← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 151 OF 171

Sashe 151

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sallama,sukaji daga kofan gidan azarin Yusuf su Jibrin ne amma kuma sai yaga ai matane,
Safiyace tai masu iso, da su karaso zuwa cikin gidan,
Dauke kowancen su take da robobin cincin da aka soya,
Har guda shidda ko wani roba da nau,in kalar abin da ke a cikin shi,
Tundaga dubbla guguru tsatsafa alkaki, dakuwa, da sai Donot, ,
Biyun wa yanda ba su kai shiddan girma ba naman kaji ne aciki soyayyaye,
Ba Yusuf ba har maryam din tana kallon wa yan nan kayan da mamaki,
Jibrin ne da KB suka karaso ciki tare da,sauran mata,
Matar mahaifin maryam kishiyar maman Anty Dije itace ke ce,wa Yusuf babane yace a kawo mai, shi da mahaifiyar maryam,
Yayi hakkuri da su saboda bai samu hadowa da kayan abinci ba abin yazo a girshi,
Kallon robobin yakeyi batare da yasan abinda ke a ciki ba,
Safiya ce tare da uwale, suka dinga bude robobin wani irin nauyi da kunya ne suka kama Yusuf a lokaci guda,
Maryam uwar kuka tana gefe idon ta ya wani ciciko da hawaye a lokacin,
Saboda tunanen da takeyi na cewa ina baba suka samu gidin yin wanan abin haka,
Tashi tayi tsam ta fada daki Yusuf wanda alokacin badon idon mutane ba ji yayi kamar ya rungumota,
Wanan matar mai magana na farko ke cewa sai zancen kayan gadon ta da sauran kaya zuwa gobe za,a kawo matasu gaba dayan su,
Cikin rashin fahintar zancen su Yusuf yafita inda su ma su KB da Jibrin suka bi bayan shi,
Fitar su yai daidai da mikewan uwale wace tabi bayan maryam din,
Zaune tasamu maryam abakin tamgamaymay gadon dakin,
Saida takarewa dakin kallo cikin kada kai ta zo gurin da maryam take zaune,
Jin shigowar ta yasa marya dan dago kanta idon ta taf da hawaye take kallon uwalen,
Tambayan da uwale tai mata yaba ta mamaki sosai,
Don ce mata tayi injin kin ta shiga ruwan zafi don tafiyan ki ya koma daidai,
Lokacin ne safiya ta shigo dakin ta wuce bathroom din nan ta kara hadawa maryam din ruwa masu dumi
Zaune suke suna hira har tafito daga bayin tare da dauro alwala,
Jikin ta yadan koma mata normal gefen safiya ta zauna, a,nan uwale ta shiga yiwa maryam din bayanan kissan zama da miji da yan uwan shi,
Tai mata bayani akan irin kayan matan da ya kamata ace maryam din tayi amfani da,su wanda zai kara mata haske a zuciyar mijin ta,
Uwale tace maryam nasan cewa ko a haka na barki bazaki taba wulakanta aidon mijin ki ba saboda Alhamdullahi kin samu duk wani horon da ya dace ki samu ga namiji,
Iyaka dai yadda zakiyi amfani da shine yanzu sai kin yi da gaske,

Yusuf yana fita waje tare da abokan shi yaja ya tsaya a bayan motar shi hannayen shi harde da juna,
Cikin marairaicewan murya yace wanan abinis too much for me,
Pls Jibrin ka gayawa baba cewa yadakatar da mahaifin su maryan hakana,
Matar da yaban kawai ya wadatar dani ga komai na duniyan nan,
Banda abinda zan saka mai dashi sai dai godiya saboda ya mai dani cikkaken mutum
Ya, bani macen da ban taba sanin cewa zan ita mallakan irin taba aruyawa na,
Da sauri su KB da Jibrin din suke kallon shi don jin abinda ya ce daga karshe,
Yadaga gira tare da kallon ido da ido yace mace kamila mai tarbiya ga mutunci da girmamana gaba wace ta rike darajan ta da martaban ta har zuwa ga mijin ta awanan zamanin ai tafi ko wace mace zama mafi daraja da kima,
Sun gane mai yake nufi da hakan gaba dayan su suka ansa da fadin hakane,
Don gaskiya Yusuf ya fadi irin wa yan nan matan matane na rufin asiri,
Don akasarin su da wuya ka samay su da wani matsala a rayuwan aure,
Dafa Jibrin din yayi yace mai ya kamata mu gagauta zuwa don baba ya samu wanan tsohon yai mai bayani yadai wani shirin kawo wa maryam kayan daki,

Mr Emanuel yana tsaye bakin kofar gidan shi rike yake da wani karfe da akatokara a tsakiyan gidan,
Motan Yusuf ce da ta shigo gidan yabi da kallo har zuwa inda ya parker ta,
Shima Yusuf yaji dadin ganin mahaifin nashi a tsaye alaman yaji sauki ke nan,
But ya bude masu aikin gidan ne sukazo da sauri suka fara fito da robobin da Yusuf ya,zo da shi,
Cikin gida suka shiga dashi shidai tsohon yana tsaye a kofa yana kallon su,
Bayan shigan su ciki sun zauna sai ga Samuel da Esther kaunar Yusuf sunfito,
Acikin yare suke magana tambayan shi sukayi da yare may ya kawo masu haka,
Esther ce ta bude robobin gani abin da ke cikki yasa ta fito da ido waje,
Mr Ema ke tambayan dan nashi kayan may wanan haka ,
Ba wani tsoro ko jin dari Yusuf yace wa mahaifin nashi wanda duk ya tsure shi da ido cewa
Kayan aure nane nakawo maku don kusa muna albarka akai,
Kafin ya karasa zancen shi yaji muryan mahaifin nashi cikin mashifa yace,
God forbids bad things,
Joseph are you out of ur mind,?
Sai da sauran yaran suka dan kadu saboda action din mahaifin nasu, irin yadda yayi,
Yusuf wanda dama yasan cewa za,a rina don haka ko gezau bai yi ba sai kallon mahaifin nashi yakeyi da addu,an shi abakin shi,
Maimakon fadan da Ema din yai niyar yiwa yaron nashi sai kawai daga mai hannu yana cewa park your things and go pls,
I don't want to see it here,
Esther wace ke tsaye daga kofa cikin wasu yan kananin kaya tace no, no papa ,
We want to test it ,
Is our brother weeding pop,,,
Kallon mamaki mahaifin nasu ke wa Esther din wace har takai ta fara daukan guguru guda tana kokarin kaiwa ga bakin ta,
Cikin wani irin daka tsawa uban yai wa Esther, magana har sai,da ta dan kadu,
Cikin dan turo baki tace me, i wan eater woo,
Tadauka takai ga bakin ta inda shima Yusuf, din yadan gutsura ya kai abakin shi ,
Samuel wanda ke gefe shima ya jawo nashi rabon a gaban uban suke ta cin abinsu suna hira hankali kwance,
Yusuf ya umurci kaunar shi da ta sam ma yan aikin su don suma su sheda,
Mr EMA wanda ke zaune murtun da fuska ya rike sandan shi ta sarautan su na IBO
Yace wa Yusuf yasan da cewa zai auri yar kabilad IBO nan bada dadewa ba,
Murmushi Yusuf yayi yace indai, musulmace may zai hana ya aure ta,
Amma idan ba musulma bace ba zai yi ba,
Duk mamaki maganar shi tabasu taya zai ce zai kara aure bayan yayi aure soon,
Amma rashin sani yasa su daukan cewa kila don dan uwan nasu yana musulmi ne,
Yadan dauki lokaci kadan ya bar gidan inda ya wuce ya kaiwa Abdulsamada nashi tare da Naimat,
Wace ke fama da laruran ciki a lokacin kamar za ta mutu,
Daga gidan ya wuce gidan Anty dije wace,kusan tun jiya baije ba,
Inko ba wanan dalilin ba ya za,a yi har ya kwana bai zo gidan na Anty shi ba,
A kofan shiga gidan yadan tsaya sai da yai gyara murya,tun daga nesa
Sanan ya kwada sallama kamar wani bako,
Jin muryan shi yana sallama a kofan gida yau,
Mamaki ya kama anty dije wace ke zaune tare da uwale suna ,zance akan auren,
Da sauri anty tamike cikin mamaki ta leka har kofan inda yake tsaye,
Bakin shi yana rawa yace, Anty ina wuni, ya gida da yara,?
Ikon Allah inji Anty Dije din,
Cikin mamaki tace Yusuf yau kuma a,waje zamu gaisa haka dakai,?
Murmushi yayi yadan sosa kai, nadauka ko akwai mutane ne acikin gidan,
Cikin girmamawa ya dan rusunna kasa ya ce,Ina wuni Anty ?
Ya gajiyan jama,a ?
Wanan karon bata tsaya ba juyawa tayi zuwa cikin gida tace,
Alhamdullahi shigo don Allah ba kowa uwale ce sai yaran ka,
Wanan ranan abinda Yusuf yai mata yabata mamaki don koma mata yayi tankar wani bako, a gidan,
Sun kusa kai wani lokaci a zaune Anty Dije da uwale suna kara bashi magana,
Ya mike cikin jin nauyi yana masu sallama,da niyar wucewa,
Ita ma Anty mikewa tayi a lokacin tana cewa Yusuf may yasa ka hana baba ya kaiwa maryam din kayan daki,
Bakin shi yana rawan bada ansa yace, Anty aiko bani maryam ta aura ba, zan iya yi mata komai daya dace,
Don Allah baba yayi hakkuri pls, ba wai na raina bane,
Duk ka duka kwana nawa zamuyi a garin kinga ke nan kayan ya zama, barnan kudi,
Anty tai murmushi ta gyada kai alaman hakane,
Har zai fita sai kuma yadan ja ya tsaya yace Anty don Allah ki ba wa baba hakkuri,
Akan zancen lefen maryam din sai na,koma Abuja sanan zan sa a hada mata komai kamar yadda ya dace,,
Yusuf , inji anty maryam tace wanan zance ai yanzu ba namu bane
Mafanar kace kai da matar ka don ita keda abin ta,
Yadda duk kukayi a tsakanin ku ya wadatar da mu don haka mu nan babu ruwan mu,
Godiya yai mata yai mata sallama akan ,ai tafi ,
Chapter 151 · 0% Book details