← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 171

Sashe 61

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Alhamdullah Yusuf ya kammala wani course da yadan kara tsayar da shi kasar Korea,
A harkan business ne dama ya tsaya don kara ita fasaha akan, kasuwanci
Don haka yanzu kimanin watan shi takwas ke nan rabon shi da kasar shi,
Duk abinda yakeyi yanzu hankalinshi yakoma gida Nigeria musan,man kakar shi wace yabar ta kwantagora, tare da Dad din shi,
Saboda yasan cewa babu shiri atsakanin su saboda banbancin churches din su, da suke bi,
Yasan cewa yan church din su Dad basu kaunar mabiya Olumbo,
Sonny ya na hankalce da Yusuf din duk kwanakin nan baya son walwala sosai,
Lafiyayyen abinci tare da abin sha daga yayan icce,aka hada masu a matsayin dinner yau,
Sai da Yusuf ya idar da sallah shi na isha,i tare da,shafa,i da wuturi,
Sanan ya koma yai wanka yafito cikin shirin shi,
Yayi mamaki Kwarai da ya samu Sonny a zaune yana jiran shi,,
Yusuf yadan bashi hakkuri tseda shi da yayi har zuwa wani lokaci,
Cikin daga hannu Sonny wanda,yake saye da wata far coth da wandon shi fari, sai bakar shirt da yasa daga ciki,
Yadan, dago wa Yusuf, hannu alamar ya share ba matsala, kawai,
Nan suka zauna suka fara cin abincin su hankali a kwance,
Saida suka dan dauki lokaci batare dayin wani magana ba sai karar cibin da suke cin abinci kawai kake ji yake tashi,agurin,
Sonny ne yadan dago kai yakalli Yusuf wanda dabi,un cin abincin shi yanzu duk ya canza,ba kamar da ba can, baya,
Murmushi mai sauti Sonny yayi wa Yusuf wanda hakan yasa shu dago kan shi yana mai kallon shi,,
Sai kuma ya daure fuska acikin yar damuwa yace,
Man this your religion is good, and have a nice characters,
Unlike Christianity,
Da sauri Yusuf yadago kai ya kalle shi,
Yace ma Yusuf man see how yo pray everyday,
Bayan yawan sallah da kuke yi a kullun, batare da damuwa da ko kowa ba, alokacin yinta,
Amma su Christian saudaya kawai suke zuwa church a cikin sati, inda wasu ma bawai dole su tafi ba,,
Littafinku mai tsarki muslumai dayawa sun haddace shi a kan su ,
Littafin ku mai tsarki Alkur,an, yana nuna abu guda ne ga kowani irin yare za,a fasssara shi,
Zaku iya shiga kiwani irin massalaci kuyi salkah aduk lokacin da ta riske ku
Ba kamar Christian ba suda da angan ka sai an tambaye ka wani church, kake zuwa a cikin sati,
Idan kafadi wanda ba nasuba, zasu iya bata rai, dakai afili,
Dazaran ance kai musulumi to daidai kake dakowa daga cikin musulmi, kuma a nuna ma so da kauna alokaci guda,
Sai kuma duk abinda ka iyayi dazaran kace Allah shikenan an yarda da zancen ka,kowace iri ce,
Amma su Christian dazaran kace God zaka zama abin zargi ke nan in ma bakai hankali ba sai antara ma taron,mutane,
A bincike ka, wani irin God, kake zance shi god din yan Catholic ne ko god din Anglicans, kona na living faith, kok, shin na deeper, life,
Duk da su ma musulmai suna da wayan nan akidodin a tare da su amma sai kayi nisa sosai a cikin su zaka iya ganewa,
Amma su kan Christian a filli suke nuna nasu,
Zaka iya jin ance maka ai jabun pastor ne wani
Banda musulumai da ko yaya imanin ka yake zasu iya binka sallah, a jam i
Gashi su musulmai aduk lokacin da suke azumin su na watan ramadam mai tsarki, duk duniya zasu sani sanan sauyi zaizo wa kowa daga musulmai har Christian alokacin wanan azumin
Amna baka taba jin wani abu maka mancin haka acikin bautar Christian,
Idan wani abin al,ajabi yafaru musulmai zasu yarda da cewa daga Allah, ne amma su Christian sai su ce wai in Jesus, name, wasu kuma suce karfin shedan ne,
Zaka ga idan mai wa,azin musulumai yana waazi, musulumi koda karamin yaro ne ya kewaye shi yana saurare har zuwa lokacin da za,a tashi koda kuwa mutum nada abin yi alokacin ba zai tafi ko ina ba, ko fitsari azasu yarda su tagiyi ba don kada afadi wani abinda basu ji ba,,
Idan ka lura da musulmi yana girmama pastor afili, badon komai ba sai don sanin cewa shugabane na addini,
Amma,su Christian suna jin haushin limamen musulumai sosai,
Yadda zaka ga musulmai suna girmama shugaban nin su sai kaga su Christian suna kokarin gardama da pastor cin su,
Kai abubuwa da dama nayi searching din su naga akwai bambanci halaiya so sai a tsakani,

Tunda ya fara dogon sharhin shi Yusuf yadakatar da cin abincin da yakeyi yana mai tsura mashi ido,
Acikin zancen Sonny din Yusuf yagano cewa akwai wani magana mai muhin,manci, da Sonny din ke son yi dashi,
Hakan yasa ya tatara hankalin shi gabadaya yana mai sauraren shi,
Yyana kaiwa karshe sai ya kalli Yusuf da kyau ya aje cokalin da ke hannun shi a cikin plate din da yake cin abinci,
Yakara duban Yusuf din sosai, yace a yar fahintar da nayi yanzu Joe nagane cewa muna da banbancin addini sosai ni da kai,
Kaga zancen mu hada harkokin mu kamar yadda muka saba ada bai taso ba ,
Kagane ko?
Yusuf yace,,
Fadi maganar ka kawai ina sauraren ka ai,,
Sonny yadan girgiza kai yana mai cewa don haka na yanke shawara nakuma rubuta komai a rubuce har an sa min hannu, cewa
Nabar maka duk wasu kaddarori da suke a hannun ka saboda nasan cewa kana bukatar taimako yanzu a rayuwar ka so sai,
Nayi hakane don in kareka daga duk wani barazanar da za,a yi kawo maka na cewa zasu iya gurgunta ka daga cikin har kokin ka,
Wata irin karfafan ajiyar zuciya Yusuf ya sake da yaji wanan zancen na Sonny,
Fuskan shi dauke da alamar damuwa mai fayyace mamaki aciki,
Magana Yusuf din ya fara cikin wata irin murya mai ban tausayi don duk mamakin wanan hukuncin na Sonny ya ruda shi,,
Kawai sai yaji Sonny din ya kaure da wani mahaukacin dariya alokaci guda,,
Sai kuma ya koma ya tsuke fuskan shi ya fuskanci Yusuf din karo na biyu yana mai kura mai ido cikin ido,
Yace may zakace min Joe, koka manta cewa da taimakon ka muka kai wanan matsayin da muke aciki ni da abokina
Inda Allah bai hada mu da kai ba ka dage har saida kaga mun gama karatun mu aida ba mu kai haka ba, ko ?
Mikewa yayi ya zagayo har zuwa kujerar da Yusuf yake zaune yadan duko yarankwafo zuwa gare shi yana mai magana kamar cikin rada,
Yace , don't say thanks pls,?
U deserved it
Yusuf wanda kanshi ke a duke don jin zancen yake tankar a mafarki,
Ya dan dago kai ya kalli Sonny din kara na biyu cikin mamaki,
Murmushi na gamsar wa Sonny din yai mai alamar eh,
Haka suka tashi gurin inda Yusuf kewa Sonny adduan fatan shiryuwa hanya madaidaiciya ,
Batare da sanin Sonny ba Yusuf ya gai,yato su jibrin tare da KB inda sukazo mai tare da,Abdulsamad,
Saboda yanzu suyake ji tankar yan uwan shi na jini,
Sunyi mamaki sosai irn dinbin dukiyar da Sonny ya tara a kasar mutane haka bayan ga kasar shi can na haihuwa suna bukatar shi,
Sun yi wa Sonny godiya sosai dafatan kara samun daukaka a dukiyar shi,
Shiko sai mamakin irin yadda suka dauki joe tankar dan uwar haihuwar bawai kawai saboda addini suke nuna mai haka ba,
Sosai Sonny yaji dadin zuwan su inda ya mai dasu kamar wasu manyan guest din shi,
Satin su guda sukadawo gida cike da farinci, dakuma alheri mai yawa,
Saida Yusuf ya tabbatar da cewa komai da ya turo su Jibrin da shi da KB sun kammalla mai
Sannan ya fara shirin komawa gida Nigeria, tare da karfin gwiwa atatare da shi,
Chapter 61 · 0% Book details