← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 171

Sashe 32

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tsaye yake a cikin dakin shi yana daura agogon a hannun shi wanda ke mai masifar kyau aduk lokacin da ya makala agogo a hannun shi,
Jerked din shi yadan aza saman wuyan shi, hannun shiguda ya rarimi yar Case din shi, da ita,
A cikin sauri yake kokarin yin komai hakan kawai zai sa mutum yagane cewa yana da wani abu mai muhinmanci yau agaban shi,
Da dan sauri sauri yake saukowa daga step din yana kokarin gyara tie din dake makale a wuyar shi,
Tun bai karasa sauko wa ba Ejoma dake tsaye a bakin dinning table take mai wani irin kallo,
Kofa yanufa don yau baiko tsaya zuwa gurin kakar shi ba,
Brother, abinda Ejoma ta furta ke nan kamar yadda take kiran shi, where, are u going
Your break fast is ready now,
Tafada cikin yar shagwaba kamar yadda yan kabilar su keyi wa yayyen su,
Dan tsayawa yayi, cak, Agogon shi yadiba ya dan ya mutsa fuskan shi kadan yace mata,
Cikin dan sakin fuska sorry sister, i don't have time for dat pls,,
Kai Ejoma ta kara dan langabewa tadauki cup tea ta,nufi inda yake tsaye har a lokacin yana kokarin gyara nicktie, din shi,
Cup din tea din dake hannun ta tamika, mai tana cewa brother i beg drink dis ,even small now,
O my god, Ejoma iam telling ,u now, dat iam, late,
Ba yadda ya ita dole ya karba ya dan kurba tsa,tsaye, kadan kadan,
Yamika mata cup din cikin sauri yabar falon don gudun kada Ejoma ta jawo mai wata matsalar kuma
Yana fita Ejoma dake tsaye tadan bi bayan shi da kallo tana dan girgiza kanta,, Busy man ta furta,
Ba laifi don yasa bakin nasu basu karaso ba, gurin da za ai taron,
Wasu yan kasan Cameron da Guinea ne zasuyi wani dan meetings da su ta yadda zasu dinga tura masu mai acikin farashi mai sauki,
Sai kuma kada watau ( Cotton) zasu yi harkan business din shi dasu,
Sosai Joseph din ke jin dadin meeting din tare da bakin nasu saboda akwai abubuwan da ya fahinta so sai a fan,nin kasashen biyu,,,
Tsawon wani lokaci suna wanan, taron har zuwa daidai da lokacin sallah a zuhur,
Kawai sai mutum guda daga cikin su baki,ne so sai wulk da shi,wanda ke cikin shigar bakaken coth
Tare da wani daya wanda shiko wasu kanan kaya yasa sun bala,in yi mashi kyau sosai,
Mutumin farkon ne yafara daga hannun shi yadan kalli agogon hannu, wanda ke nuna karfe, daya da wani abu na rana,
Mikewa yayi zubur yana mai ce ma sauran abokan meeting din I want to pray,
Joseph da a,lokacin yake kokarin diba wasu takardun dake a gaban shi yai sauri daga kai ya kalli mutumin
Wanda shi azaton shi tun farkon shigowar su yadauka dan bishon ne,
Wai a,she muslumi ne, diban shi yakara konawa ga gudan da ke kojarin sance agogon hannun shi
Kamar yadda yaga su KB na yawan yi idan zasu yi, alwala,
Duk a cikin mamaki yadinga kallon su a zuciyar shi kuma cewa yayi,
Ashe shi musulumi bawai dole ta kam ki wani hali zaka iya sheda shi ba ke nan kamar yadda yaga sauran, musullumai suna rike tasbaha ko kuma rawani ko sa tufafi mai nuna sheda,
Kafin ya farga yana a cikin tunanen sai gani wa yan nan biyu dake gefen shi sun mike suma zuwa yin sallah,
Ya kai wani lokaci yana ta al,ajabin wanan abin da yagani a tare da wa yan nan baki nasu, sosai,
Wayar shi tai kara don haka yafita tadan waje kadan daga dakin taron,don,yar karba call din,
Abakin wani daki dake gefen inda,suke taron yaga takalma mutane agurin,
Sautin ladani sallah yaji har inda yake yana fadar Allahu,Akbar, Sami,al,llahu limal,hamd
Kamar ance ya waiga hango su yayi still suna cikin shigar tufafin da Joseph ke tunanen zasu hanasu yin sallah,
Can karshe yanufa ya ci gaba da maganar da yake yi,
Har zuwa dawowar shi sun rarage sallah sun idar suna zaune suna lazimi,
Ya zauna bada wani jimawa ba saiga su Aoudullah sun shigo duk kan su fuskan su cikin fara,a,
Nan suka fara mikawa mutane hannu suna musabi,a da duk wanda ke gurin,
Sau guda yadan daga kai ya kalle su yai saurin kawar da kan shi,
Sai dai haka kawai ya kalli yan uwan shi Christian dake ta harkokin su cikin rashin damuwa,,,,,,

A gajiye tafito daga dakin daukar lectures din din su yar jakar ta na sabale a kafadar ta,
Tasan cewa A,A yana aji a lokacin don haka bata wahal da rayuwar ta zuwa office din shi,
Saboda yanzu ma duk ta rage yawan zuwa gurin shi don guje wa shedan,
A,kwai wani dan korido wanda zai sadaka da wata department namasu yin computer science,
Iccen da ke gurin andan kawata shi da wasu kuherun kasa da akayi wa farin penti,
Can ta nufa da niyar zuwa ta zauna, kafin lokacin shigar ta lecture yayi,
Wata matashiryar buduwar ce zata dan girmay ma maryam kadan,
Zaune take ta hada kai da gwiwa alamar a cikin tashin hankali ,take,don tayi zaune tayi tagumi,
Gefen ta maryam ta zauna tare da fadin Bissimillahi,
Hannu tasa acikin yar jakar ta tadauko wani dan bunch din digestive, biscuit, da wani dan lemon kwali,
Gefen da yariyar data tarar a zaune tadan kalla karo na farko tunzuwan ta tazauna gurin,
Mikawa yarinyar ledar biscuit din tayi tana mai mata Bissimillah,
A hankali yariyar tadaga kai da idon ta da sukayi jawur, a lokacin, ta,dan girgiza wa Maryam kai alamar a,a, tafurta nagode,
Sau guda maryam ta dan tauna biscuit din sai taji kawai bataji dadin yadda ta lura da cewa yarinyar na kokarin share hawayen ta da gefen gyalenta,
Lafiya dai ko Maryam tai katsalandar din tambayar yarinyar,
Wani kuka tasake lokaci guda tace wallahi yar uwa matsalar malam nan ne ke damuna ace mutane yan uwanka musullumai su dinga maka sheri,
A hankali Maryam ta aje kwalin lemon da tafara dan zuka a lokacin ta mai da hanjalinta gun yarinyar,
Yarinyar tace ni sabuwar zuwa ce a wanan school din, gashi na kusa kamalla duk wani abin da yakamata inyi amma gashi HOD din mu yaki samun hannu a takarda na wai bai yarda da results dina ba,
Wani irin mugun tausayi yarinyar taba Maryam jin bakinta kawai tayi yana tambayar yarinyar wani department ne,
Tace computer science, zubur Maryam ta mike ta kokarin gyara gyalen da tai rolling din kanta dashi,
Shigar shi office ke nan yana kokarin dauko ruwa acikin dan karamin Fridge din dake office din,
Da sallamar ta shigo office din sam bai zaci zuwanta yanzu ba don yasan cewa sai ta gama abin da takeyi takan zo su wuce gida, watarana ma sam baya ganin ta saidai suyi tayin waya,
Ganin ta yanzu yasa yasan da matsala fuskanta ya dan kalla yaga damuwa fal acikinta,
Daidai lokacin da yake zama yake cewa lafiya kuwa Maryam,
Ido tadan tsura mai yau babu ko kiftawa, yai mamakin hakan sosai a, ranshi don yasan cewa ba halinta bane hakan,
Zai yi magana sai yaji muryan tana cikin rauni tana magana,a hankali,
Malam banaso sam, sunan ka, ya dinga fitowa daga cikin azzaluman malam makarantar nan,
Masu kokarin kayarda ditan mutane, daga cigaban su,
Kafin taci gaba yadaga mata hannu alamar ta tsayar da zancen ta hakana,
Cikin mamaki yake tambayar ta komay ke faruwa da har tazo mai a haka,?
Nan ta kwashe yarda sukayi da wanan yariyar ta fada mai,
A, cikin mamaki yake tambayar cewa yaushe akai haka da shi,sam bai ma san zancen ba
Can yace ina ita yarinya tana daga waje inji Maryam,
Da sallama maryam suka dawo tare da wanan yarinya,,,
Cikin ladabi tagaida malam din wanda ke dan rubutu a wani dan pepper,,
Yadago kai yakali inda suke yana mai mika mata hannu alamar takawo takardun ta, dake hannun ta,
Ba,bata lokaci taciro su daga cikin handabag din ta, ta mika mashi su, jiki na rawa, kamar zata fadi don tsoro,
Tai mamaki kwarai da taga yasa mata hannu batare da bata lokacin komai ba cikin yan mintuna
Ita ko yanzu kusan wata daya da rabi ke nan tana ta faman bin, ai, mata wanan aikin abu ya faskara,
Sai gashi yau Allah yakawo mata shi a cikin sauki ta samu an mata,
Yana gamawa yadago ido ya kalli yariyar yace mata kin taba gani na akan wanan takardan,
Tace duk lokacin da nazo sai messenger ya ce min baka nan komaya yace ance bazan samu ba karshe ma sai ce min yayi ance takarduna basa yi wai,,,,,,
Chapter 32 · 0% Book details