Sashe 88
Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Maryam ce tafito daniyar zuwa nan yar kasuwar bayan kwanar kuka don ta sayo yan abubuwan da suke bukata don yin abinci dashi tunda yace yau zai shigo,
Turus taja tai tsaye don ganin da tai masu akofar gida,
Cikin kasa boye mamakin ta take kallon su
Harara ya saki mata daga inda yake a tsaye yace shine taron da za mu samu ke nan ko, ?
A hankali yake kokarin takowa zuwa cikin gidan nasu,
Gefe maryam ta dan rabe mai don yashige,amma sai yadan kurawa maryam ido wace a ko yaushe cikin kara canza mai take,
Ya na zowa daidai inda take tsaye yasa kafar shi ya take mata yan yatsun kafar ta da takalmin shi,
Wani irin dan sautin kara, ta sake, a lokacin guda da sauri ta daga kai ta dube shi,
Amma sai taga bai ma ko kallon inda take, sai kokarin gyaran kwalar rigar shi yakeyi,
Murya na rawa tace wayyo ya Yusuf katake min kafa fa,
Har zuwa wanan lokacin bai nuna yaji may tace ba,
Sai wani irin zugu take ji a yan ya tsun ta,gashi sai kara matse mata su yake da takalman shi,
Zafi da radadi ke ratsa ta alokacin gashi shi yaki daga kai ya kalli ko da gefen da take tsaye ne,
Wasu hawaye masu dumi suka silalo daga idanun ta,
Takara cewa dan girman Allah ya Yusuf kayi hakuri,
Sai a lokacin dan sasauta mata kadan wani irn ajiyar zuciya ta sake cikin kuka,
Sai da ya hango Jibrin yanufo kofar shigowa gidan yai sauri yadan ja baya kadan,
Yantsun kafar nata, ta kalla sunyi wani irin ja jajir
A hankali ta dafa bangon dake gefen ta, tana bi a hankali cikin dan gyashi,
Nan da nan ya tsuke fuskan shi kamar bashi bane yai mun wanan muguntar,
A lokacin jibrin ya karaso gurin yana cewa an sauke kayan ga mutanen ka nan zasu shigo dashi, yana nufin samarin nan da ke kofar gida,
Sai a lokacin idon shi ya kai ga maryam wace ke kwalla, wahala,
What's going on here man,?
Tankar da dutse yake magana yake magana don ko kallon shi bai yi ba,
Kokarin wuce jibrin dake son jin abin dake faruwa ya yi,
Sai a lokacin maryam tace mugu kawai azzalu,,,,,,
Saboda yadda ya waigo ta rai a bace idon nan sun kada sun yi mai jajir
Matsowa yayi a hankali batare da yadamu da jibrin na gurin ba ya dan nuna ta da yar ya,tsar shi ya ce
Ki kiyayeni fa don bata maki tsari,
Bata son nuna kariya a gaban shi don haka sai ta dake acikin tsiwa itama tace mai
In dan ban ki yaye ka ba fa sai may?
Kai ya gyada mata yace ok haka kikace ko ?
Zaki san kin taba Yusuf maryam,
Ya wuce fuuu ciki yabar ta nan tsaye tana kara kallon yadda kafar ta yai wani jajir a lokaci guda,
Wani hawayen takai ci ya kara zubu mata a fuska ta sa gefen hannun ta takara sharewa,
Sai a lokacin ta sauke wata irin ajiyar zuciya wanda bata masan tayi ba,
Amma zuciyar cushe da mamaki da tambayar abinda taiwa yusuf yai mata wanan salon muguntar,
Da murna Anty Dije ta tare shi tana kuma yi mai korafi cikin harara,
A she saida kaga cewa zaka shigo gari shine ka kirani, ko,?
Yai yar dariya ya sosa kan shi da key din dake hannun shi,
Ai don kada in kara laifi nai ya sa na bugo maki lokacin muna bayan mariga kadan,
Kai Yusuf karage wanan gudun wallahi, mutun baya tausayin kan shi,
Shigowar jibrin ya sa tai shiru nan suka fara irin ba,an da akeyi a tsakanin matar wa da kanin miji,
Falo Yusuf yashiga ya zauna ya bar su nan suna ta shan matar juna a tsakanin su
Shigowar maryam yayi daidai da isowar ta da ruwa a cikin gora taba Jibrin
Batare da anty ta kalli fuskan maryam ba tace maryam ba Yusuf ruwa don Allah,
Jibrin yai sallama da su yana cewa zai tafi ya kai tsara ban da yayo gida don kada zafin buth ya lalata su,
Zaune yake saman kujera amma zaman balance yayi alamar yana tare da gajiya alokacin,
Tashigo falon batare da sallamar ba, duk kan shi na sama idon shi a lumshe bai hana yagane cewa ta gurin ba,
Saboda kamshin da ya daki hancin shi na turaren ta duk a ranan humrah kawai tadan shafa,
A hankalo ya bude idon shi ya sauke su gare ta, gutun hawayen dake makale a fuskan ta yai tozali dasu,
Subbahanallahi ya furta da sauri har saida maryam din tadan razana
Tana waigen bayanta ko wani abu yagani yake kiran suna Allah maigirma haka,
Cikin wata irin murya ya fara magana,
Dan Allah maryam kiyi hakkuri ki yafe min pls, ban san cewa zaki ji zafi haka ba har ki kuka,
Banza tayi da sai ta dangwar da tiren da takawo mai abin shan açiki gaban shi,
Tana kokarin mikewa yai yunkurin kai hannun shi da niyar ya rike ta,
Komay ya tuna kuma yai sauri ya jaye hannayen shi gare ta,
A,rau,nane yakara fadin don Allah dai maryam kiyi hakuri
Wallahi wasa nake maki saboda naga baki tare mu ba kina muna kallon mamaki, kawai, shine nataka maki kafa don ki san ba mafarki kikeyi ba,
Kala maryam batace mai ba sai mikewa da tayi tana kokarin barin gurin,
Haba maryam ina mun daina fada dake haka don may zan baki hakkuri ki kyale, ni,?
Ganin zai sa har anty taji ta dauka ko wani abin ne yasa maryam,
Tai saurin dagawa daidai lokacin da shima yadago sai jikin su ya gogi juna
Cikin sauri tabar falon batare da ta ko waiwayo inda yake tsaye ba,
Sai da yaga shigewar ta ya karkada kan shi yana murmushi don dariya ma ta bashi,
Sai gab da magrib ya bar gidan zuwa gidan shi don yaje ya watsa ruwa,