← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 171

Sashe 116

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shigowar shi gida ke nan a gajiye daga office da kyat yake dan iya cira kafan shi saboda gajiyan da ya kwaso
Don yau su Alhaji sambo sun shigo garin tun da safe suke zaune a na wasu lissafi akan harkokin business din su,
Saman kujera guda ya samu yazube gaba daya maman Choima wace ke zaune daga gefen shi guda ta wani kalleshi a yatsune ta kauda kan ta gefe,
Saboda wani irin matsanacin haushin Yusuf din da takeji a yanzu,
Yamai da kan shi musulumi yakuma mai da diyar mutane dake zaune a karkashin shi,
Pipkin ne ya sheko da gudu daga dakin da ya fito,
Yazo ya fada mai ajiki yana mai oyoyo da dawo wan uncle din shi,
Rugumay yaron yayi tsam a jikin shi yana mai jin wani feeling akan yaron
Shi har kullun wanan yaron tausayi yake bashi a irin yadda zai tashi ya rayuwa babu mahaifi a tare dashi,
Kara rungumay yaron ajikin shi yayi ya dauke shi cak zuwa saman dining table, inda ya dire shi,
Sai,da suka kammala cin abincin su ya kira Nani din shi taje ta kwantar da shi saboda school da safe,
Shima a gajiye ya haura sama don yadan watsa ma jikin shi ruwa,
Wayar shi ce dake rike a hannun shi yaji tana ruri,
Bakuwar noba ce yagani don haka sai bai dauki kiran da wani muhinmanci ba,
Sai bayan fitone daure da alwala don ka,idan shi ce yin hakan,
A lokacin da yake sallah ya dinga jin wayar ta shi kira nata shiga,
Sai da ya idar yadauko wayan misscall goma sha daya yagani duk da noba guda,
Sai da ya zauna yakira mai wanan nobar da bai san ko waye ba,
Bakuwar murya ce yaji wanda bai san kowaye ba, ya karba mai sallamar shi,,
Tambaya yayi ko waye a layin tare da shi don bakuwar noba ce a gare shi,
Ansa aka bashi a dayan bangare da ce wa, hello don Allah da Joseph Emanuel nake magana,
Murmushi yayi kawai inda ya karba mai da cewa eh dashi kake magana,
Ok inji mai wayar yace kana magan da Aminu ne dan gidan, masuga dake a unguwar jankidi,
Look Joseph ina son sanin inda yaron da Ejoma ta taba haihuwa ne yake,?
Shin macce ce ta haifa ko namiji ina kuma yaron yake, ?
Tsuki Yusuf yayi baiko gama jin bayanin ba ya kashe wayan ,
Komawa yayi bakin gado yazauna ya mai harde hannayen shi a cikin juna,
Maganganun da,wanan guy din yayi a lokacin ne suke dawo mashi a rai,
Abubuwan da yace a gamay da Naimat din a wancan lokacin sune abinda ke mai yawo akai tankar yanzu akayi su,
Mikewa yayi zuwa downstairs dakin da Pipkin ke kwance ya turo a hankali,
Inda ya hango yaron a kwance cikin sleeping dress din shi fare masu dan adon pink colour,
Tsayawa ya yi daga kofan daki kafan shi a harde yana ma yaron wani kallon cikin tausayi,
Yasan dama something wrong zai faru da yaro din shi yasa duk kwanan na yake yawan tunanen al,amarin yaron,
Yadade gurin yana kallon dan yaron dake kwance dunkule a saman gadon shi yana barci,,,,,

Maryam wace ke jin cewa duk duniya ba mai son ta a wanan lokacin saboda babu mai kaunar farin cikin ta ashe,
Ba wanda yafi bata mamaki ga wanan al,amarin kamar Anty Dije wace, taki aiwatar da komai akan zancen,
Don a zaton ta Anty Dije zata iya shawo kan mahaifin ya yi hakkuri da zance hada ta da Yusuf da baba ke kokarin yi,
Idan har suna ganin cewa baba ya zai hada tane da Yusuf don wani ra,ayin kan shi to lalai sunyi kuskure sosai, da yin hakan,
Ita dai sam zuciyar ta yaki amincewa da zance Yusuf din akanta,
Mutumin da tun tsawon sanin shi da tayi babu wani zancen so ko makamanci soyayya a tsakanin su,
Shine yanzu za,a ce wai ta aura a matsayin mijin auren ta,
Yusuf din nada abubuwan da mata da yawa ke so a gurin namiji a rayuwar su,
Amma ita sam wa yan nan abubuwan basu burgeta haka kawai take jin tsanar sa,
Yanzune ma da suke dan sabawa a hankali tarage jin wanan tsanar da take mai,
Wanda tun farko ya samo asaline tun lokacin da yake dan mabiyi addinin Christian,
Tun alokacin take jin batason al,amarin shi a rayuwar ta,
Wasu hawayen ne masu zafi suka kara zo mata wanan karon, bata damu da wai ta goge su ba,daga fuskan ta ba,,
Jin alamar shigowar mutum a dakin baisa maryam wace ke kwance tana sharban kuka, dagowa ba,
Gefen gadon ta samu ta zauna takai wani lokaci ta kurawa kaunar nata ido sosai,
Tawani ramae acikin dan kankanin lokaci, tayi baki ga kukan da tasawa kanta duk ya wani kumbura mata ido,
Duk da farko tausayi take bata yanzun ganin da tai mata yasa ta jin tausayin ta sosai,,,,

SEENABU MAKAWA,
[4/7, 6:57 AM] ‪+234 703 981 8283‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
6⃣9⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

MA, LLIKI,YU,MMIDEEN,,,,,

BARKAN MU DA JUMMA,A YAN UWA MUSULMAI,,,ALLAH YA SADA MU ALHERIN DAKE A CIKIN WANAN RANAN
ALLAHUMA AMEEN👏

Hannun ta takai a hankali tadafa yar uwan nata dake a kwance tankar wace bata a cikin hankalin ta,
Sautin kukan na, ta ne tasake gaba daya a lokaci guda,,
Jawota Anty Dije tayi zuwa jikin ta itama hawaye takeyi saboda tausayin yar uwar ta,
Murya irin ta mai kuka Anty Dije tace, Maryam ki daina wanan kukan haka kada ki jawa kanki matsala,
Don dai kin san halin baba ko waye, mutun ne wanda bai magana biyu,
Kamar yadda ta fada maki cewa ke din tausayin ki ne yake ji har yasa kika samu fagen mai musu,
Ina son ki kwantar da hankalin ki kin sai dai cewa aure na Allah ne ai,
Kika sani cewa ko wani matsala yazo ya hana ayi auren,
Kamata yayi ki barwa Allah zabi akan al,amari ba wai ki kama butulce mashi ba, irin haka da kike yi,
Maryam sam banso tun farko har ki bari Yusuf yagane cewa ba kya son shi ba, haka,
Shima da ba wai baba ne ya haife shi ba ya daure ya nuna boyewar zuciyar shi,
Don may ke da baba ya haifa zaki kasa daurewa ki nuna biyayyan mahaifin ki,
Sai a lokacin ne maryam ta dago idon ta dake face face da hawaye ta kai kallon ta ga Anty nata,
Anty yakike son in yi da abin da raina baiso Anty ban taba jin cewa ina son uncle da soyayya ba arayuwata, tun farko,
Daukar shi nayi a cikin mu tankar wani dan uwar mu,
Amma Anty taya za, ace wai ni dangin mijina duk kafirai ne,
Da sauri Anty Dije ta dafe mata baki kafin ta karasa zancen ta,
Da cewa Assha maryam kin san abinda yasa Allah yai wanan hadin a tsakanin ku,
Kin sani ko shigar ki cikin su zai kawo sanadiyar musluntar wasun su,
Maryam Yusuf mutum ne wanda ke bukatar mace wace zata ba shi kulawa,
Saboda yana cikin maraicin rashin yan uwa na sahihi a tare da shi,
Yana son mace mai mutunci da sanin ya kama tane bawau irin wa ancan matan da suka laje mai don kwadayin dukiyar shi ba kawai,
Wani irin kallon tuhuma maryam ke aikawa Anty ta don jin wanan maganar da ta,jera a lokaci guda watau ke nan Anty ce ta ke son wanan hadin ko ?
Saboda son Yusuf din da takeyi tan,kar wani jinin ta can,
Wai may yasa Anty Dije take son al,amarin wanan bawan Allah haka ne,?
Muryan Anty ne ke cewa maryam kinfi kowa sanin cewa bawai don abin hannun Yusuf nake ra,ayin shi ba, ko ke da shi,
Tadan girgiza kanta cikin ban tausayi ta ce kawai don kyawawan halaiyan shi ne na alheri,
Wanda tun farko na hango su daga gareshi amma baida mataimaki,
Kanta takawar daga kallon yar nata, a lokacin da taji haka din,
Wani irin bakin ciki ne ya tokare mata zuciyar ta ta rasa yadda,zatayi da,shi,
Komawa tayi da kanta saman filo tana mai kallin silin din dakin a hankali ta lumshe idon ta saboda tuno wasu abubuwa da dama a zuciyar ta da tayi,,,,,

Kusan kwana nawa Yusuf bai kira yan dattijan da suka maye mai gurbin mahaifin shi ba gurin sa ma albarka da fatan gamawa da duniya lafiya,
Mahaifin jibrin ne ya fara kira inda suka gaisa a cikin ladabi da biyayya,
Sun dan kai wani lokaci yana mai bashi hakkuri da duniya, da mutanen cikin ta,
Sai kuma malam Abdulsamad da yakira shima kusan irin yadda sukayi da mahaifin jibrin ne sukayi da shi,
Sai kuma yai niyar kiran mahaifin Anty Dije wanda dattijon ke burge shi saboda irin halaiyar shi na sanin mutuncin mutane,
Da gaisuwa ne suka fara magana da mahaifin na su Anty Dije,
Inda yake mai magana kamar nasiha akoda yaushe,
Anan yake sheda mai cewa ya yi kokari ya shigo ya duba mahaifin shi,
Ya daina dadewa baizo gurin shi ba saboda hakkin mahaifa ya na a kan shi,
Sosai Yusuf yaji dadin wanan nasihan na baba shi yasa shi har kullun yake sun al,amarin wannan tsohon,
Ya kai wani lokaci, azaune gurin da su ka gama waya da mahaifin su anty dije din,
Hannun shi bibiyu ya tallabo haban shi da su yana mai tuna nen yadda zasu kwashe da mahaifin shi,
Murmushi yayi shi kadai don sanin cewa sai sun kwasa da mahaifin nashi,
Wanda har zuwa yanzu bawai ya hakkura da zancen shi bane,
Amma ya zai yi dole ne ya bi zancen dattijon nan don neman albarkan,mahaifa,
Chapter 116 · 0% Book details