← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 171

Sashe 9

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gudu yake shararawa a motar shi tanyar ta zuwa kudu, don kirar da yasa na gagawa daga abokan sanar shi saboda meeting din da zasu yi don kara wa mai farashi saboda harajin da gwaunati ta saka masu,
Shi kadai ne a cikin motar sai kidar da ya sa nawakar wani dan yaren su inda yake wa egwaii of Benin kirara,
Wayar shi dake gefen shi tai babirashon, hannu ya mija yadauko wayar hankali shi na saman titin kadan don yafara jin kamshin okene,
Ganin bakuwar noba yayi acikin wayar shi dan mamaki ya baiyana a fuskan shi kadan,
Don gani bakuwar nobar kuma yasan cewa wanan wayar sai special mutanen sa ke kiran shi da ita,
Kamar ya aje saidai ya dauka yana mai karata a kunen shi,
Muryan mace yaji tana mai sallama a cikin hausa,
Cire wayar yayi yadaga yana kallo don shi a bin ya bashi mamaki so sai wallahi,
Sai kuma yace kila wrong noba ce,
Karakara wayar yayi a kunen shi don yace is wrong noba,
Saida abin mamaki daidai lokacin da ya kara wayar akunen shi a lokacin ne, yaji mai maganar tana cewa
Yakake Joseph ?
Mamaki karara a fuskan shi ya ansa mata da lafiya,
Wake magana ya ke tambaya cikin mamaki, saida tai yar murmushi har yana jinta daga inda yake
Tace kana magana da Aisha Sanda ce,
Aisha Sanda ?
Joseph ya kara nanata sunan cikin mamaki a fili
Tace mai eh
Wace kuka hadu a wurin dinner din hamza har ka kaini gida,
Ok ok yace nagane ya kuke ta amsa mai da lafiya lau,
Yau nake tambayar KB kai yace min ka wuce sai tadan shake muryan ta kamar mai shirin kuka,
Tace shine bakazo munyi sallama ba katafi, ?
Maganar ta ba shi mamaki sosai don dai ya san cewa bawai wani sanin juna sukayi ba ko sabawa,
Amma sai kawai yadake duk da cikin mamakinta yake , ya ce , mata just sorry,
Kamar ta na ganin shi kai kawai ta gyada mai kamar yana ganin ta a fili,,
Wani irin ajiyar zuciya yayi yana mamakin maganar ta acikin zuciyar shi,,,
Ita ko Aisha wani irin shu,umin murmushi tayi bayan sun aje wayan azuciyar ta tana kiyasta abinda, take planing akai,,,,

Tsaye yake a cikin wani ma,aikatar tatan man petroleum, da ke kudu, yana son idon shi ya tabbatar mai da ko mota nawa daga con n motocin su , suka shigo,
Wayar shi tai kara noba ce ya gani babu suna don haka bai san mai wanan nobar ba,
Yadauka yana mai cewa hello,
Aka ansa mai adayar bangaren, jin muryan mace kuma ba hausa tana cewa
Hello mun wuni lafiya ya kwana biyu ?
Hello wake magana yace
Mamaki ne ya kama Aisha jin cewa har yanzu ashe bata shiga ba,
Ansa mai tayi da cewa Aisha ce daga KG,
Dan shiru ya biyo baya kadan sai can yake ce mata ok nagane
Pls ki bani dan lokaci zan kira ina aiki yanzu pls
Ba matsala race tana mai aje wayar cikin jin takai ci,
Amina wace ke kwance gefen ta har tagama wayar ta numfasa tace wallahi Aisha kina bani mamaki
Cikin dan jingina bayan ta da bangon dakin da suke zaune tace agani ki ko,
Amina tace a ganin kowa ma,
Kin fasan cewa ba musulmi bane wanan guy din don may zaki nace a kan shi dole sai kinyi halak da shi,
Daidai lokacin ta dauko wani abin gyara kumba daga cikin jakar ta,
Tafara dan kankare kumbar hannunta da abin sai can kamar bazatai magana ba tace
Kina nufin don ba musullumi bane bazan yagi rabo na ba ke nan,
Cikin mamaki kawar nata ke kallon ta don Aishan ta ba ta mamaki kwarai ta ya zatai mu,amula da wanda ba musullumi ba,
Gaskiya ita bazata iya ba, iyakar harkan ta ga musulumai yan uwanta,,,
Saboda yawan matsin da take mai dole yafara dan sakin jikin shi da ita har suna dan hira jefi jefi a waya,

Tafe take ciki uniform din su na girls day secondary school, sauri takeyi don ta isa gida, saboda ta samu ta shirya da wuri zuwa islamiya,
Don a kwaita da tsoron bugu bata son abinda ya tabi lafiyan jikin ta sam
Wasu "yan matane mutum biyu cikin shiga ta isa da nuna lokaci ke tafiya,
Tafiyar ta takeyi cikin sauri yasa sukayi kusan yin karo da daya daga cikin yan matan ne tai karfin halin cewa haba malam wani irin tafiya ne kikeyi babu ko tsari balle ki nuna ajin cewa ke ma mace ce,
Maryam wace duk saurin da takeyi bai hana ta tsaya wa guri guda ba cak,,,,
A hankali ta juya inda suke tadan kalle su murya a raunane tana mai cewa kuyi hakuri pls ban san cewa gurin ba zai muna bane,
Daga haka ta juya batare da ta kara cewa uffan bata ci gaba da tafiya sai dai maganar na kona mata zuciya,
Don may zasu ce ita bata da aji kodon batasa bujen da ya manne mata jiki bane, shine rashin wayewar da suke hange a gareta,

ZEEE MAKAWA
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
7⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

Kusan duk wanda ke cikin wurin yana saye da rigar coat ce a jikin shi sai yan kali lqn ne ke da shiga irin ta hausan arewa ko su basu mutum uku ba daga cikin su,,,
Daga ni meetings suke yi kuma meeting ne ma tsauri don duk kan su fuskan su babu wallawa a ciki,
Kadan kadan hayaniya ke dan biyo baya musan man idan an fadi wani abinda ba,a yarda da shi ba agurin,
A wajen harabar gurin kuma maza ne kaitai majiya karfi kashi, kashi, da alamar security ne su
Sai wasu irin manyan motoci da sai inda idon ka ya tsaya,,,
Kowani kusurwa na wajen an zuba jamian tsaro birjik
Sunan mutum uku ne yanzun haka ake muhawara akai,
Mr Inok ,Ishaya noma sai Joseph,Emanuele,
Daya daga cikin su ake son ajewa a matsayin sectarianism din su na matasa masu harkan man petrol,
Daga karshen zaben ya fada akan Joseph wanda akasari mutane ba,su so hakan ba ,,,,
Wani dan Jos suka so Ishaya Noma,
Wanan mukamin ya jawo mai ci gaba sosai tare da duk wani wanda ke kusa da shi,
Abokan shi dana sanar shi sun hada mai party samun cigaba,
Mutanen kwantagora sun zo mai murna, don kusan duk, yan abokan su sun zo,
Wanan zuwan ya tayar masu da hankali so sai fiye da tsab manin su,
Don duk daukan da suke mai ashe yafi da haka a fili,
Sai bayan sun wuce ne Aisha ta samu wanan labarin kuma har an tafi, don haka ta lalashi Amina har ta yarda suka shiga motar kasuwa suka tafi har can,
Bayan sun isa ne, takira nobar KB take sheda mai cewa gasu sun iso garin,
KB yai mamakin jin wai ga su sun shigo cikin garin
Inda Joseph yake cikin abokan harkan shi KB ya rutsa yaje har cikin kunnen shi yai mai rada yaba sheda mai zuwan su Aisha
Sai da Joseph yadan nuna kaduwa don bai taba tsan manin zuwan su ba,
Wani yaron shi yakira yai mai nuni da KB yace su je tare azo da, su masauki
Su kan su sun yi mamaki kwarai da irin masaukin da suka samu,,

Washegari ne zaa ,gudanar da taron tayar murnan samun cigaban da su Joseph suka samu,
Inda taro yai taro don duk bakon daya zo dana kusa dana nisa Joseph yasa an karama shi da wada tacen abinci da na sha daidai gwargwado,
Fili na musan man yasa aka bawa abokan kurciyan shi a ce war shi, inda suka fito cikin musulunci tare da hasken musulunci a fuskan,
Sai mamaki su akeyi yadda sukazo taya,shi murna haka da yawa,
Anyi yan wasan ni da kuma raha kamar yadda akanyi inda wani abokin kasuwan cin shi da Lagos ya ba shi shawaran yai aure, hakana tunda Allah ya,wadata shi da arziki tun yana yaro,,,
A haka taro ya,watse , wa yanda suka zo daga nisa suka fara niyar komawa gida,
Sai, a lokacin Joseph yasamu kebewa da su Aisha cikin yar sakin fuska yake masu maganan,,,
Inda yai mata godiya sosai da kuma bata, appointment, nan da two weeks zasu hadu,
Aisha taji dadin wanan tafiyar da sukayi saboda irin guzurin da suka dawo dashi,
Tun wanan lokacin ya rage samun lokaci kamar da, yanzu ya kwana biyu baizo kwantagora ba duk da aiken da mahaifin shi Mr Emanuel ke mai na cewar church members na son ganin shi,
Aiki yakawo shi Abuja don haka yai amfani da wanan damar ya iso amsa kiran mahaifin shi,
Yan church din sun gudar da,addu,an su gare shi tare da fatan alheri zuwa gare shi,
Yaji dadin wanan adduan da akai mai don haka yaba gagarumin gudun mawa a church din nasu,
Tun jiya Sunday da suka dawo church din bai kara fita duk da yawan wayan da friends din shi keyi don jin cewa yana gari,
Bai samu fitowa sai bayan karfe biyu inda yace ma KB yazo su fita,
Don motar shi ta na bukatar, wanki sosai, don haka, yabar ta kanin sa ya fita mai da ita gurin wanki,,
A,saman mashin din KB suka fita, fitan da yasa mutane suka san cewa Joseph yazo gari,
Hmmm Dan Adam da kudi, kafin wani lokaci har yan kai koke sun isa gurin da suka san cewa zasu ganshi su yi maula,
Mutanen mu ho, idan zuciya ta mutu koma mutum na iya yi don kawai ya samu kudi,
Sai bayan sun gama maula ne sai a koma gefe ace ai dan kafirin nan yazo
Ai yanzu ba asan sanar da yake yi ba sai dai kudi ake ganin shi da shi ba a san ida yake samun su ba,
Wasu kuma, cewa suke yi ai Joseph mafiya yake yi yanzu sosai, irin na ya birni wanda ba,a gane akidar mutum,,,
Chapter 9 · 0% Book details