← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 142 OF 171

Sashe 142

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Tunda safe babane ke sallama akofan gida jin muryan shi yasa kowa dake gidan tsinkewa saboda, ansa da akwai abinda ya kawo shi,
Daguda guda suka dinga fitowa har Safiya din wace ta kwana gidan don taya aminiyar ta jamame,
Sun gashe shi a cikin mutunci da kuma girmamawa irin yadda diya kewa iyayen su,
Baba wanda yake tsaye daga kofan shigowa yadan jim
Can ya kalli inda maryam take tsugune cikin zumbulelen hijabi, yace,
Maryam , maryam wace jin an kara kiran sunan ta yauma din tadago takai kallonta gare shi a cikin girmamawa tace Na,am Baba,
Yace Allah yai maki albarka kin ji Allah ya sa wa auren ki Albarka ,
Sai kuma yai shiru can yace ina Dije ?
Anty Dije takarba dacewa Na,am baba
Baba yace ban so ance jiya wanan yarinyar ta kwana gidan nan ba naso ace ta kwana adakin mijin ta,
Gaba dayan su suka dago kai suna kallon mahaifin nasu,
Yace na tuntubi shi malam mudi yace min abari har yaron yazo gari a ji ta bakin shi,
Don haka sai ki zauna da shirin yar uwar taki akan duk ranan da mijin ta yazo zata tare a dakin ta ne
Dafatan kin fahinci abinda nake nufi akan zance na,
Anty Dije ta gyada kan ta tare da cewa eh baba shiru yadan yi yana kallon su yace
Allah yai maku albarka Allah yabaku zuri,a masu albarka,
Daga haka yasa kai zai wuce, sai kuma ya juyo gurin da Anty Dije take yadan juya yace bani son samun wani matsala,
Anjima zandawo don muyi maganar dan abinda za,a sai mata,
Sai a lokacin Anty Dije ta samu bakin magana tun shigowar baba gidan,
Tace to amma baba bisa ga hukuncin da naji ka yanke na cewa da yazo ranan zata tare ,
Sai naga cewa ba,a fa yi wani shiri ba akan tarewan
Don may baza a dan dakata harzuwa lokacin da za a shirya,
Ke inji baba cikjn muryan da har saida ta dan razana yace,
Ni komai nawa na dogora ga Allah wani shirine can,
Abinda Allah ya hore min shi zamu kai mata tayi hakkuri yadda kowa yayi,
Ina fatan kun fahinta da magana na don kadaazo ace min ga kara ka itace,
Daga haka yasa kai ya wuce nan ya barsu a cikin tashin hankali,
Daki maryam ta fada sai kawai ta ji hawaye ya na silalo, mata daga idon ta saboda hukuncin da baba ya yanke a kan ta,
A daki maryam ce da aminiyar ta tana bata shawara akan tayi hakkuri da kaddaran ta,
Shawarwari da dama Safiya din ta dinga ba maryan har taji hankalinta ya dan kwanta,
Ànty Dije tun da tashirya tafita zuwa gidan wata aminiyar ta da suke siri
Duk da matar ta girmay ta sosai sai amma suna siri da mutunci a tsakanin su,
Saida taima matar bayanin abinda baba yazo masu da shi yau da safe,
Na akan lalai sai dai maryam ta tare duk randa mijin ta yazo garin,
Matar tai dariya tace wa dije wanan ai baika na ta da hankali ba,
Don haka yanzu zan dan fita in je in fara samo hakki bakin daji,
Anty Dije tace kai haba ke da anyi zance saiki maganar akan zancen gyaran harka,
Nizancen abinda zan wa maryam na gyaran gida da dakina ke magana,
Kai, matar ta kada tace aikin banza Dije, ai wanan abin shine babban tsaraba da yadace mugyara yafi wanan kayan banzan da kike zance,
Saboda ai shi kayan daki babu inda sunna yace an halattawa mutun shi ko ?

ZEEE MAKAWA YALWA

[5/3, 10:46 AM] ‪+234 706 262 3470‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
8⃣4⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI

Barka da jumma,a yan uwa Allah ya sada mu da alherin dake cikin wanan ranan,,,,,,,,,,
RAMADAN KAREEM👏👏👏👏👏👏👏👏👏

Kwance yake saman tafkeken gadon shi mai cin kusan mutun biyar,
Barci yake son yi saboda jikin shi akwai a gajiya, amma yakasa saboda tunanen da yasha mai gaba,
Kara juyawa yayi ko zai samu barcin yazo mai amma ina yakasa
Mikewa yayi daga kwanciyar dayake ya sauko da kafafuwan shi kasa a hankali,
Anty Dije ce ta fado mai arai agurin ta zai samu amsar damuwar shi,
Kan shi yadaga a hankali ya kalli agogon dakin goma saura nadare don haka baya son ya takura mata,
Balle ma matar aure ce duk kiran da zai mata da ranane ko kuma idan tana da magana itace kan kirashi da dare,
Gurin window dakin ya nufa inda ya yaye labule ya zuge glass din a hankali,
Wani irin fresh air ne ya shigo dakin a lokacin maidadi ya bude hancin shi ya shaki iskan ya dan lumshe idon shi,
Ya dan kai wani lokaci agurin tsaye yana kallon yan motocin dake wucewa a titin jefi,jefi,
Tsayin mintoci yana tsaye a gurin har na,wani lokaci sai kuma ya maida window yarufe kamar yadda yake da farko,
Bathroom ya shiga inda watsa ruwa da kuma dauro alwala, don yai sallah nafila kafin ya kwanta,
Wanan nafilan da yayi yasa shi samun relief mai sosai
Don yayi barci mai nauyi har da mafarkin wata,zukekiyar yarinya tana shayar dashi wani abu mai dadi a cikin cup din tankagaram mai daukan ido,
A daidai lokacin da yake kokarin dago kan shi ya kallo fuskan yarinyar sai kawai yaji wayar shi tana kuka acikin daren,
Cikin jin haushin wanda duk ya katse mai wanan mafarki mai dadi da shiga rai da yake yi, ya farka,
Hannu ya mika daidai gurin da wayan shi ke caji ya dauko wayar acikin kasala don duk jikin shi a mace yake jin shi,
Samuel ne ke kiran shi da sauri ya duba time karfe biyu da wani abu na dare,
Cikin sauri ya mustsike idon shi, babu abin da ya fado mai a rai kamar Dady shi,
Don har gobe yana mutuwar son mahaifin shi a rayuwar shi,
Fatan shi Allah ya nufi dad din shi da musulunta a rayuwar, shi,
Yana daukar wayan muryan Samuel din ne cikin daga murya yake cewa,
Brother Dad baia lafiya tunda rana yadawo daga filling station,
Yana kiran sunan ka yana cewa ,Na, lie, Joseph no, go, marry, just like that, yana ta shan giya, ko na karbe, sai ya ansa ya sha,,
Yanzu dai gashi har ta kai, jikin shi duk ya sake bai masan inda yake ba ga jikin tsufa,
Yusu ya ji wani irin zafin jin wanan mugun labarin a zuciyar shi,
Don haka ya rintse idon shi saboda takaici sai a yau yakara godewa Allah akan kwato shi da Allah yayi daga cikin kafirci,
Amma a fili cewa Samuel yayi zai turo likita ya duba mahaifin nasu,
Daga haka suka kashe wayen zuciyar bakikirin da jin wanan labarin takaicin da yayi,
Barcin da bai koma ba ke nan saboda wanan mugun labarin mai takaici da Samuel ya sanar dashi,
Yasan cewa ire iren wa yan nan dabi, un kesa wasu mutane suna masu gori masu karancin imani,,,,,,
Chapter 142 · 0% Book details