← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 171

Sashe 91

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Shine a tare da,Sadiyar shi zaune a cikkn motar shi,
Suna hira don tun da yazo garin yaune karo na biyu da yazo gidan su hira,
Wani kanin mahaifintane yazo zai shiga gidan nasu a lokacin
Ganin bakuwar mota akofar gidan na su ne yasa shi da,katawa bai shiga ciki ba kamar yadda yai niya, shiga.
Yaran yake tambaya ko motar waye a kofar gidan nasu,
Wani dan yaro cikin wasu dinkin yadi blue yaje cewa baban nasu ai anty sadiya ce da saurayinta,
Kamar ya wuce amma sai wata zuviya tace yahe yagani kowaye,
Ganin shi tafe inda suke yasa Yusuf yai saurin fito daga cikin motar
Har kasa ya tsugun na yana gaida kanin mahaifin nata dace shike bi wa mahaifin ta gurin haihuwa,
Bai karba gaisuwar da Yusuf ke mashi ba sai nuna shi da yatsu yakeyi,
Yace kai Sadiya ashe abinda ake fadi a kan ki gaskiya ne,
Yanzu ace kin rasa wanda zaki jawo muna sai wanan Furen Jujin,
Dam gaban Yusuf yafadi don jin sunar da aka kirashi dashi, wai FUREN JUJI,
Mutumi yaci gaba da fadin wa zaki jawo abin kunya ke da mahaifinki,
Don mutanen gari su ce kwadayi yasa muka baki Dan Ka Tuba, watau, (TUBBABE),
Kuka Sadiya tafara yi wi,wi don jin kanin mahaifin nata yafara nuwa Yusuf halin shi,na jahilai ,
Barin fada maki gaskiya badai acikkn zurian mu ba Sadiya,
Don babu mai kawo muna dan gin kafirai a gida wai jikoki,
Ya juya inda yusuf yake duk kai a kasa don ji yayi kamar kasa ta tsage ya shige irin yadda yake ji,
Yace wa Yusuf din tun wuri kaje ka bidi irin naka ba a gidan nan ba kaji,,,
Juyawa yayi ya shige cikin gidan nasu yana ta zabga masifa shi daya,
A, hankali ya juya bude mota yashiga Sadiya wace kanta yake a duke tana ta faman rusa kuka wiwi,
Da kyat Yusuf yai gyaran murya ya ce ta yi hakkuri tabar wa Allah komai yafi,
Ita ko sai hakkuri take ba Yusuf din cikin kuka tana mai mashi magiya cewa kanin mahaifin nata baida hankali sosai ne,
A dadafe sukayi sallama da juna yatafi zuciyar shi a cushe kamar zata fito mai,
Don irin cin fuskan da akai mai yai mai muni,har ji yayi kamar ba,zai iya tuki ba,,,,

Tunda yadawo yake zaune a falon shi ji yayi tankar kan shi zai tsage mai a lokacin saboda irin ciwon da yakeyi mai,
Ga zuciyar shi na mai wani irin soya kamar zata fashe mai,
Zaune yake asaman kushin ya mai da kan shi baya saidai kuma yadafe goshin shi da hannun shi guda,
Wasu hawaye madu dumi yaji sun gangaro mai a fusaka saboda tuna sunan da aka kira shi dashi, wai FUREN KAN JUJI,
Ya Allah ya furta a hankali yace Allah kai kasan dalilin yina a haka,
Nakuma gode maka ya uba giji na da ka bani ikon bin hanya madaidaiciya,,
Idon shi ya kara lumshewa yana ma zubbda hawayen bakin ciki,
May ye laifin shi a yanzu kuma bayan dashi da su duk matsayin su guda a gurin ubangiji,
Da wanda yai she kara dari da wanda ya shigo yau duk abu guda suke a gurin Allah subbahanahu, wata,ala,
Dangin shi kuma ko ya suke shi ba zai guje su ba saboda sune nashi,
Bai san ko daga cikin su akwai mai rabon shiga musulunci ba a ta dalilin shi,
Irin tunanen da yai tayi ke nan har dare ya raba tsakiya ya kasa barci, ga wani daci da yake ji a makoshin shi,
Sai zafi da yaji jikin shi ya fara yi kamar wanda fever ke shin kamawa,

Kiran wayan shi take tayi tun tana jin yana,shiga sai ya katse layin da kan shi,
Anjima kadan kuma takara kiran shi amma sai taji ya katse, wayan
Daga karshe ma sai taji kawai ya kashe wayan ma gaba daya,
Tsuki tayi ta wurgata da wayan ta kwanta taci gaba da zubar da hawayen bacin rai,
Tana mai Allah waddai da irin halin baba Ado wanda bai san darajan addini ba sai kuri da shi,
Ko a wani nafsi akace mai an kya maci auren wanda ya tuba
Ita dai a sanin ta baba Ado ya hada da al,adace kawai in bashi ba don mai zai kira Yusuf din da wai furen kan juji,,
Sai zuwa dare tayi taji kira ya shigo mata a waya lokacin har ta yi shirin barci, duk da tasan cewa yau ba zancen barci gare ta,
Jibrin tagani barobaro a wayanta, saida tai tsuki tadauka da fadin cewa kaga damar daukar wayan
Don kaga ina kiran ka shine harda kashe min layi ko,
Dariya yayi mata ya ce haka kawai zan yarda ki damay ni ga banza
Kuka ta farayi tana aheda mai abinda Baba Ado yaiwa Yusuf yau da yazo gurin ta,
Innalillahi kawai Jibrin ke ta nanatawa alokacin saboda maganar tazo mashi a ba,zata,
Yace wai ko dai da gaske Baba Ado bai da hankali kamar yadda mutane kece mai mahaukaci
Ra,ra,shin ta ya yi yace ta bari yaje gurin yusuf din yagani ko ya akayi,
Yusuf wanda alokacin yana can cikin bargo yana jin wani irin amai da zafi na damun shi,
Kuma duk yabi layin wayan shi ya kashe gabaya ba mai kiran shi ya samay shi a lokacin,
Jibrin gidan Yusuf din yazo direct don yadiba shi am.a sai yaga duk ko ina a kulle yake,
Dole yakoma badon yaso ba don yana gudun ya ta dashi daga barci,

ZEEE. MAKAWA
[3/24, 2:21 PM] 0mmer Farouk: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN, JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
5⃣7⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA,

Ya Allah mun gode ma dakayi acikin Al,uman Annabi Mohammad S,A,W,
Allah kaba ikon koyi da Sunnan a tafarki mai umfani,
Ya Allah katai make muslimi kasar Syria da ma na duniya baki daya,
Ameen Ya Allah👏👏👏👏👏👏👏👏👏
Chapter 91 · 0% Book details