← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 171

Sashe 31

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Shiko Joseph yanzu yakai kusan wata, hudu a can
Har kasar chaina, yake tare da wani abokin karatun shi,
Cikin dan kankanin lokaci mr Sonny, da suke tare ya dan kara gwada mai wasu yan dabarun kasuwan ci,
Allah da ikon shi ya kara daukaka shi sosai, ga harkan business,
Ga harkokin shi na Nigeria su ma suna ci gaba,
A, sannu yasamu ya kulla, a,laka da wayan nan mutanen suka yarda zasu zo Nigeria su kafa irin wanan masana,antar,
Wanan harkan duk ya,samay shi da ga taimakon da hamshakin maikudi a kasar IBO yai mai hanya, abokin karatun shi
Wanda tun kare karatun su shi yana can zaune yana harkokin shi, da turawa da chainawa,
Mr Sonny shine ya basu sunar Joseph saboda yabawa da hankalin shi da yayi,
Don tun a can da yasan halin Joseph sosai da rikon amana,
Abin mamaki,Joseph nadawowa,da wanan harkan,
Saiga shi ya dauki yaran hausawa cikin ma, aikatar company da aka bude Bunue,watau makurdi, wanda su yan kabilar su sam basu so hakan ba,

A, bangaren su maryam da Anty dije kuwa,
Tun bayan tafiyar wanan tsohon sai maganar tazauna ma maryam a zuciyar ta
Tunane takeyi ta yadda zata fara aiwatar da wanan shirin kamar yadda aka basu shawara, su tallafa mai,
Don haka tasawa zuciyar ta cewa zata bada nata gudun mawar amma ba tare da sanin kowa ba,,
Don haka shiri na farko da tafara yi shi sayen sabon sim card na layin,MTN,
Sabanin wanda kowa yasan ta dashi a da tana amfani dashi,
A cikin wayar anty Dije ta samu nobar wayan shi tai serving a sim din ta,,,
A wani dare bayan ta gama komai tana shirin kwanciya ne
Sai zance malam Abdulsamad yafado mata arai,
Tashi tayi tsam daga inda take kwance,ta dauko wayanta,
Ta rasa may zata rubuta da farko,sai can wanan
Sakon farko da tafara tuwa shine,
Come to the light of life, islam,,,,,
Joseph dake zaune yana searching din wasu kaya a cikin laptop din shi yaji sako ya shigo mai a wayar shi,,
Kamar ya share kada ya karanta saidai ya mika hannun shi yadauko wayar, a hankali,
Da niyar,yadan diba sakon yaci gaba da aikin shi,
Sosai yai mamakin ganin wanan sakon awayar shi batare kuma da da sanin mai nobar ba,, Nan da nan duk wani abin da ke gaban shi ya dushe mai,
Kafin wani lokaci idon shi ya kada yai jajir kamar yaci gauta ja,
A hankali ya runtse idon shi, yana sauke numfashi a hankali, ya fida wani huci ta bakin shi,
Tsayin lokaci babu abin da ya iya yi ko tunawa, wayar ya kara dauka ya diba sakon,
Ahankali, maganar mahaifinshi ya fado mai a rai,
Inda yake yawan ce mai hausawa basu da kyau, don wata rana zasu iya canza ka Joseph,,
Sai kuma inda Mr Ema ke cewa kadaina yawo da yaran hausaw don basu da tabbas,
Cikin wani irin yanayi ya aje wayan kamar mai tsoron wayar, na shi alokacin,,,
Da kyat ya iya mikewa zuwa cikin bedroom din shi jikin shi,duk ba kwari,
Duk da ya kwanta da ya runtse idon shi ba abinda yake gani sai wanan sakon na wayar shi,
Come to the light of life, islam,,,
Rintse idon shi ya karayi kamar wanda bai son tunawa da sakon,
,,,,,,
Maryam wace ke zaune bakin dan matsakaicin gadon su ita da Issalam,
Takai wani lokaci tana jiran replay din shi saidai taji shiru ba wani alamar da wani sako tafe,
Haka ta hakkure ta kwanta tare da tunane kasadar da tayi na tura mai wanan irin sakon duk da tasan cewa ba wai zai gane cewa ita bace,
Amma dai tasan cewa kasada ne haka din, don ina ruwan ta da addinin shi,
Tsuki tayi gami da juyawa tana may ganin laifin kanta, dayin katsalandar da shiga harkan da ba nataba,
Sim din tacire a hankali ta samu wani guri inda tasan cewa, ba mai taba ganin shi gurin, taboye
A hankali taja bargon ta dake gefe aje, tai rufe jikinta da shi ta,na mai lumshe idon ta,
Sai dai sam barci yaki daukar ta don tana tunane akan sakon da ta tura,
May ye,wai, amfani abokan shi su jibrin da KB da bazasu iya fadakar da shi gaskiya ba,
Tsuki tayi gami da kara juyawa ta wani gefe tanamai cewa
Ina zasu iya fada mai gaskiya tunda suna samu kudin agurin shi a kai a kai,
Wai may yasa mutane kudi ya rufe masu ido ne haka da yawa,
Kudiba fa, ba kunya yadda suke rawan kafa akan ARNE, wanda suke darajawa da kiman,tawa saboda kudi,,,
Shin wai basu san cewa shi kanshi yasan cewa sun fi shi daraja ba da kima mutunci, saboda hasken addinin su, yafi na shi,,,,
Amma saboda kwadayi duk sun zubar da damar tasu,
Kara jan bargon ta tayi ta lullube lif daga haka barci mai nauyi ya dauke ta, zuwa wata, nahiyar,,,,,

A,A masuga ne zaune a office din shi yai tagumi da hannun shi, guda ,
Ba komai yake tunane ba sai wanan yariyar da yafara ji a, cikin zuciyar shi,
Watau Maryam wace duk wani tsari da kuma diri da yake bukata ga mace tana dasu,,
Kafin ya kai karshen tunanen shi yaji an turo kofan office din nashi,
A hankali yadago kai da idon shi da suka dan sauya yanayi yana mai kallon kofar ,
Da sallamar ta ta,shigo office din cikin shigar atamfa, da dan hijabin ta mai kara mata kyau ko yaushe,
A nutse take kamar kullun yau madai kamar ba sabo a tsakanin su har yanzu,
A mutunce ta dan durkusa ta gaishe shi, sannan ta dan samu kujera guda ta zauna,
Sai a lokacin A,A yadago ido ya zuba mata su kamar na yan mintina,
A kunyace maryam ta kauda kanta daga kallon shi, saboda bazata iya jure kallon namiji ido da ido ba,
Yar murmushi yayi har fararen hakoran shi suka dan baiyana fili,
Magana yake yi mai kama da rada,maryam kina kokarin ki min illa a wani part na jikina,
Cikin dan razana da dago idon ta,akaro nabiyu suka kara yin arba da juna,
A,A yace yes, ba wai, ba gaskiya ce nafada, saboda duk second ina ganin ki a zuciya ta Maryam
Cikin mamaki maryam tace mai malam ni kuma ? ta fadi cikin sanyin murya,,
Kai yakada mata a hankali, yace akwai wata maryam ne nan a tare da ni,
Ido ta dan kura mai sai kuma tai saurin kawar wa , azuciyar tako tace ban taba tsan manin cuta da ga gare ka ba malam,
Ansar da yaba tane yasa ta gane cewa zancen zuci ya fito fili,
Don ji tayi yace har abinda yafi haka zaki iya ji daga gare ni ai,
Zan cena sam babu maganar cuta ko yaudara acikin ta,
Gaba daya suka kurawa juna ido cikin dan mintina,
Maryam ce tai saurin kawar da na ta idon again
Saboda in badon a zaune take ba da zata iya faduwa don kaduwa,
Sannu a hankali A,A masuga yaciga bada kafa gwaunatin shi a zuciyar maryam,
Cikin jin kunya da kuma nauyi Maryam tai mai sallama daniyar wucewa yau ita kadai,, don dai wani irin nauyin malam din take ji yau,,,,
Tafe suke ya na,takara kafa gwaunatin shi gare ta, ita ko har yanzu ta kasa gaskan ta zancen nashi a cikin ranta,,,,

ZEEE. MAKAWA
[2/20, 10:28 PM] ‪+234 806 595 8685‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
2⃣0⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

Masoya novel din furen juji ina maku fatan alheri aduk inda kuke ina kara maku fatan gamawa da duniya lafiya ,
Rahama ,daukaka azurta,dacewa da alheri ubanginji Allah ya hada ku dashi,
Don nasan cewa bawai novel din kuke kauna ba kishin addinin mu ta isalama yasa kuke kaunar novel din, fatan alheri gare ku ko yau she👏👏👏👏👏👏👏👏
Chapter 31 · 0% Book details