suruntun yaran da yai yawa,
Tau fa zuwa ina da daren nan yake tambayar yaran,
Suna hada baki gurin cewa gidan Anty Naimat, zamu tafi tare da little mum
Wani murmushi yayi mai sauti yana cewa cikin daren nan zaku bazaku bari da safe ba,
No, Uncle inji Assalam gobe akwai school bamu zuwa ko ina,
Idan mun fita sai na gama zan je nadauko ku ke nan,
Tsigar da yake maganar shi yasa yanayin maryan jin tsoro don tasan ceq zai zube su nan ne yatafi nashi tsabgar,
Idanu ta zare don tagona manufar zancen shi da sauri ta kalli agogo inda taga takwasa saura na dare,
Muryan anty ce ya katse ta tana cewa wai ina maryam ta zuba ma abinci,
Da sauri ta karasa daurin dankwalin dake hannun ta tun kafin anty ta balbale ta tafito,
Karan daurin zanin ta ne dake bada sauti idan ta taka yasa shi daga lumssasun idanun shi yadan dubi gefen datake tafiya,
Wasu shaddane jikin ta masu ruwan makuba dinkin fitted ne anyi aikin wuta akai an darza wasu duwatsu kanani suna walkiya,
Sai wasu takalma plat masu dan tudu kadan adudugen su,
Ganin shi zaune a cikin falin nasu alokacin yasa tai mai
Sannu da dawowa tace mai a takaice ta wuce abinta zuwa kitchen,
Mamakin iya kwalliyan wanan yar karamar yarinyar yake yi,
Yarinyar duk yadda tai kwalliya sai ya burge mutum,
Already abincin yana a cikin kula don haka daukowa kawai tayi takawo mai inda yake zaune,
Kai maryam har kin ban tsoro da,wanan kulan naki ,
Masan da naci dazu baiko gama aikiba fa yadda yai maganar saida kowa falon yai dariya har maryam din dake ta faman daure fuska,
Harara maikama da murmushi ta sakar mai ta gefen ido tace aiko tunda munyi dole kaci shi uncle,
Assalam ya jowa yana cewa zo ka tayani my son kada in kasa ccinyewa ni kadai,
Bayan tagama zuba mai dan kadan tamike tsaye ahankali tana mai kokarin wuce,
Sunan ta yakira a hankali yana mai langabar da kan shi cikin marairaicewa kamar dan karamin yaro ya na mai cewa haba little Mum ai wanan yai muna yawa,
Mikewa tayi gami da dan mai hararan wasa wanda yakarawa fuskan ta kyaun kallo,
Tace cikin yar murya irin nata,
You have to eat, it ,all so pls excuse me,
Da sauri Yusuf wanda sam ya manta cewa anty Dije tana gurin yai niyar kamo ta cikin wasa,
Maryam wace a zaton ta dagaske kamota zai yi sai ta dan zille mai tayi waje tana dariya ,
Wanan abin yasa anty dije cikin farin ciki amma sai tai kokarin boye farin cikin nata agaban su,
Don haka sai ta nuna cewa bata fahince shi ba takawo wani zance na daban,
Kwalaben turaren wuta anty bawa su maryam sukaiwa Naimat din,
Inda Yusuf koda bai gani ba afili yai murna sosai irin yadda yaga tana kokari da yar uwan nashi,

Wakan secret lover's ke tashi a motar inda Yusuf ke marming a hankali,
Yana tukin motar tankar wanda bai son tukin alokacin, a hankali,,
Wayar shi ce tai kara inda yaga kb ne bai fi minti biyar ba yakashe wayan,
Sai kuma ga kiran Jibrin ya shigo again, kamar hadin baki,
Yadai mutumina yace da ya dauki wayan, alokacin wankan dake tashi bai bari suji may yake cewa,
Amma dai taji lokacin da yake cewa gani nan da su maryam za mutafi unguwa,
Batasan ko may yace mai ba sai murmushin da taga ya dan yi,
Fuskanta na gefen widow tana sauraron abin da mawakan ke fadi gamay da secret loves, d two hearts dat beat together,
Kaman kada ya gama wayan sai wani irin annashuwa yazo mai a lokaci guda,
Muryan shi ya kashe ta yadda yaran dake bayan motar baza su iya jin ko may yake cewa ba
Maryam ya ambato cikin muryam maikama da wanda ke rada, yace,
Kiyi hakkuri da ni pls duk da nasan cewa bai kai matsayin da zaki soni a zuciyar ki ba
Badon komai ba sai don kasan cewa na tankar FUREN KAN JUJI,
Don banda wasu yan uwan da zan gwada wa alumma inyi alfahari da su, acikin su,
Kinga kuwa hakan zai sa duk wani mutum mai raunin imanani ya ji kyamar hada wani alaka dani kamar yadda iyayyen Sadiya sukai min ikirari da hakan,
Abin mamaki sai maryam taga kawai hawaye wasu na bin wasu a fuskan shi
Abinda bata taba gani ba a rayuwan ta taga namiji na kuka haka,
Itama maryam haka kawai batasan lokacin da hawaye wasu na bin wasu afuskanta cikin kukan tace may injiwa
Ni uncle bana kyamar yan uwan ka tunda mahaifana basu kyamace ka ba tun farko,
Cikin murya maikama da rada tace kawai dai malam A, A da mukayi nisa da shi nake jiwa,
Murmushi yayi daidai lokacin da zasu karya kwanar da zai sada su da unguwar su Naimat,
Hasken motane ya hasko mata motar A, A din tare da wata yarinya a tsaye hannu rike da na juna,
Yana saye da wani dinkin shadda light green
Ganin hasken yaimai kau a lokaci guda yasashi kokarin kate fuskan shi da hannayen shi,
Gaban maryam ne yabada damm kardai A,A karya yai mata dama,
A zaton maryam Yusuf baigane cewa A A din ta bane can suka wuce, a baya,
Wayan ta ta jowo takira layin wayar shi, tambayar shi tayi da ya isa lafiya ko?
Ya amsa mata da cewa a,a lafiya kalau har ma na kwanta,

ZEEE MAKAWA YELWA
[4/10, 6:23 AM] 0mmer Farouk: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
7⃣2⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI

IY,YA,NA,A ABBUDDU WA,IYYAKKA NAS,TA,INN,
Chapter 120 · 0% Book details