← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 171

Sashe 21

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Washe gari tunda safe ya nufi gidan su jibrin don gaida mahaifin jibrin din,
Yadda yake zato abin yafi nan don duk dan dattijon yaramay yayi baki,sosai,
Sundan dade zaune a dakin baban jibrin din da zaitafi yaba shi dubu hamsi yace ai sai mai lemo,
Sam yaki karban kudin saida kyat yakarbi kudin da farko Joseph ya zata ko baison abin hannushi ne,
Saida dattijon ya yace mai yarage sunyi yawa yabashi ko kadan ne,
Yace baba lemo kawai za ,a sai maka kasha,,
Bayan fitar su waje ne Joseph din ke cewa jibrin yanzu may ake ciki akan zancen,
Nan dai Jibrin ya sheda mai cewa kotu tace mutumin yabiya shi nan zuwa karshen shekara,
Joseph yace har lokacin ba,atafi aikin ba ke nan,
Jibrin yace kai haba har wasu na shirin zuwa ma alokacin ,,
Kai haba impossible inji Joseph gaskiya asan yadda za,ayi musamu baba su tagi wanan shekaran,
Jibrin yace yaya zamu man tunda duk dan abi da ke ga baba shine ya hada yabiya masu
Joseph dake kokarin bude mota yace ma jibrin a ina zamu samu kujerar, ne,
Mamaki karara a fuskan jibrin yace kai bafa maganar wasa bane man kudin mutum uku baba ya bita fa,
Joseph yace and so what,
Indai har zamu samu ai sai su tafi,
Murna jibrin zaiyi ko kuma may
Saidai kuma a zuciyar shi ya na tunanen in har mahaifin su zai yarda da zuwa makka da kudin Joseph,
Don haka ba bata lokaci suka shiga cigiyar kujerar makka
Saida kyat suka samu a wani local government kusa da kwantagora magama local government,
Saidai an masu karin kudi sosai akai amma haka ya juye madu yabiya, don dai kwai yadda yake jin kada a wuce baban jibrin bai samu zuwa aiki hajji ba kamar yadda ysi niyya,,,
Maganar nazuwa gurin baba aikuwa baba yace sam badashi za,ayi awanan aikin ba,
Ina zai tafi aikin hajji da kudin kafiri,
Da tambaya dakomai malamai sukace ya halatta su tafi tunda shi yaga dama yabasu kudin shi kyauta,,
,,,

ZEEEE MAKAWA
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
1⃣4⃣

ZAINAB IDRIS MA KAWA

Wanan tafiyan na mahaifan Jibrin da Joseph ya ba kudin zuwa Saudiya ya jawo muhawa sosai a cikin gari,
Har takai wa yanda basu san shi ba yanzu sun fara samun labarin shi,,,
Dashi akai komai har zuwa rakiyan su airport a Minna inda zasu tashi, zuwa kasa mai tsarki ,,
Wanan abin yabawa Joseph mamaki sosai don tun a nan sun fara ibada
Daga can ya wuce zuwa Abuja gurin zancen business din da suke so sufara jonawa,
Wanan tafiyar tankar tafiyar don jibrin a kayin don itace samuwar aikin jibrin din,,,
Anbashi In charge na supplying din duk wani shinkafa da mangyada da za,a shigo dashi daga wata kasa,
Zuwa kasar arewa da kewayen ta, kamar su Cameron da Chadi, Niger
Bakaramin sa,an samun wanan nasar yayi ba don mutane da dama sunyi ta korafi akai,
Wanan abin yaiwa mutane da yawa dadi saboda jibrin mutum ne mai tsimakon nakasa da,shi sosai,
Lokacin tafiyan su Joseph da kakar shi yayi kawai sai ji Mr Ema yayi cewa Joseph yafita tare da ita, zuwa Jerusalem,,,
Wanan fitar mutane kauyen suka,dinga mamakin cewa tunda ita witch ce yaya zata iya zuwa can wurin bauta,
Wanan tafiyar ta daure wa Joseph kai sosai saboda abinda yagani a can ya banbamta da yadda suke gudanar da tasu,addinin a nan,,,,,
Saboda sai yaga cewa ai duk kusan al,adun da akeyi acan kamar al,adan musuluman Nigeria ce da sauran duniya,
Hatta da alwala indan bakayi ba ba,za,a bari kashiga cikin massallacin ba,
Abubuwa da dama yagani a can sai kuma yaga cewa ai har da musulumai daga wasu kasashe suna zuwa yin bauta a cikin wanan masallacin mai tsohon tarihi watau masallacin, BAITI,MUKADIS,,,,
Ya dawo gida zuciyar sa fam da tunane kalala, acikin sa,
Kakan shi mai suna Ciyoma, tun acan tadinga wani irin kuka na farin ciki tana mai samai albarka,
Addu,an gamawa da lafiya da duniya yadinga mai aciki tasako zancen da ake mata zargi dashi tana mai cewa,
Tagode Allah da jikanta ya zama abin kwatance a cikin jamar su, har yafidda ita daga zargin mutane, cikin wani irin magana kamar waka,
Joseph dake zaune yana kallon ta a cikin dan gurin shan iska da suka tsaya a wani airport,
Yana saye da wani katuwar rigar sanyi,a jikin shi yataso daga inda yake zaune tun fara maganar ta,
Ya rugumay ta ajikin shi don maganganu da take fadi sun ratsa mai zuciya sosai a lokacin
Tunanen mahaifiyar shi wace a yanzu bata da rai ya fara ji dama ace tana da rayuwa ne da yanzu suna tare da ita a wanan gurin,
Saboda yasha tayawa mahaifinshi cewa suzo wanan gurin ziyara amma sai Mr Ema din yace bai son abin wahala shi,
Wasu hawaye masu dumu suka silalo mai daga ido zuwa kasar fuskan shi,
Yanajin mutuwar uwar su kamar yanzu ne abin yafaru mata mai hakkuri da sanin ya kamata
Don yana da wayon shi irin yadda mahaifin shi yadinga wahal da ita a lokacin zaman su,
Jin hawayen Joseph na diga mata a wuyar ta ya sa yar tsohuwar dagawa daga cikin jikin shi ta dubi fuskan shi,
Ta ce Joseph my child don cry pls,
Kara rike kakan tashi yayi saboda yadda yake ji a zuciyar shi ba dadi
Sun kai wani lokaci a haka sanan nan ya ja ta da kyar zuwa wurin da kayan su yake gefen wasu kujeru da aka tanadar wa matafiya,,
Sun iso gida Nigeria cikin farin ciki da walwala a zukatan su saboda, sun tafi inda kowani dan addin Christian ke burin zuwa,,,
Ta Abuja suka,sauka don haka yasa wani abokin shi ya kwaso su, daga airport,
Zuwa gidan shi da yake sauka a Abuja,indan yazo,
Sai da ya huta san nan ya kira KB yana sheda mai cewa sun dawo shi da kakar shi,
Kwanan su biyu abokanan shi suna ta zuwa yi mai barka da dawo wa,
Tun wanan tafiyar tasu josepy yasa wa ranshi cewa ba,zai kara barin wanan yar tsohuwar kakanshi cikin wahala ba saboda tana bukatar hutu a rayuwar ta yanzu,,
Kwantagora suka nufa daga Abuja inda tsohuwa ciyoma bata so hakan ba don dai ita taso ne takoma gida,
Don yanzu bata son wani alaka ya hada ta da mahaifin su Joseph tunda ya iya rabata da 'ya'yan diyar ta,
Inbadon Allah ya bata jika mai albarka ba wanda yasan darajan ta,

Sai bayan tafiyar Joseph Jerusalem ne labari ya iso ga mahaifin shi irin tai makon da yai wa jibrin again,
Abinda takai shi har da hawan jinin shi ya tashi mai dama ko yan uwan Ema IBO sun san shi mutum ne wanda baya son taimakawa na kasa dashi,
Cikin dare suka isa don tun a hanya sukai waya da Samuel nan Samuel yake sheda mai abinda yafaru
A cike da rashin son taimakon da mahaifin shi baison yana yi ya iso fam a zuciyar shi,,,
Murna sosai yan uwan shi sukayi daganin kakar su wace tun suna kanana so sai rabon da su ganta
Mr Ema yana dawo Church gurin service din dare yai arraba wanan tsohuwar duk shi ba wai wani girmuwar shi tayi ba sosai
Nan da nan anurin fuskan shi ta gushe mai sai da kyat ya iya controlling din zuciyar shi,,
A nuse Joseph yafito daga dakin shi don zuwa tariyan baban shi,
A fusace ya ke karba mai inda yafara mai sababi na rashin bin umurnin shi da Joseph din baiyi,
Yace saboda kaga yanzu kana cin gashin kan ka shiyasa ban isa in sa ma doka kabi ba,
Kafada min may hujjan ka na taimakawa yaran hausawa kuma musullumai,
Joseph har in bazaka daina hurda da wa yan, nan mutanen ba ina warning dinka kadaina shigowa kwantagora pls,,,
Joseph wanda kan shi ke duke tunda mahaifin nashi ya fara fada yadago a hankali ya fara magana acikin natsuwar nan tashi yace
Dole in taimaka masu baba saboda sun min abinda yafi haka alokacin da nake bukatar hakan,
Rai bace Mr Ema yadaga kai cikin mamakin kalamin dan nashi yace,
Kana nufin cewa ba,zaka iya rabuwa dasu ba ke nan,
Shiru yayi mai wanan karon yana dai sararon shi kawai,
Barin falon yayi saboda yasan cewa yanzu wani ,zafi ba ,zai lankwasa Joseph din ba,
Chapter 21 · 0% Book details