← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 171

Sashe 26

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Alhamdullah jerabawan su maryam yafito yanzu ,yaya I,lliyasu ya samo mata guri bi karatu,a FCE kwantagora, inda zata karanta bio,chemistry,
Maryam taji dadin wanan abin so sai ba maryam ba kawai har baba
Don har gida yazo yai ma Anty Dije da mijin ta godiya akan kula mai da yar shi da,sukeyi tsakani da Allah,
Maryam wandda yanzu girma da wayo yazo mata ta roki Anty ta barta taje gurin mamanta, acan Bobi kafin ta fara karatu,
Anty bata kiya ba saida tace sai ta fadawa baba don kada, yazo yaji daga baya yai fada
Baba bai,yi fada sai fatan adawo lafiya da yai mata yabata dubu daya yace tasai masu tsaraban man shafi da sabulun, wanka,
Cikin kwana biyu akai mata yan shirye,shiryen tafiya,
Duk da bawai maryan ta saba da mamanta bane amma dai tai ta zumudin zuwa kauyen,don tagane su,,,
Ranan da zata tafi tunda safe ta hana idon ta barci don zumudi,
Har saida Anty ta kasa kan,newa tai mata, magana
Maryam wai,dama dai ashe kin dade kina son yin wanan tafin ne ko,
Yar kunya taji da kuma nauyin Anty nata, saita dan sune kanta tace ,aa anty kawai dai ina son zuwa ne inga yadda garin yake wallahi,
Har inda zata shiga mota Anty ta rakata tare da yaran su,,
Inda yaran ke kuka sai sun bi little mummy su inda zata,
Shiru take zaune cikin mota sai tunane takeyi yadda zata riski mahaifiyar ta ,
Don dai tasan cewa zaman kauye na maida mutum iri, sai tausayin mahaifiyar ta ya,kamata
Tace Allah sarki mama ita kuma nan Allah yai nufin zaman rayuwan ta,
Haka tai ta tunane azuciyar ta har suka isa garin kamfanin,Bobi, saidai tai mamakin ganin garin a saman babban titin zuwa minna da kwantagora,
Tana sauka idon wa yanda ke zaune a bakin titi yayo kanta caaaaa
Wani yaro tagani ya tafiya sai,tai mai sallama nan take tambayar shi gidan liman hamza,nan yaron yai mata kwatace akan tabi wani dan lungu, zata ga wani gida mai katon icce a kofar gidan tashiga nan ne gidan, tana bi kuwa sai gata a kofar gidan,,
Da sallamar ta tashiga mata uku tafara gani su guda tana daka guda kuma tana duke tana wanki dayar kuma tana wanke wanken kwanoni,
Duk kan su daurin zani agaba, ga yara manya da kanani nan jagwal da su, wasu majina ahanci wasu kuma kunu ya bushe masu a baki har hanci,,,
Sun karba mata sallama cikin mamare ki wace don ganin tada sukayi da kaya a tare da ita,
A cikin ladabi ta durkusa har kasa tana gaishe su ,
Abin mamaki sai ganin mata takeyi suna bulowa daga wani dan lungu, ashe ganin tsoro taiwa gidan matane, ciki fam kusan su goma,
A cikin sanyi muryan nan nata take cewa, don Allah mama Rukaiyan saleh nake nema,
Wata mata wace ke daure da wani zani blue mai photo barewa ce tace taufa gani nan,
Sai wata wace ke gefe tsaye tun shigowar shin kodai Mamuce,,
Maryam tace maryam ce sai salati suka hau alokaci guda,
Suna murna da farin cikin ganin ta, cikin sauri suka fara kwasan kayan ta zuwa ciki dashi,
Maman ta tace a kai ta, dakin abokiyar zaman ta, wace suke cewa Ladi,
Anan akai mata masauki ita, da kayanta, kafin wani lokaci har an kewaye ta da abinci kala kala,
Da yake kauye ne duk sunyi abin sanar su tasayarwa,
Kwarai mahaifiyar Maryam taji dadin ganin Maryam, da kuma wanan ziyarar da takawo masu,
Bayan kowa ya watse akabar Maryam da mahaifiyar ta, a hankali maryam ta dago kan ta takalli mahaifiyar ta wace ke tsugunne a gefen dan gadon ta,,
Tace mun samay ku lafiya mama, cikin kariyar murya take maganar kamar wacce zatai kuka alokacin,
Mahaifiyar tace takauda kukan da cewa yasu wajen yayan naki ina fatan duk kuna lafiya ?
Kikara rike yar uwar ki da amana kin daiga yadda itama tarike ki amana,
Ba maicewa ga yadda kuke da ita ,don ko da nake nan ina jin irin zaman da kukeyi da ita
Duk wani abinda ta hore ki dashi kiyi kokarin rike shi,
Allah ne kawai zai iya saka mata da alherin sa,,
Saidan hiran sauran jamar su da sukayi inda take tambayar ta ko kwana nawa zatai masu ta sheda mata sati guda zatayi ta koma,
Daga karshe ta gabatar mata da tsaraban da tazo masu dashi
Nan mama tai filla,filka da kayan saida ta,tabatar dakowa na gidan yasamu tsaraban,
Maryam taji dadin zama tare da mahaifiyar ta duk da a kauye suke sam bata nuna masu kyama ko nuna wayewa,
Dan zamanta har da karatun addini suka dan samu daga gareta,
Duk safe za,a kawo mata abin kari daga ko wani shiya nagidan hakama da rana ko dare kowa da kwanon shi da zai aiko mata,
Ana gobe zata koma har daga makwabta aka dinga kawo mata tsaraba irin na kauye,
Badon sun so ba washegari tabar su takamo hanya dawowa ita kadai,
Tunda motar ta tashi sai taji zuciyar ta duk ba dadi ya cushe mata guri guda ji take kamar kada su rabu da su,,
Hannu tas tadan share hawayen ta da taji yadan gangaro mata,
Sannu a hankali sai gasu Allah ya kawo su cikin gari lafiya,
Chapter 26 · 0% Book details