← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 171

Sashe 62

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ànty Dije ce zaune a saman tabarman robar da ta shimfida a,waje saboda zafin da akeyi a garin tankar rana zai dafa mutum,
Gefen ta Abubakar ne a kwance cikin net na yara yana barcin shi hankali kwance,
Maryam ce ta fado gida a daidai wanan lokacin, cikin gajiya tashi gida da sallamar ta a bakin ta,
Anty Dije tadan daga kai, takalle ta gami da ajiyar zuciya,
Tacd don Allah maryam, huta kidan taimaka min muyi aikin nan,
Maryam wace tanawo wani farin kujerar roba dake aje a gefe guda, ta zauna,
Tace wai Allah ana dai zafi gaskiya, sosai shi yasa yau ma banko tsaya jiran safiya ba na sa kai kawai na wuto,
Kallon ta Anty Dije tayi cikin yar tuhuma kamar zata daure sai kuma ta kasa
Tace shi A,A din ya daina dauko ku ne yanzu,?
Maryam wace tambayar yazo mata a bazata,
Shiru tayi saboda ta rasa ansar da zata ba Anty Dije a lokacin,
Kara maimaita tambayar tayi wa yar kaunar nata,
Wacce dama duk kwanakin nan tana lura da bata acikin walwala tun lokavin da baba yazo da zancen ta,
Dan hawayen da take kokarin makalewa, ne yadan digo daga idon ta,
Ki tashi ki dauki abinci kici inji Anty saboda ta fahinci, cewa kuka kaunar nata take shirin yi,
Tausayin irin hanlin da yar uwan nata take ciki takeyi
Saboda ta san cewa tana cikin wani hali saboda so,
Maryam ta share hawaye ta da bayan hannunta ta mike zuwa cikin da kunar su,
Kallo anty Dije tabi bayanta dashi tana mai mata fatan alheri a rayuwa,
Fatan dai Allah yai wa Maryam din zabi na alheri, a rayuwa,
Tunda maryam tashiga ciki tana zaune, a bakin gadon ta ko, takalma bata cire ba akafar ta,
Wayar ta dake a cikin jakar ta ce tai kara alamar kira,
Kamar ta share kamar kullun saida tace bari yau ta dauka taimai kashedi ya daina kiran ta kwatakwata,
Cikin wani irin murya mai birkita maryam a duk lokacin da taji shi,
Wanda yasa gaba daya duk maryam din ta rikice, alokaci guda ta rasa duniyar da take,
Wani irin taji aranta na yadda sam bazata iya fada mai maganganun da ta shirya fadamai ba,
Maryam ta saki wani irin ajiyar wanda shima A,A din yaji kamar yazo inda maryam din take alokacin yabata hakkuri duk da irin kunyarta da yake ji,
Shima A,A din anashi bangaren ajiyar zuciyar don jin cewa maryam din tadan sauko daga fushin da ta dauki lokaci mai tsawo tana yi dashi,
Yakara cewa cikin wata irin murya ransarauniya maryam yadade ga A, A gaban ki tuba yake yi,
Murmushi ne ya subuce mata tai shi a hankali, duk yadda taso tai magana alokacin ta kasa,
Yace Maryam ina fatan zaki bani dama in zo in maki bayanin irin abin da ake ciki,
Shiru tayi saboda sam bata san may zai ce mata ba idan har yazo din,
Tasan dai bai wuce yace mata kawai tayi hakkuri ya aure su su biyu kamar yadda safiya tace yace,,
Wani irin ajiyar zuciya tasake tace, idan zuwar naka bazai zai haifa min alheri ba kawai kabarshi
Yar dariya tayi irin ta mazan da suka san kan su,
Ya Allah dai ya kai mu anjima ki dubi hanyata nagode,
Idan ta ta lumshe tanamai jin wani iri atare da ita
Ajiyar zuciya tayi mai fitar da sauti tana mai bude idon ta, da suka sauka a saman na Anty Dije,,,,,,

ZEEE. MAKAWA
[3/7, 1:14 PM] ‪+234 803 381 3188‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
4⃣0⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA,,,

Yan uwa musulmi barka mu da jumma,a , Ubangiji Allah yasada mu da Rahama da Albarkan da ke cikin wanan ranan,
Allah ka yafe muna kurakuraren mu Allahuma Ameen,👏👏👏👏👏👏

Sanye yake cikin wasu, fararen coth, da wani, farare, takalma rufaffu, kayan sun karbi,
jikin shi, sosai, sai idon shi dake saye da dan farin glass karami,
A hankali yake ta,kowa daga matakalar jirgin, guda ,guda, hannun shi,guda yana cikin aljihun wandon shi,
Jirgin su a airport din Lagos ya sauka, inda masu taron shi suka zo,,
Gurin screening yanufa batare da wani bata lokaci ba akai mashi, duk wani screening yadda yakamata,
Daya daga cikin driver s din da suka zo daukan shi yakar bi wata yar case da ke hannun shi,
Bawani bata lokaci su,kabar airport din shi da wa yanda suka zo tariyan shi,
Sannu a hankali yakarewa gidan shi kallo gidan da yakewa kallo tankar wani sabon guri da bai taba zama ba,
Saboda gyaran da ya turu da kudi akai mai,
Anan falon ya zube saboda yana tare da gajiya, ba abin da yake bukata sai ya dan watsa ruwa ajikin shi,
Ko zaiji dan karfi karfi ajikin nashi, kafin ya samu dan abin da zaici,
Motsin da yaji ne ya sanya shi saurin daga kai, don ganewa idon shi kowaye,
Hakan yai daidai da Ejoma, wace ke sauko daga wani dan steps da yafito wani part na gidan,
Da saurin ta tazo daniyar rungumar shi kamar yadda su ka saba idan yadawo koda gurin aiki ne,
Da sauri yadan jaye jikin shi daga gareta amma yana mai,mata murmushi,
Dan yaron dake rike a hannun ta ya daga sama cikjn wasa yana zagaya da shi,
Sauke yaron yayi yana mai kallon Ejoma wace ke saye da wani bakin buje da yafitar mata da surar bayanta baro,baro, gashi dan guntu, daidai iya katarar ta,
Ejoma ce tafara magana bayan taga ya, sauke yaron daga daga shin dayayi,
Tace brother we don base, woo,
Shima murmushi yai mata yana cewa where my grandma ?
Grand mother dey for village since, tree months ago,
Murya kasa kasa yake tambayar ta ya akai haka ,
Ejoma tadan tabe baki tukun sai tace,
You know Dad no dey allowed her to go to her church,
A dan tsora ce ya dago fuska cikin mamaki da jin mamakin zancen ta,
Saikuma ya maida mamakin nashi zuwa dan murmushi mai sauti, saboda tunawa, da sanin kowaye mahaifin shi,
Fuska kumshe da murmushi yace ma Ejoma is alright, i, will go and seen soon,
Daga haka ya haura zuwa sama inda dakin shi yake don yadan watsa ruwa,
Cikin daga murya Ejoma ke cewa brother your food is ready on the table,
Yakai wani lokaci a sama sannan ya sauko daidai lokacin da Ibrahim shima yashigo gidan, don taron shi,
Duk atare suka taru suka ci abinci, gabadayan su,
Tsab ya mike yashiga wani dan bayi dake makale a cikin makewayin,
Alwalar sallah azuhur yadauro alokacin amma saboda gajiya nan ya tsaya a falo saman sallaya,
Addu,oin da yajeyi bayan sallah ne ya gabatar alokaci har tsawon wani lokaci,
Brother are still bearing the Muslim,
Idanu ya zuba mata don mamakin kalamin ta, saboda yaji abinda tace kamar a mafarki,
Don haka ya shafa addu,an shi ya fuskan ce ta, da kyau,
Gyaran murya yayi yace mata dama ana canza addini ne anyhow,?
Sai ta girgiza kanta tace ba haka bane kawai dai taji Dad na cewa evils spirit din da suka shige shi har ya juya zuwa Islam,
An, kore su dakarfin addu,oin pastor's masu yawa daga cikin pastocing su,
Wani iri Yusuf din yaji a cikin zuciyar, wanan maganar ya kasance mara misaltuwa agare shi,
Shin dama ashe har yanzu Dad naga bakar shi na cewa sai ya canza addinin shi da yake ra,ayin yi a rayuwar shi,
Gaskiya zai dauki wa Dad duk wani mataki da yakamata yadauka wanan karo,
Ai bashi kadai bane, dan shi yafara zama musulmi, da zai ce ba zai hakkura ba ,
Koda kuwa Dad din zaiyi barazanar kwace mai duk wani dukiya da ya mallaka a rayuwar shi batare da yabar mai koda kwandala ba,
Ya tuna da labarin da Abdul samad yabashi, na,wani matashi , da yai zamani da manzon Allah S,A,W
Maisuns Mus'ab Ibn Umair, matashine, mai ji da kanshi a cikin garin makka,
Matashin ya fito daga wani family mai karfin arziki sannan,sannan ya kasance dangata sosai daga duk wani matashi na zamanin,
A wancan lokacin kaf samarin Makkah suns jin jins mashi wajen ado, don ko turaren ma dayake amfani dashi alokacin abin kallo ne,
Sannan mahaifiyar shi takasance mai tsananin sonshi wanda hakan ya haifar da shakuwa mai karfi gaske a tsakanin su,
Tufafin da Mus,ab Ibn Umair yake sawa, da takalmin shi masu matukar, tsadane so sai,
A lokacin da manzon Allah SAW ya fara wa,azi da kira ga mutanen makkah akan subi addinin Allah, watau musulunci,
Yawan wa,azin da yake saurare daga Annabi yaji ya gamsu zai shiga addinin islama.
Hakan yasa ya fuskanci tsanani da azaba da rashin galihu,
Inda yakoma yakassnce tankar almajiri, duk wanda yaganshi bazai gane shine shiba
Dan yadda ya koma ma abin tausayi don hatta suturar jikin shi duk sun yayyage,
Sai watarana mahaifiyar shi tace ya kai Mus,ab kadawo vikin addinin mu kafita,wanan addinin na islama, da kashiga
Amma sai Mus,ab yaki suka dinga azabatar da shi azaba mai tsanani, amma yaki ya tsaya akan addinin shi na islama,
Daga karshe ya koma gurin Annabi Muhammad, (SAW),
Ya hakkura da duk wani daular duniya da ake kwadaita mashi, anan
Chapter 62 · 0% Book details