← Book details Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 171

Sashe 79

Furen Juji Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Dan zagayawa take yi, cikin super market din, tana dan dibawa ko zata samu, abinda zata saye a matsayin gift , duk da bawai wasu kudine masu yawa acikin jakar na taba,
Layin sai,da kayan kamshi take dan zagayawa don dibawa,
Duke take tana kokarin ciro wasu set na shafa, irin ta mata, acikin wata, yar kit,
"Yan mata ya kike kwana biyu, ?
Muryan take tunane a ina tasan shi ne wai, don ko bata waiga ba tabbas tasan wanan muryan,
Bashir Alhasan ne tsaye da wasu kayan da mafi yawan matasan maza hausawa ke sawa a yanzu,
Tunane takeyi a ina tasan wanan fuskan ne wai, kafin second ta tuno, dashi.
Bata san lokacin da ta sake wani dan munrmushin da iyakar shi fuska,
Ina yuni tace cikin yanayin muryan nan nata,,
Yar kwaikwayon ta yayi hakan yakara sata sake wani lalausar murmushi again,
Tsayuwar shi yagyara yace ai nasan dama kida baki fada min inda kike ba wata rana zamu kara haduwa ne,
Yakara zancen, yana mai dan rausayar da kai, kamar wani kara min yaro,
So ya kwana biyu ya karatu Maryam Abdullahi ko,
Yana mai mata wani kallo irin na wayyaun maza,
Kafin ta bashi amsa yakara jefo mata wani tambaya,
May a kazo saye ne haka, ?
Bata bashi ansar ko guda ba sai dai yar murmushin da takeyi a kasa kasa,
Set din kayan, da ta dauka ya mika hannu ya karba yana dan karanta sunan shi,
Yace da alama dai gimbiyar gift take dibawa ko,
Hannu taga ya mika can ciki ya dauko wani babban set mai kaya kala kala cikin kit din,
Yace ina ganin ai wanan zai yi ko,
Maryam wace sai binshi da ido take don kara tan,tance halin shi,
Sai ya dan daga kai saman yana karanta wasu set haka, dake gurin,
Yadawo da kanshi yana mai kallon ta fuska a sake yace bazamu layin Sweet bane ko?
Kai ta girgiza mai alamar a ,a bazata ba, don haka yadan daga kafadar shi alamar ba ruwan shi,
Zan wuce ta furta, a hankali, kamar mai maganar rada,
Ok muje ko yace mata tana kokarin ce mashi ai ya barshi,
Sai ganin Yusuf tayi tsaye da alamar tun tsayin su gurin yake kallon su,
Tsaye yake a bakin wani da kantar kaya yajin gina da wani bango dake gurin kafar shi a harde, acikin wani,
Biye Bashir yake da ita, duk tawani kunya da ganin su da yayi, atare,
Suna tafe sai yaba kyawon kwaliyar ta yake yi yana kokarin cusa ta gwaunatin gare ta,
Sun kusa kaiwa inda Yusuf yake tsaye cikin dakewa sai wayar shi yaje latsa,
Maryam ta dan kalli Bashir,ta juya inda Yusuf yake tsaye tace,
Ga yayana ku gaisa dashi,
Wani kallo yai wa Yusuf na second, inda yagane cewa ba karamin mutun bane, don komai na jikin Yusuf zaikai kusan million, guda,
Yana yar dariya yace au kice min bake kadai bace dama,
Hannu ya mikawa Yusuf suka gaisa, sai dai Yusuf din,ya, na yin hausa sai Bashir din ya dan waigo maryam,
Tagane may yake nufi a cikin style ta kada mai kai alamar eh,
Amma tunda nayi ni,yar biyan kudin, wa yan nan kayan ina fatan cewa yayan mu zai bari in biya ?
Fuska aba walwala, Yusuf yace wa maryam indan kun gama sai ki samay ni a mota, ina jiran ki,
Daga haka ya juya zuwa waje inda suka aje motar su,
A tare suka fito dafa cikin plaza din da bashir wanda motar shi take aje a gefe guda,
Gurin motar Yusuf Maryam ta nufa ganin haka Bashir yadan fidda idon shi yana mamaki hafin maryam da wanan guy din,
Yusuf na kallon su daga cikin motar shi dake makale da tin tak glass,
Sun kysa kaiwa gurin motar maryam taja tai tsaye tace mashi, to na gode kwarai Allah saka da alheri,
Yadan sa key holder din shi ya sosa kan shi,
Sai kuma mukara haduwa ko maryam makarasa zancen mu ko ?
Da,sauri maryam ta dan kaleshi, tace yaushe kuma zamu kara haduwa ai ko yau sa,a ce,
Sai,da yai yar dariyar maganar ta, san,nan yace, aini dama ko yaushe a cikin sa,a nake,
Kai kasa cike da jin nauyi maryam tace to shi ke nan nagode badamuwa ki, sallamar min da yayan mu,
A nutse kamar kulun ta isa gurin motar inda tadan kwan kwasa mai glass, ,
Tana shiga motar yataya suka harba saman titin, sai dai a hankali yake tukin shi
Duk da kasan cewar motar babbace amma hakan bai,sa,shi yin gudu ba,
Sun dayi tafiya kadan, batare da, yawaigo inda take ba yace,
Wani, kuma sabon mayaudarine kika,samu, haka ?
A cikin mamaki take kallon shi ido a zazzare
Kallo, mai kama da harara ta yayi yace, gaskiya maryam ko wanan bai dace da ke ba, sam wallahi,
Kanta aduke tai shiru saboda wani irin bakin ciki da ya tokare mata mokoshi,
Ya dago ya kalle ta idon shi ya canza zuwa bacin rai,
Haka itama maryam domin maganganun sun daga mata hankali,
Idanu a runtse tana jin wani irin bacin rai, da kunar zuciya,
Haba ya Yusuf, ai wanan maganar bai,dace ka fada min ba,
Cike da mamaki, ya ware ido yana kallin ta don sam bai dauka maganar zai sa bacin rai haka ba,
What maryam bakya son a fada maki gaskiya ne, ?
, a,fusace kamar wace zatai shirin kuka, tace mai, haba dai daga ganin mutum kawai zaka yanke man hukunci akan shi,
Yakamata ace katambayeni bayani akan shi bawai kawai a yanke mun hukunci ba
Ya Yusuf ya,kamata ace kana cikin wa yan da zasu shedeni,
Kamar yadda kake tuhumar ina hurda da yan duniyar samari,
Ma,ana nima din yar duniyar ce ke nan ko,?
Murmushi ya yi kawai har zuwa lokacin da ta kare fadar maganar ta,,
Hakalin shi ya mayar a,titi, sanan yace,
Don nasan cewa,ke yarinyace karama , duk sun fiki wayo da sanin duniya,
Sam baki dace dasu ba gaba dayan su ,bai,kamata ace kina tsayawa dairin su ba,,
Daga haka ya mai da kan shi a kan titi sosai, bai kara,bita kanta ba,.
Saida suka kawo unguwar ya tambayi maryam tai mai kwatance a takaice ,
Kofa ta bude tana kun,ku ni, tana cewa wanda ke tare da irin su Aisha da sadiya ba ace mai ya bari ba sai wace ba ruwan ta za,a sawa ido,
Lock din motar ya dan na tayi tayi ta bude ta kasa sai a lokacin ta waigo in,da shi,ke zaune,
Kamar ba shi take jira ya bude mata kofa ba, sai kawai,ya kama lalabar wayar shi,
Cikin murya mai nuna karaya zuciya da kuma kuka, tace mai,
Ina son zan fita ne
Bai juyo ya kalle ta ba, tankar da dutse take,
Sai da yagama taba wayar shi san nan ya dan,na unlock, motar ta bude,
Ran ta a bace ta sa kai kawai tafita batare da ce mai komai baya,
Bayan ta ya bida kallo a hankali, sai kuma yai saurin kau da kan shi yana mai cewa Astangafurllah,
Ganin irin tai makon da yai mata bai kamata don ya fada mata gaskiya ba haka tai fushi tafita ko godiya babu,
Ta dan waigo kamar mai rada tace mai nagode
Kai kawai ya kada mata batare da cewa komai ba ya ja motar shi yabar gurin,
Duk da taron bukin yai kyau ya kawatar, ga kuma abokan su na tun makarantar secondary sun hadu,
Rayuwar maryam a bace yake saboda duk kusan ba yan yan mintina sai ta tuna da zancen Yusuf,
Har yanzu kanta ya daure ta rasa gane may maganar shi take nufi ne haka,
Da zaice mata wai ta kara samun wani mayaudari,
Yana nufin cewa A,A din ta mayaudari ne ko may ya ke nufi da hakan,
A haka tai tawa yan uwa yake don kada su gane halin da take ciki,
Chapter 79 · 0% Book details