← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 171

Sashe 44

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

ZEEE MAKAWA
[2/21, 9:16 AM] ‪+234 806 595 8685‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
2⃣8⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA,,,

Tafe yake cikin motar shi baka mai kama da siffan wani kifin ruwa, motar bakace wulk da ita,
Yana rataye da yar suit shi a gefen kafadar shi sai hannu yake sawa yana dan sa,sau,ta nicktie, din shi, dake makale a wuyar shi,
Air freshness yake son ya dauko ya, dan kara fesawa motar shi don shi al,a,dar shi ce sa kamshi duk inda yake,
Dan save din motar yajawo daniyar dauko dan kwalban dake dauke da ruwan, freshness din,
Wasu takardu suka fado daga gurin da yajo kwalban,
Takardun da ya manta tun shekaran jiya ne a motar shi,
Ibrahim yake son ya ba ya cika wani form, da yake son ya,je gurin computer training,
A gagauce yadan fesa kamshin, sanan yajawo takardun ya aje a gefen shi ta yadda zai iya tunawa,don kada ya manta,
Bayan ya Parker motar shi, yafito a,gajeyi don tun safe suke vurin wani taro da,akayi,
Da takardun a hannun shi ya wuce zuwa dakin Ibrahim,
Har yasa hannu zai tura kofar dakin, sai muryan yaron yani yana rera katun alkur,ani mai girma cikin wata irin murya maidadin sauraro,
Maimakon ya shiga sai yadan tsaya har nakamar minti biyar yana da yaron ke fidda,harufan ya da ya dace a cikin natsuwa,
Juyawa yayi yakoma hanyar cikin gida don ba zaiso ya katse mai karatun dhi
Tunda bai san lokacin da ya farawar ba, balle kuma ya katse shi,
A,hankali ya tura kofan falon ba kowa aciki a lokacin sai TV dake ta aiki, shi kadai
Tashan wasu Christos ne wai peace TV, rawa suke kwasa da i,ho,ce,i,hoce,
Wani iri yaji aran sa kawai sai yaji haushin su ,daukan remote din yayi ya kashe TV,
A hankali ya fara tafiya a saman steps din da zai sada shi da bangaren shi sama,
A kusan hawan karshe maman Choima tafito saye da wani dogon riga kanta daure da dankwali ta tsuke shi tam,
Tace wa Joseph, So, you, are back,?
You na welcome, wooo,
Thank u mama,
Your food don ready since,
Cikin wanan turancin may kama da yare ta dinga jefo mai magana tanayi tana hadawa da,harshen IBO din,
Ruwa ya watsa sai a lokacin yadan ji zuciyar shi tadan rage mai suyar da bai san dalilin yin ta ba,
Yaso ya koma gurin Ibrahim don yai mai bayani amma sai kuma ya kasa saboda gajiyar da ya kwaso,,
Don haka baima,sauko kasaba kamar yadda yasaba, indan yadawo yakan je gurin mama su dan yi hira,
Don kawar mata da zaman kadaici duk da yasan Ejoma tana iya kokarin ta da yar tsohuwar,
Washegari, musalin karfe takwas na safe, Joseph yasamu ya sauko tare da takardun Ibrahim na jiya a hannun shi,
Dakin nashi ya nufa don yakai mai yasamu ya cika idan zai fita yau sai ya tafi dasu ya mayar,
Tun daga yar hanyar da zata sadaka da dakin Ibrahim zaka ji muryan shi rarara, yana karanta suratul Maryam,
Jin maryam mu da yake ambata aciki yasa Joseph tsayawa guri guda cif,
Yace a hankali maryam in ,Qur'an, ?
Ji kawai yayi yai kundunbale fadawa dakin yaga may yaron keyi haka,
Ibrahim wanda ke zaune kamar a tsugune can wani dan sakon gado yana rike da Qur'an din shi yana mai karantawa,
Jin kamshin turaren Joseph dayayi a dakin yasa shi dan bude indon shi da suke a lumshe,
Don ya tabbatar da kamshin da hancin shi ya shako mai na Joseph din shine agaban shi ,ko,kuwa,?
In ko har shi din ne to ko jiya ma da,dare da ya jiwo wanan kamshi tabbas shi din ne a gurin duk da bai bude ido yatabatar da hakan ba,
Daidai ya kai A,ya" yadan dakata kadan yana mai cewa Sadakallahul,Azeen,
Ina kwana yai mai acikin yaren su na IBO, Joseph ya dan daga mai hannu yana mai cewa,sorry for disturb pls,
Takardun ya mika mai yace mai, ya cikia inda bai gane ba yasa may shi yai mai bayani,
Daga haka yajuya kawai yabar dakin yana jin wani irin abu kamar kasala tana lu,lube shi,
Sai zakakkan muryam Ibrahim ke mai yawo a kunuwa shi kamar a ciki yake wanan karatun,.
Lumshe idon shi yayi yabi bayan kujerar da yake zaune yadan kwanta,,
Chapter 44 · 0% Book details