← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 156 OF 171

Sashe 156

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Guri guda taja ta tsaya takasa karasowa zuwa cikin falon,
Don ganin yar tsohuwad da tayi zaune ta murtuke fuskan ta babu walwala ko kadan atare da ita,
Kamar ta koma sai dai ta daure ta kara sa cikin falon,
A hankali ta isa har gurin da maman Choima din take zaune cikin matsanacin bacin rai,
Gefen ta ta isa inda ta durkusa har kasa kasan ties take ce mata cikin ladabi,
You are welcome ma,
Maryam ta karasa kai zaune a gurin taci gaba da gaida tsohuwan wace alama ya nuna cewa yar uwan maigidan ne,
Tsohuwan na zaune da wani zanin jugei ta aza wani saman wani kanta babu dan kwali sai dai duk an aske gashin kan,
Pipkin wanda ke kwance gefen tsohuwan yana danan game din shi jin muryan maryam yadan sashi dago yace,
Grandmother dis is my new, Mumm,
Buge mai hannun da yake nuna maryam din tayi tana cewa cikin yaren IBO kada yakara fadan hakana agaban ta,
Wani irin mugun kallo ta,watso ma maryam din wace ke zaune a kasan ties, tana dan wasa da yatsun hannun ta,
Mikewa tayi ta shiga kitchen ganin cewa kusan lokacin fara girkin marance yayi ,
Amma kuma sai ta tuna da cewa bata ba wa wanan tsohuwar ruwa ba don haka ta shiryo su a ture ta kawo mata ai wani mugun kallo ta,watsa mata,
Ba,shiri maryam ta bar gurin batare da ta kwashi kayan ba a nan tabar su,
Abinci irin na gargajita ta hada masu, tuwon semovita da miyar agushi yaji nama gudun gundun, naman ya nuna da kyau,
Sai ruwan shayi da ta dafa da kayan yaji saboda tadan yi nazirin maigidan nata ma,abuci shan shayi ne shi,
Kamarya yadda tasan Anty ta dije tafison sarrafa zobo a nau,i nau,i ita ma dai maryam din hakan ne don ta hada masu zobo da kankakana ,
Kafin wani lokaci ta hada komai ta gyara kitchen din
Ta koma dakinta ta shirya jikin ta tsab cikin wani dogon rigar atamfa din kinshi mai matse jikine sai hannu shara,shara da akai mai,
Daidai lokacin taji horn din motar maigidan a wajen gidan,
Takowa tajeyi daga steps din a hankali inda hakan yai daidai da shigowan shi gidan,
Ga maman Choima zaune yana mata sannu da zuwa ga kuma maryam black din shi tana saukowa daga steps,
Kamshin jikin ta har zuwa gurin da yake tsaye ,
Cikin daurewa da matsewa ya dan je gurin tsohuwan wace ke kallon mamaki,
A lokacin ne maryam ta karaso gurin tana mai sannu da zuwa cikin yar makkan murya,
Barin tsohuwan yayi ya riko hannun maryam din yadan kai mata kiss riko ta yayi zuwa jikin shi yana cewa Mama meet my beautiful wife maryam she is hausa fulani by tribe,
Sai kuma ya juya gurin mraryam ita da hannun yace mata dis is my grandmother,
My mother, mother,
Dan kara rusun,nawa maryam din tayi cikin girmamawa tace you are welcome mama,
Sai yaji dadin yadda tayi batare da nuna wani kyama ba a yadda maman tazo da kai ko dankwali babu, sama,
Jakar hannun shi ta karba inda ta juya tabar su nan a tare,
Dakin da Grandma, take Maryam da kanta ta kara gyarawa,
Ita ko sai wani ya mutsa fuska takeyi wai tana jin haushin Maryam tare da,jikan ta,
Abinci so sai su ka kwasa don kowan su har Pipkin yaji dadin wanan girkin,
Maman choima ce ke tambayar ya canza mai masu girki ne halan ya girgiza kan shi lokacin da yake wanke hannuwan da ruwan da maryam ta ahe mai a gefe don wanke hannayen su,

Washegari Yusuf bai fita zuwa gurin aiki ba yana gida manne da yar amaryan shi yana morewa,
Wanan yinin haka Yusuf din yakoma masu kamar wawa agidan don yna manne da matar shi,
Cin abinci kawai ke fitar dashi waje don kar ya zauna da yunwa,
Sai zuwa karfe shidda saura yabar gidan yana saye da wani wando cryzy fari da bakin tie shirt mai yar wuya,round,
Wani katon super market ya tafi inda ya sawo masu kayan bukatan gida,,
Daga ciki kayan maryam yafi yawa saboda yasan tana da bukatan su,
Yaso da sai sun tafi waje ne yai mata lefen ta a can,
Yasan tabbas maryam takai yar albae
Amma kuma yanzu fitan su kasan zai dan dauki lokaci saboda shigowan grandmother,
A,falo ya samu Grandma tare da, Pipkin, suna kallo maryam tana,dakin tana lazimi don anyi sallah magrib,
Grandma tabi ledodin da ido don gano ko may ke a cikin su,
Ukeria, mai masu wanki da guga shine ya shigo gidan da kayan wanda tun can ogan shi ya fada mai cewa ya kai sama gurin madam din shi,
Yana ajewa shima Yusuf din yana,shigowa da,wasu,
Maryam ta tofa adduan gami da shafe jikin ta dashi tadan dago kai tana cewa maigidan nata sannu da zuwa,
Sai kuma yakai kallon ta ga kayan fuskan ta taf da tambaya,
Shida kan shi ya zauna yana fitar da kayan tare da yi mata bayanin cewa yan kayan da,zata fara amfani dasu ne ya,siyo mata don tafiyan su ba yan zu ba
Idan kuma akwai wasu abinda take so sai ta fadi a sayo mata,
Da sauri maryam ta dago kai ta kalle shi tace wanan ma,sun isa basai an karo ba nagode kwarai tausayi tabashi saboda ganin dan abin da yai mata amma tana mai irin wanan godiyan da addu,a,
Bayan ya fito ne ya ga wani irin kallon da maman Choima taimai direct gurin ta ya nufa saboda bai son ace, za,a samu matsala daga gurin ta,
Hannun tsohuwan yariko yace mata cikin yaren su yana son taso matar shi kamar yadda take son shi,
Kafin yaci gaba tai wani irin daga hannuwan ta tazagoyo da su takan ta tace,
Over my death body,
To love dis awsa girl never, never,
Murmushi yayi ya mike ya na cewa mama I don't want to have problem with you,
Juyawa tayi tana fada acikin harshen yaren su tana cewa, ita sam sai ya sallami maryam din tabar gida
Dariya maganar taba Yusuf saboda yasan kafirci yasa kakan nashi fadin haka,

Su Jibrin ne da KB din suka kawo masu ziyar da daren yau,
A gidan suka ci abincin dare tare da su amma banda maryam wace ke
Ciki bata fito ba don kascewar su baki maza,
Sai bayan sun gamane maryam din tafito cikin wani dogon riga har kasa rigar yai mata kyau sosai
Tana saye da wani dan hijab a saman shi wanda iyakar shi iya kafadar ta,.
Da murmushi a fuskan ta don ganin su da tayi tankar a gida kwantagora take,
Su ko su Jibrin sai kallon yadda maryam din ta canza cikin dan lokaci guda sukeyi,
Shiru tadan yi inda su ka ci gaba da hiran su a tsakanin su,
Maryam din ce ke tambayan Jibrin labarin Safiyan ta,
Saida yadan kalli su KB sai ya kwashe da dariya yace maryam ai kin,fi kusa da safiya yanzu
Mamaki maganar Jibrin ya ba maryam din don maganar ya daure mata kai,
Yusuf ne ya gane cewa maryam tadan shiga rudu a cikin maganar tasu,
Sai KB ne ke cewa Yusuf ai ya bar matar shi ta kusa haihuwa don haka ba zai dade ba zai koma KG din,
KB nawa yusu hra shiko Yusuf duk hankalin shi na gurin rabin ran shi maryam,
Yusuf ne ya jefowa Jibrin tambaya don dai maryam ta fahinci zan cen shi ,
Tambayan Jibrin yakara yi da cewa yaushe ne wai zancen auren ku kai Jibrin da Safiya,
Nan ma dariyan yayi sai da yadan numfasa sanan yace wa Yusuf din gaskiya maganar nan tamu tana rawa ne yanzu,
Da sauri maryam tadago idon ta ta sauke su ga Jibrin cin don gaskanta zancen sshi
Pipkin ne ya katse zancen don ya sauko da gudu nani tana bin shi a baya wai ya tsaya yasha maganin shi,
Shiko sai tsala ihu yakeyi yana gan garowa, duk sai hankalin su ya koma gare shi a lokaci guda,
Kuka yaron ke yi matyam ce ta karbi magani cikin hikima ta bashi yasha, ta dauko ruwa taba shi ya kara kurbawa,
Hakan ya burge kowa dake gurin don daga haka tajawo yaron zuwa cikin jikin ta shiko ya lafe,abin shi,

Tun wanan lokacin Yusuf bai gane kan maryam din ba badon komai ba sai don maganar da Jibrin din yayi akan aminiyar ta,
Tana zaune bayan ta samu ta lalaba Pipkin yai barci shine tadan shiga bayi tawatso ruwa,
Ribon take kokarin kama kan tada shi guri guda,
Yayin da taji hannun Yusuf din akan, ta, ido suka hada daga cikin mirrow da Yusuf din,
Ribon din yakarba a hannunta, ya daura mata shi tsab a kai,
Gaban ta yadawo ya tsaya inda yadan jingina jikin shi da mirror din da take kwalliya akai,
Sunan ta ya kira a hankali ,
Ita ma ido tadago ta kalle shi cikin jin nauyi kamar kullun,
May kika fahinta akan zancencen Jibrin a Safiya ne, ?
Murya narkarka kamar mai shirin kuka cike da shagwaba maryam din tace ,
Gaskiya uncle ina ganin kamar akwai rikici a tsakanin su saboda tun ina gida na bar jin Safiya tana zancen Jibrin din,
Yusuf ya funkule hannun shi guri guda yana dan bubuga su cikin juna,
Ya lumshe idon shi ya bude su a lokaci guda ya dan furzar da iska waje,
Zan sa a bincikar min dalili insha Allah,,,,,,,,

ZEEE MAKAWA YELWA

[5/5, 9:13 PM] ‪+234 703 055 6607‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
9⃣3⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI

ADDU,AN NAKE NEMA AGURIN KU, DA FATAN ZAKU TAYANI ROKON ALLAH
JUMMA,AT MUBARAK YAN UWA RAMADAN MUBARAK👏👏👏👏
Chapter 156 · 0% Book details